Saturday, 8 April 2017
KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
written by miemiebee👄
0⃣7⃣
A daki ta wuni ranan se danne danne take a sabuwar wayarta. Washegary da safe umma ta wuce kasuwa haka abba ma, daga Saalihah, se Sa'ad da baaba a gda se can 9:45AM Saalihah ta tashy tafito zuwa kitchen wayam bata ga abinci ba daman umma ta saba kafin ta fita kasuwa seta musu breakfast, bayan dogon hamman datayi tace "yau akeyinta wato kod'an breakfast din nan yau babu ni zan dafa knan ko meh?" Nan tayi dakin baaba ta sameta zaune kan sallaya tana karatun Al Qur'an, ko gaisuwa babu tace "baaba kin karya?" Sanda takai qarshen ayan sannan tace "bansani ba tunda baki iya gaisuwa ba fitsararriyar yarinya kawai," Saalihah tace "haka kkace ko?" Bata jira amsar baaba ba ta fice hijabinta ta sako tadau purse nata ta fita daman akoi me siyar da masa a unguwarsu nan ta siya amman daidai bakinta dana Sa'ad tana komowa gda tadau kujera ta zauna ta kusa da dakin baaba sannan tafara bude buden ledar tana kolla ma Sa'ad kira "fito muci masa kai! dan baran iya aikin hura murhun nan ba," baaba najin masa ta ajiye Qur'anin ta fito "masa? A ina kka samu?" Saalihah tayi banza da ita ta cigaba da kiran Sa'ad "wai baraka fito bane?" "Gani adda Saalihah ina wanke baki ne," ya fadi a takaice, "toh gara kayi sauri" ta amsa, nan yafito ta sa masa guda biyu a plate nasa, baaba tace "ke Saalihah ba mgn nake miki ba?" Saalihah tace "ba na tambayeki ko kin karya kkacemin baki sani ba, shine nasiyo mana abin karin kummalo nida Sa'ad kadai" Baaba tace "ohh ai kinsan sarai nima ban karya ba neman mgn ne kawai" tasa hannu zataja plate na Saalihah da sauri Saalihah taja plate din takai bakin kofa da gudu, "Sa'ad taho nan" shima ya dau nasa plate din suka tsaya a bakin kofa sanda suka gama cinyewa tas sannan suka dawo tsakar gdan suka ajiye inda ake wankewanke baaba na kallonsu, daga bisani tace "nikuma me zanci Saalihah?" Saalihah tace "aww daman baki karya ba shine dana tambayeki kka cemin baki sani ba, woo baaba tafara jin yunwa heheh" Nan ta ciro wata kodaddiyar hamsin ta miqa ma Sa'ad "ungo je ka siyo ma baaba bread agun masu shayi in yace bana hamsin kace ko yanka ya maka," Sa'ad ya amsa ya fice itakuma tafara wanke wanke, baaba na kallon ikon Allah bejima ba yadawo tace "kai wa baaba... gashy baaba seki karya nakega akoi ruwan shekaranjiya a flask dan umma tace insa jiya naqi in yayi sanyi dayawa seki kora breadin da ruwa kawai inkuma zaki iya kunna murhun seki tafasa sabo." Baaba ta amsa breadin "baran ce miki komi ba Saalihah amman kisani Allah ze kawo ranar da zakiyi nadaman duk abubuwan da kkeyi," Saalihah dake wanke wanke tace "ikon Allah ynxu baaba fisbailillahi in siyo miki breadi amman da abinda zaki saqa min knan? No wahala nanda 'yan kwanaki zan koma makaranta balantana ki ganni har kina gasa min mgn iya san ranki," baaba bata ce da ita komi ba takoma cikin daki dan Saalihah tafi karfinta.
5 days later ana gobe Saalihah zata fara zuwa babbar makaranta, da yamma ta je ta amso dinkunanta tana dawowa gda ta hadu da ameenatu zaune a tsakar gda, dagani jiran ta take, Saalihah tace "anniya tun yaushe kka zo?" Ameenatu tace "ban wani jima bade," Saalihah tace "mushiga daga ciki," kayakin Saalihah ta zazzage kan katifar ta, ameenatu tace "anniya sabin dinki kkayi? Yaushe haka?" Saalihah tace "kina wasa da Saalihah" nan tashiga gwada su gashy kuwa sun bala'in mata kyau daidai jikinta, bayan data gama gwadasu ta ninke ta sasu cikin akwatinta, "kinga ameenatu ba baki zaki bude kina kallo na ba" nan taja sabin akwatin data siya inba wai ance 2nd hand bane za'a dau sabi pil ta siya, "oya tayani shirya kayakin nawa a ciki" haka suka fara ninke mata kayakin suna sa mata cikin akwatunan, ameenatu tace "toh ban lbr ya akayi kka sami kayakin nan haka? Saurayi kkayi?" Saalihah tace "ko kadan kinga ke tawa ce baran boye miki komi ba" nan taba ma ameenatu labarin komi, bayan data gama ta dau sabuwar wayartan ta mika ma ameenatu da har digan miyau take dan yadda ta wangale baki, "kaii amman tayi kyau, ke Saalihah amman baki tsoron rananda asirin ki zai tonu?" Saalihah tace "ai in shaa Allahu bare tonu ba kinsan meh?" Ameentu ta kada kai da alaman a'a, Saalihah tayi lowering voice nata "duk randa na hadu da daya daga cikin mutanen nan ke zaki yi saving dina nikuma na miki alkawarin baki kud'i," cikin rashin fahimta ameenatu tace "kamar ya knan?" Saalihah tace kede kawai anytime am in trouble zan kiraki d moment na kiraki da sunan Hassana seki shirya kwararo karerayi", tana mata signal da gira "inade kin gane ko?" Ameenatu tace "shgya Saalihah bakici sunanki ba," Saalihah dake dariya tace "nidin knan" sekusan maghrib ta rako ameenatu.
Washegary! Kasancewar ranan Saalihah zata fara zuwa babbar makaranta around 4:15PM ita da umma da Sa'ad suka tsari napep bayan wa'azi da fatan alheri da abba ya mata baaba ma badan tanaso ba tace "toh Allah bada sa'a ya raka taki gona" tare da murguda baki, Saalihah tace "oh! baaba ta ta kaina bansan me zan miki ki fara sona ba ungo nifa umman kice" dari biyu ta ciro a jakarta "a sai goro da kyau, abbana ga wannan kaima" dari biyar ta miqa masa da kamar bare karba ba Saalihah tata insisting sannan ya amsa ya suburbuda mata albarka sannan suka fice daidai gabar ATBU aka saukesu, se gashy yawancin samari da 'yan matan cikin mota ake kawosu wasu kuma su suke driving kansu ma a zuci Saalihah tace "oh! Wannan sch ze kawo light sosai" har dakin ta suka qarisa suka ajiye mata akwatunanta a bedside ,umma tamata wa'azi sosai sosai sannan suka fice ita da Sa'ad bayan wayarta na da da dari biyun da Saalihah ta basa. Zama tayi bisa gadon tana me kare ma dakin kallo 4 pple ne per room, dakuma toilet aciki se 'yar wardrobe dake gefen kowani gado.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment