Saturday, 8 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  0⃣9⃣


           Ahaka har suka gama shirya kayakinsu itade khadeeja tana mamakin irin isgili da addini da bint da phaary sukayi. Bayan sun idar da sallan maghrib khadeeja tadau Qur'ani tafara karantawa bint da phaary da Saalihah kuwa duk sun taru akan gadon bint suna hira acewarsu hiran da sukeyi zesa khadeeja tayi shiru. Phaary tace "so Saaly tell us more about yourself" Saalihah tace "kunga ni baran muku karya ba mahaifina talaka ne sosai hasali ma scholarship nasamu shine sanadiyar shigowata wannan makaranta amman kwata kwata banason talauci, kyaman kowani talaka nake." Phaary da bint suka ce "kinyi gaskia talauci ba abin yi bane, ba yadda za'ayi kici kuka agdan ubanki kiyi aure kuma still kicigaba da cin kuka," Saalihah tace "ashede kun gane," bint tace "ai ure right emmata. Kinga mu dinnan iyayenmu sunada arziki iya gwargwado na rufin asiri dan su suka biya mana kudin makarantarnan sede ba duk abinda mukeso muke samu ba mukuma a gaskia lashe money ne mu, tun muna ss2 muka sa neman samari a gaba komi su suke mana ciki harda irin manyan alhazan nan duk muna alaqa dasu badan mu auresu ba kuma dan kawai muci kudinsu ne." Saalihah tace "ayyah kunyi gaskia ynxu gashy in ba wai kun fada ba wa ze dau ku ba 'yan manyan gda bane," bint tace "ai karki damu kema zamu saki a kan hanya kici kudi baby." Khadeeja dake jinsu tace da kanta "wa'iyyazubillah bekamata Saalihah ta biye ma wadannan munanan kawayen ba in zasui abinsu suyi su biyunsu kar suyi including dinta yakamata in mata mgn kar ta biye musu, karatu ne yakawota ba neman samari ba"
       Can dare around 11:30PM, hirar bint da phaary ne kawai ke tashy a dakin. Khadeeja ta karaso xuwa gadon Saalihah tare da ce mata "can we talk?" Saalihah tace "sure"... khadeeja tace "naji zancen ku duka daxu a gaskia beh kamata ki biye masu bint da phaary ba kekanki kinsani abinda sukeyi haramun ne. Me acikin talauci da zakice kina kyamatan talaka kina nufin kina kyamatan annabi muh'd SAW fa knan, dan ko annabi yakasance baida arziki amman se muce Allah ya kisa knan ko me? Ai da arziki wani abu ne da bawanda zekai annabinmu arziki a fadin duniyar nan, ana yini a gdan Rasulillah ba tareda an aza kwanon abinci ba, in Allah yayi ka a talaka karka ga Allah baison kane, wani sa'in kudi ma sharri ne ga dan adam dan sau nawa zakiga masu kudi suna kashesa kan emmata da kayan mahe, in Allah yayi ka da arziki kuma bawai yana nufin yafi sonka akan dan uwanka talaka bane. Ki aje shawarar da bint suka baki ki dage da karatu in shaa Allah, Allah ze baki nasara ki kallesu fa ynxu? Lokacinsu suke batawa a banza adole suna hira da samari inda karatun Qur'ani sukeyi da befi musu ba? Ban taba fada ma kowa wannan mgn ba ammn ke zan fada miki da kke gani na mahaifina senator ne amman ko kadan kudinsa be dameni ba." Saalihah data dafe kirji tace "senator?"  Khadeeja tace "eh amman karki gaya ma kowa, nima bawai na gaya miki bane dan ki fara respecting dina a'a na gya miki ne dan kiyi changing ways naki." Saalihah tace "toh nagode khadeeja seda safe," khadeeja tace "Allah bamu alheri" takoma kan gadonta ita kuma Saalihah ta mike akan gadonta, "lalle kam khadeeja dama taya kudin samari ze tsole miki ido bayan mahaifinki senator ne? Ai kibarni kurum nima naji dadin kud'i bawai zance shawarar da kka bani beyi bane a'a naki yayi sede nasu phaary yafi kwanta min a rai" ahaka har tayi bacci.
          Washegary da asuba khadeeja ce ta tashe su sallah dan kuwa su bint sun saba se 8 saura sukeyin sallan asuba. Basu koma bacci ba kasancewar sunada lectures 9:00AM wanka duk sukayi one by one su bint da phaary aka yi zaman makeup sun kusan awa daya akan gyarar fuska sannan suka gama Saaly tace itama a mata ras suka mata me kyau itama ta dauko daya daga cikin sabin dinkunan data yi tasa harta dau gyale phaary tace "gyale kuma? Dillah aje ungo wannan ta miqa mata wata side bag da takalmi sasu," Saalihah ta amsa tasa ita kanta tasan tayi kyau khadeeja de kallonsu take tana kada kai hijabinta tasa harda niqaf da gloves nata sannan suka rufo dakinsu suka fice gaba gaba khadeeja tayi dan bataso hada sahu dasu. Taku one by one suke bazawa cikin ATBU kowa ya gansu seya sara musu ahaka har suka isa lecture room suka zauna kusa da juna ta gaba yadda duk wanda yake shigowa ze gansu.
       Bayan sun gama first lecture din aka fita 15mins break Saalihah ta fice zuwa toilet dan gyara fuskarta. Tana tafiya ne tana kallon wayarta kome takeyi aciki oho hankalinta du yabi kan wayar, kawai jinta tayi taci tuntube kafin tace me ta fadi a qasa, tarota kawai taji anyi daga baya a razane ta dago idanunta kallon ko waye, wani kyakkyawan saurayi ta gani yana mata murmushi gwada dago kanta tayi amman takasa sanda ya dagota yace "nxt time kina kallon gabanki" yana kaiwa nan ya yi tafiyarsa yabar Saalihah da baki wangalau a bude, love at first sight kawai tafara feeling masa ga har ynxu kamshin turaren jikinsa bebar gun ba, da kyar takoma lecture room din har aka kare lectures din Saalihah bata san me ake koya musu ba se tunanin yadda wancan guy din ya rikota ta baya kawai take.
        Bayan sun qare lectures na ranan suka fita eating out a aroma, acan Saalihah ta hadu da guy din dazu wanda yayi saving nata from fadi dazu. Su bint suna ganinsa suka fara "gashy can ga can FUDAIL, omg!" Phaary tace "muje mu masa mgn," bint tace "eh muje, Saaly muje ko?" Saalihah tace "a'a kuje ni bansan sa ba baran je ba." Phaary tace "pls muje fudail nefa, kinsan guy din kuwa?" Saalihah tace "kuje nide ina jiranku." Haka suka nufa gunsa ba ita bayan sun gaisa suka zazzauna sukayi ordering abinci se hira sukeyi, fudail kuwa se kallon Saalihah yakeyi yana wani tauna chewing gum. Duk sanda suka hada ido da Saalihah kuwa seya kashe mata wata shu'umar murmushin dayake melting mata zuciya. Abinda Saalihah ta lura gameda Fudail shine tantirin dan iska ne dan har wani magnet dan kunne yakedashy a kunnensa amman kyakkyawa ne ajin farko ga iya dressing gasa dogo, so smart. Bint ce tace "Fudail baka ga new frnd dinmu bane?" Fudail yace "naganta mun hadu daxu a sch meh sunanta?" Phaary tace "haba? Saaly sunanta." Fudail ya ajiye wasu kudi gashy pay for this inada lectures in the nxt  1hour" yana mgnan yana kallon wata rolex dake hannunsa. Phaary tace "toh thank you for ur time" daidai yakai bakin kujerar Saalihah yace "Saaly till we meet nxt!" yamata wata murmushin da ta kashe mata zuciya. Alokaci daya taji kawai tana son Fudail, ji take kamar sonsa tayi shekara da shekaru a zuciyarta, tace da kanta "I'll do whatever it takes Fudail yazama nawa ni kadai, daman akoi guys hadaddu haka a bauchi shine nake kula erinsu yunusa mstww. Saalihah this is ur time, rocking rayuwata zanyi to the fullest"

No comments: