Saturday, 29 April 2017
KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
written by miemiebee👄
4⃣5⃣
Umma de ita bata goyi bayan wannan idea ba amman ya ta iya da Saaly? Dolenta ta yarda tace, "toh naji amman aiko guda d'aya muka had'a yayi ko yaya?" Saaly taja da baya sannan tace, "d'aya? ba sesu raina mu ba su kawo mana 24 mukai musu d'aya? 3 de xamu had'a barin d'au mayafina mu wuce kasuwan ynxu" "toh" umma tace mata nan da nan Saaly taja mota se wata shagon da ake sayar da shaddoji zalla haka tata kwasan masu tsada wa Fudail, umma de nata ido ne dan batasan ina Saaly ke samun kud'i ba, duk yadda take pacaka da kud'in amman bai k'arewa. Suka gama da shaddojin sannan sukayi shagon takalma designers masu kyau nanma haka tata kwasa, agoguna turare da huluna babu wanda bata sai ba daga k'arshe akwati set me guda uku tasaya mekyan gaske sannan aka xuba mata kayakin ciki suka dawo gda. Daidai lokacin baaba da abba keta kallon kayan lefen Saaly baaba de batak'i ta wuni ranan tana kallon kayan ba dan ba k'arya sun had'u bayan ya musu sannu dazuwa kasancewar yana d'an ma umma mgn sama sama ynxu.
Yace, "daga ina haka uwata?" Tace, "kasuwa abba mun had'o ma Fudail kaya ne shima... ina yaron yake?" Tana kallon k'ofar "shigo da kayan mana" ta fad'i nan yashigo da akwatunan guda uku bayan sun k'are duban ne abba yace, "sunyi kyau sosai uwata" "Allah sanya alkheri sede bansan ina kka samu kud'i dayawa haka ba, har kukaje k'asar waje da umman ki dan miki siyayya". Saaly ta taresa da wuri "ahh haba abba karkaji komi, kud'ad'e dayawa Fudail yabani wanda ni kaina bansan yawansu ba kashesu kawai nake sunk'i k'arewa". Abba yace, "gaskia wannan yaro jarumi ne Saalihah ki rik'e masa amanar kanki ki kasance me ladabi da biyayya a garesa, ki guji b'acin ransa kuma, kinji ko uwata? Allah miki albarka". Saaly data sadda kanta k'asa kamar dgsk tace, "in shaa Allahu abba nagode". Ya k'ara da "kaya sunyi kyau sosai Allah sanya musu albarka". Kowa gun ya amsa da "ameen."
Washegary Saaly ta kira su Phaary, bint, ameenatu, ruky da de sauran frnds nata kan suzo ganin kayan lefenta da yamma duk suka iso wane sun had'a baki nan ta ciro musu akwatunan gaskia kaya "yayi kyau" abinda suke ta fad'i knan bayan sun k'are kallon ne Phaary ta tab'e baki tare da fad'in "Saaly wai are u serious kin bar ATBU?" Saaly tace, "sit down here, yawwa zancen ashobe fa? Yakamata colour'n kaya na yayi rhyming da naku kamar ynxu in xan sa sky blue kaya ku kusa milk kunga ai colour combination d'in yayi ko?" Duk suka amsa da "eh" haka de suka samu suka curo colour'n ashoben da zasu siya in response to colour'n kayan Saaly.
Ameenatu de nata ido ne dan da akayi total d'in kud'in ashoben na events biyar ya tashi dubu ishirin. Ita ina take da dubu ishirin? Saaly ce ta kwantar mata da hnkl "karkiji komi ni xan saya miki duka nide kawai inganki gun biki". Ameenatu tayi godia.
Haka preparation na biki yacigaba da gudana Saaly de wutaaaa kawai take ina binta gas. A saura sati biki ne wedding gowns nata suka iso duk ba wanda za'a zaga sbd duk sunyi kyau na inna naha haka kayan hana gorinta ma. Oshewa Beauty makeup artist daga Lagos tayi booking tazota har Bauchi. Fudail kuwa yagama musu booking flight ticket nasu is ready sauran tafya kawai.
A yau ne aka fara events na bikin Saalihah da Fudail da bridal shower suka fara wanda sukayi a gda k'aramar party ce duda haka be hana Saalihah booking photographer one in town ba wato George okoro haka sukasha bidiri ga makeup nata yayi bala'in kyau skin nata sekace ba bashi ba, ba alamun bleaching ba alamun damb'are damb'aren bak'i ga wani hasken data k'ara sekace asalinta ma fara ce, tasha gyaran jiki sosai. The nxt day akayi pre weddding dinner a Zaranda hotel daga kan ango, amarya, da bridesmaid duk ba wanda za'a aibanta sunfito sosai. Ikleema maman ango tasha ashokin nan haka umma ma. Sanda Saaly ta tabbata tafito da ummanta ras!. Naira de yayi kuka a wannan biki. Bayan pre wedding dinner akayi kamu wanda aka mata lallen ta hadadde daga borno (garin mu) me lallen tazo ta zana mata mekyau. Se mother's eve da akayi washegari, se kuma cocktai night tge following day, biki de wane a Abuja. Washegary akayi polo wanda Saaly tasha pencil trouser da polo shirt abinta haka Fudail nata ma.
Biki de wanda yaje shi yasan meya gani dan bare labartu ba! Ranan asabar kamin a d'aura aure aka kai kayan ango Fudail yaji dad'i sosai dan ba k'aramin burgesa kayan yayi ba haka daddy ma Ikleema de tarasa ina wannan pand'ararriyar yarinyan ke samun kud'in da bai k'arewa danko Fudail be gaya mata yabawa Saaly kud'i ba. Da misalin k'arfe 11:00AM na safe aka d'aura auren FUDAIL AHMAD DA SAALIHAH IBRAHIM KAN SADAKI NAIRA DUBU D'ARI BIYU.
Saalihah na zaune a d'aki da frnds nata se tsula mata tsiya sukeyi itako tana biye musu. Da daren ranan akaxo d'aukan amarya su ameenatu sun d'au kuka Saaly keyi dam yadda ta rufe fuskarta tayi shiru har suka soma lalashinta sede da suka d'aga alkebban sukaga idanunta fari fat! Phaary tace, "shgya kece 1st amaryan dana fara gani batai kuka ba". Saaly tace, "lower ur voice jorrr, to kukan me zanyi? After all gdan Fudail d'ina za'a kaini ai abin murna ne ba abin kuka ba rufa min fuska da Allah". Ko da akazo fita da ita daga gdan batai kuka ba pretendn kawai take kamar tana kukan harda kama zanin umma haka de dangin ango suka d'au amaryarsu makeupartist da k'awaye suka bisu.
A wani had'add'en d'aki a gdansu Fudail aka sauk'esu sannan aka fara shirin dinner. 8:30PM on the dot suka gama shiri ahaka aka fara tafiya multi purpose inda za'ayi dinner'n decoration din wajen ma kad'ai ya isa yatafi da imanin mutum ba k'arya Ikleema tayi k'ok'ari kud'in daddy yayi kuka a nan ga wani k'atoton cake wanda irga steps nasa ma b'ata lokaci ne gown dayafi tsada kap cikin gowns natan tasa, ja ne da fari shikuwa Fudail yasa farin shadda me tsadan k'arshe gashi yasha zubi me tsada, babban garin ba k'aramin karb'ansa yayi ba.
Ahaka de aka samu aka k'are wannan event amarya da ango sunyi rawa daidai gwargwado ba erin na hauka wanda wasu keyi ba suna ganin kamar burgewa ne. Washegari akayi bud'an kai shima yayi kyau sosai. Sannan da dare aka kai Saaly baby'nmu d'akin mijinta hira sukasha sosai da k'awayenta sekace ba amarya ba harsanda abokan ango suka iso suka sallamesu. Bada jimawa ba suma suka tafi ya rage daga Saalihah se angonta Fudail.
beeenovels.mywapblog.com
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment