Saturday, 29 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  3⃣5⃣



      Batareda yace komi ba, itace tace "hello baby?" Nan ne yagano Saaly ce dan kwata kwata ma yayi losing number'nta halan emmatansa ne suka goge, wayincewa yayi "bae ya kke?..." Ga hayaniya kota ina, duk muryan emmata ne gun, tuni Saaly tajiyo wani tokari a zuciyarta "haba! baby ynzu dan Allah ka kyauta kenan? In ban kiraka ba baraka kirani ba nd koda na kiran ma bakada time d'ina ina kake duk muryan emmata haka?" Fudail yace "worry less sweetheart birthday'n wata childhood frnd dina ne, bawai clubbing nake ba", duda Saaly tasan k'arya yake amman tayi choosing to believe him dan yadda takesonsa, hiran da takeson masa ma ba san sauraro yake ba "i'll call u later wajen is too crowdy bana jinki, love you", yayi hanging.
    "Fudail wlh kawai dan Allah ya jarabceni da sonka ne inbahaka ba banga namijin daya isa yamin irin wannan iskanci inbarsa ba..." Bata k'are mgnar ba call d'in d'anladi yashigo d'agawa tayi bayan ya gaisheta yace "hjy fa ansamu gdan a old GRA 4 bedroom flat da BQ", Saaly tace "yayi kyau, kuma nawa?" Yace "8mil" "ahh toh yayi, zanso ganin gdan ynxu". Ya ce "ba matsala se mu had'u a gun" nan yamata kwatancen wajen wata doguwar riga tasa tafito se old GRA gaskia gdan yayi gashi ginin zamani ita ynxu damuwarta d'aya ne taya xatayi convincing abba ya yarda.
        ***tana dawowa gda taci karo da abba yana kokarin fita sallan maghrib bayan tagaishe sa cike da ladabi ya amsa da fara'arsa "sannu uwata anyi hutu knan, dama akoi wata mgnar da nikeson muyi" Kai ta giada tare da fadin "toh abba adawo lfya".***  bayan abba ya dawo daga masjid ya tura Sa'ad ya kirawo masa Saaly, a k'asa ta zauna shikuma yana kan gadon d'akinsa, "yawwa uwata nace ynxu kina wani mataki ne a karatun?" Da kanta a k'asa tace "300lvl abba sauran shekaru biyu in k'are gabadai..."  "Ahhh toh masha Allah ai kinyi nisa ma sauran kad'an ne, ina fatan kina sa kanki a karatun sosai ko Saalihah?"  "Eh abba" tace. "Toh masha Allah kamar yadda kika sani, ni bana turaki yin abinda bakiso aiko?" Kai ta giada ya cigaba "to kawunanki ne suka sani a gaba Saalihah wai a dole sena aurar dake tunda kinyi nisa ynxu, kawu abdullahi nasan had'a ki da d'ansa mahmoud amman nace masa kina da tsayayye ko?" Saaly da kunya ya ciketa tace "eh abba", abba yace "da kyau seki masa mgn ya turo magabatansa tun akoi lokaci koyaya uwata?"  "Hakane abba" ta fadi a takaice "daman nima akoi maganar da nikeson muyi abba, shi Fudail d'in ne ya siya mana gda a old GRA dazu ma daga gdan nike wai yanason mukoma can", abba yace "ah ah ah gaskia bareyi mukoma canba uwata halaccin da ya mana yayi yawa kice masa mungude amman kam baramu koma ba".  "Haba abba ai bareji dad'i ba inhar muka k'i komawa can d'in kuma cemin yayi koda kun had'u dan Allah karka masa gdy, shi a matsayin iyayensa ya daukeku ba gdy a tsakaninku dan ya kyautata maku". Abba yayi shiru bece komi ba dan haka Saaly tace "kayi shiru abba, toh shiknan zan gaya masa kace baraka iya komawa can dinba ba". Abba yayi saurin cewa "a'a inhar komawan mu ze faranta masa rai dole mukoma sbd Fudail yaro ne me hnkl da tausayi kice masa ina gdy, ko xaki bani number'nsa ne in kirasa?" Saaly tace "a'a abba ba damuwa cemin yayi ba gdy a tsakaninku". Abba yace "toh masha Allah amman uwata duda abinda yafaru tsakanin ummanki da abban shi Fudail din still kinason ki auresa? Kina ganin yin haoan ba matsala? Ta numfasa sannan tace "nima na masa wannan mgnan amman sam be nuna min damuwarsa ba, kan yayi mgn da abbansa kuma abban nasa ya amince"  "toh masha  Allah, Allah sanya alheri, xaki iya tafiya". Godiya tayi sannan tafice zuwa d'akin umma da Sa'ad ta samesu zaune Sa'ad na homework umma kuwa ta had'e kai da guiwa nufowa tayi gabanta tace "umma dan Allah ki yayyafa ma zuciyarki ruwan sanyi ki rage tunani with time in shaa Allah abba ze sauko kukoma rayuwarku irin ta da". Murmushin takaici umma tayi batare da tace komi ba dan haka Saaly tace "ehm daman nazo in gaya miki kan zamu bar nan gdan nasa ma mana gda a old GRA amman nayi k'arya wa abba na cemasa Fudail ne ya siya mana", zaro ido umma tayi "innalillahi! Saalihah dan Allah ki rufa mana asiri gabadai da wani kud'i kka sai gda? Eh Saalihah?" Saaly tace "haba umma, wace erin tambaya ce? Aikema kinsan inada kud'i akoi wani alhajin dake bani kud'i, sbd muna mutunci da d'ansa damuwana na gaya masa shine ya sai mana gdan ko so kke inbari Fudail yazo neman aurena a wannan b'ab'urukan gdan? Ba se raini yashiga tsakaninmu ba". Umma tace "Saalihah dan Allah ki rufa min asiri in ma sata kkeyi ki bari tun wuri kafin ki makara dan kuna mutunci da d'anaa seya sai miki gda? Nasan k'arya kkeyi kuma gado ba gwaninta ba amman dan Allah kiyi hkr ki soya banzayen halayen da kkayi gado a guna kuma fisabilillahi har ynxu kina kan bakarki na cewan zaki auri Fudail? Bayan sarai kinsan abinda ya faru tsakanina da mahaifinsa taya kkeson mukalli junan mu as surukai? Kiyi hkr dan Allah Saalihah" ta k'are maganar cikin kuka, tuni Saalihah ta tura Sa'ad waje tace "kukan me kuma umma? Believe me wlh bawani tona miki asirin da zanyi wannan kud'i dana saya mana gda baran b'oye miki ba kud'in wani alhj ne shiyaban dan ko na masa alk'awarin aurensa kuma da kke fad'in in ajiye mgnar auren Fudail, wlh da kinsan yadda nikeson Fudail da bara kicemin na hakura da sansa ba, umma inason Fudail duda abinda yafaru tsakaninki da abbansa still banji sansa ya ragu a zuciata ba dan Allah kimin rai, in har kinasona karki hanani auren Fudail". Umma dake hawaye har ynxu tace "Saalihah dama koda nace karki auresa zaki ji mganata ne? Baji zakiyi ba, tunda abinda kkeso kenan Allah baku xaman lfya yasa kuma abbansa ya amince muku"  "ameen" ta fadi "ko kefa umma?"


beeenovels.mywapblog.com

No comments: