Saturday, 29 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  4⃣6⃣


           Tana zaune akan tapkareren royal bed nata yashigo da manyan leather bagd guda biyu wanda ya sauk'e kan dressing mirror sannan ya cire babban garin ya rataya a jikin wata hanger ya k'araso kan gadon shima. A hankali yakai hannunsa kan hannunta datasha bak'i da jan lalle da kuma zobuna da warwaro masu tsada. Jin haka yasa tayi saurin jan hannun nata ta mayar cikin lullub'in da aka mata, ita a dole wai amarya me kunya.

     Murmushi yayi abinda bata tab'a yi ba knan. Danko tun kafin suyi aure ma in ya tab'a ta bata resisting se yau da ya biya sadaki zata fara resisting? Impossible! Ba tareda yace komi ba yasa hannu ze yaye mayafin da aka rufe mata fuska dashi. Hannunsa buge tare da kawar da kanta. Fudail yace, da kansa "yau akeyinta!". "Sweery wai me haka ne? Yaukuma rowan kanki kkemin?" Tayi shiru kamar wacce baratayi mgn ba sannan tace a hnkl, "eh mana bayan ka rabani da umma na". Fudail yace, "nima fa? Ai kin rabani da daddy".

     Tayi shiru batace komi ba. Fudail yace, "toh yi hkr ko sweery kinsan fa gbe ne flight namu and na safe ne lets go eat ko?" Tace, "ni baran ciba". Fudail shide mamaki yake sekace ba Saaly dake binsa a hnkl ba kullum, segashi yau shi ke lalashinta da k'yar ta yadda ta bisa palour'n dake k'asa. Shi da kansa ke bata ahaka har suka gama ci ya tattara plates d'in ya kai kitchen sannan suka dawo sukayi sallah raka'a biyu dan godiya wa Allah daya sa suka kasance tare. Bayan nan yafara janta da hira tana d'an biye masa sama sama se chattn take dasu Phaary a wani group da suka bud'e iyaka su hud'u da Saaly, bint, phaary nd ruky.

      Ruky ta turo da "amarya yakuma kina online? Mu da muka d'au yanzu haka kina sheding tears?" Phaary ta turo da "aikuwa de nima". Saaly ta turo da "kuka? Chab ai namiji yayi kad'an ya sani kuka". Bint ta turo da mude abar mana kurin baki..." Haka suka ta tsula mata tsiya tana biye musu. Can later on Fudail ya fad'a toilet ya watsa ruwa yayi oredering nata itama datayi.

       Bayan ta shiga toilet d'in ne shikuma ya taho ta side drawer'n dake inda Saaly ta tashy dan ajiye key'n motarsa seya ga wayarta tayi k'ara alamar shigowar mssg kowani gulman ne yakaisa oho seya d'aga wayar yashiga group dayaga mssg d'in nan yafara karanta chats d'in yana dariya tare da mamakin Saaly wato "na miji be isa sata kuka bako?" Yana jin k'arar k'ofar ya ajiye da sauri tare da hayewa kan gadon da 'yar nicker ajikinsa kad'ai yace da kansa, "lalle kuwa sena saki kuka sweery Allah kaimu New York. Yau kam baran miki komi ba sbd munada tafy gbe". Binta da kallo yake bayan tashafa mai  tasa wata had'addiyan night gown nata sannan ta feffeshe da turare. Ta hauro gadon ta kwanta tare da masa goodnight.
 
           Matso da pillownsa kusa da nata yayi ya rataya hannunsa kan waist nata, nan fa zuciyar Saaly ya hau bugu dudum dudum! Ita datace batta tsoron na miji, na miji bai isa yasata kuka ba. Idanunta ta maste gamgam sun kusan 5mins a haka be sake yin wani abu ba, setaji shirun yayi yawa.

        A hankl ta juya tana fuskantarsa se taga shikam har yayi bacci. Wata ajiyar zuciya ta sauk'e tace da kanta "awwn! amman Allah maka albarka my Fudail, wlh kamar kasan am not ready for it now duk kurun baki ne dani, I love you so so much. Fuskarsa ta shafe a hnkl seta ga yayi murmushi wanda ya k'ara masa kyau cikin baccinsa, peck ta basa a kumatu. Idanunta suka kai daidai kan abdomen nasa (cikinsa)  daidai kan packs nasa. Hannu tasa ta shafa cikin Fudail a hnkl tana bin packs nasa da kallo dan ko ita a rayuwa akoi san namiji me packs segashi Allah ya bata! Takuma washi na miji me uban tunbi. Sannan ta rik'o hannunsa a haka itama tayi baccin. Da asuba wayar Fudail yasoma kiran sallah. Sbd ya washi k'aran alarm a rayuwa saisa yamayar da alarm nasa na 5 daily prayers atleast kiran sallah bai hargitsa baccin mutum. Da kyar ya bud'e idansa fuskar Saalihah yafara cin karo dashi se baccinta takeyi da hannunta rik'e da nasa tsayawa yayi yana kallonta, wani kyantan ma se yau ya fara gani. Ga lips nata nan kamar tayi pouting nasu da d'an siririn hancinta. Murmushi yayi sbd yadda yaji santa na shigansa. Gaskia duk cikin 'yan matan da yayi ba kamar Saaly, she's not his first love but she is his one nd true love. A hnkl ya raba hannunsa da nata yatashy ya fad'a toilet yayi brushing sannan ya d'auro alwala ya dawo kan gadon ya k'ura mata ido. Sannan a sannu a sannu ya soma shafa sajen dayayi lub a fuskarta a hnkl tasoma k'ok'arin juyawa nan ne yace, "sweery wake up lets pray".

         Cikin gigin bacci tace, "har subh yayi ne?" Yace, "eh tashi kinji". A hnkl ta bud'e idanunta tayi setting nasu daidai kan kyakkyawar fuskar mijinta. Murmushi ta masa shima ya mayar mata sannan ta tashi taje tayi brushing tayi alwala. Already har ya d'au mata hijabinta ta amsa tare da gaishesa "good morning honey". Ya amsa da "morning sweetheart ya gajyan jiya?" Ta amsa da "fine, alhamdulillah". Yace, "good, lets pray ko?" Ta giada masa kai nan yajasu raka'a biyu. Suna idarwa suka hau d'an shirye shirye sbd jirginsu na safe ne.


 beeenovels.mywapblog.com

No comments: