Saturday, 29 April 2017
KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
written by miemiebee👄
3⃣4⃣
D'anladi ya sake murmushi sannan yace "eh hjy, miliyan ishrin da d'aya amman kinsan mu anan bamu cika hawa sabin mota pil acikin leather ba 2nd hands muke hawa wanda turawa suka d'anyi amfani dashi, a 2nd hand nasa kuwa miliyan 18-19 aka siyarwa kinga kuwa ynzu in xaki siyar yazama 3rd hand knan k'ila a siya miliyan 15 da d'an abu a ka". Saalihah dake ji kamar mafarki take tace "ahh ba damuwa nide kayi duk abinda ya kamata a siyar min", d'anladi ya amsa da "toh hjy karki damu", ahaka sukayi sallama.
Isarta hstl su bint suke gaya mata nxt month exams nasu bata ko damu ba dan ita ynxu ba karatu bane a gabanta, rabuwanta da tayi attending lectures ma ta kwana biyu. Tunanin me zatayi da wannan miliyan 15 take, daga bisani tace da kanta "yanzu what if Fudail d'ina yazo neman aurena fa? Se in kaisa wannan b'ab'urukan gdan namu? Chabdi ai seya rainani, ynxu in kud'in nan ya iso renovating mana gda zanyi..." Can tasake cewa da kanta "unguwar xango? Ai sanin kowa ne masu ji da kud'i basu xama a zango what do I do now? Dole ne in sai mana gda mubar zango gabadai, ynxu taya xanyi convincing abba?..." Ba erin tunanin da batai ba amman sam takasa figuring out wani karyan zata ma abba ya yarda!
2 weeks later Saaly na xaune a gaban dressing mirror se making up take k'arar alert yashigo wayarta tana kai dubanta taga miliyin shabiyar da d'ari biyar wani tsalle ta daka nan take call na d'anladi yashigo wayar tana d'agawa bayan ya gaisheta yace "alert din yashigo ko hjy?" "Eh d'anladi gaskia kayi kokari nagode sosai xan d'an baka abu aciki kaima but before then da Allah kana harka da dillalai?" "Eh hjy wani abu ne?" "Gda nikeso ne, ko meh 4 bedrooms haka, bungalow me kyau na zamani", danladi yace "na haya knan hjy?" Tace "a'a inda so samu saya nikesonyi", "toh ba matsala za'a shiga nema miki hjy", "toh ngd i'll br waiting for ur call knan", tayi hanging call din.
Nan da nan tagama shafeshafenta ta sha brazillian hair dinnan sannan ta dau key'n motar ta ta fice bata tsaya ko inaba se inda sukayi zasu had'u da T boi, can suka gama soyewarsu ya mata shopping sosai sannan ta dawo hstl. Sallan maghrib suka idar ta soma bawasu phaary lbrin motar data sata gun mutumin ranan duk mamaki ne ya cikesu dan ynxu Saaly tayi wuta ta wuce level nasu, khadeeja dake karatun forthcoming exams nasu tana sauraronsu se kad'a kai take cike da takaici.
Mu kwana mu tashy be bar komi ba su Saaly har sun gama 1st sememster exams nasu na 300 lvl tafito da CO har biyu dan rashin karatu da sa kai kuma ko ajikinta ma, ita da a yau Fudail zece ze aureta ma zatayi dropping sch. Kayakinsu suke ta had'awa kasancewar anyi hutu atare suka gama duk sukayi ba-bye wa juna. Jifatu store Saaly ta biya ta ma family'nta sayayya da dama ciki harda baaba sannan ta kama hanyan gda. A bakin kofa ta tarar da almajirai suka shiga mata da kayakin ciki.
Umma ta iske a tsakar gda se de kallo d'aya ta mata tagano tana cikin damuwa sosai, kokarin boye yanayinta tayi amman sam ta kasa, duk se tausayinta ya cika Saaly, nufowa tayi gabanta "haba umma ya haka? Kinga yadda kka rame kkayi bak'i kuwa? Meke faruwa?" Muryan baaba suka jiyo tana fitowa daga d'aki "ahh lale lale 'yar makaranta sannu dazuwa" tana mgnan tana karisowa gabansu umma, Saaly tace "sannu baaba wai meke damun umma ne?" Baki na rawa baaba tace "ita tasa kanta cikin damuwa kullum cikin tunani take ko abinci ba kullum take ci ba, na mata mgn amman sam tak'i jina badan komi ba kuma dan kawai abbanku yadena mata mgn". Saaly ta dawo da kallonta kan umma datayi langwai kamar wanda akama rasuwa sannan tace "haba umma! Dan abba yabar maki mgn shine tashin duniya? Gaskia kin b'ata min rai, ga wannan..." tana nuni da ledojin data musu siyayya "kowa ya d'au nasa", baaba se gdy take Saaly ta nufa site nata ta watsa ruwa sannan taci abinci ta d'au wayarta takai daidai kan contact na Fudail tace da knta "ynxu in ban kiraka ba baraka kirani ba knan Fudail? Wat have I done kake min haka? Ina da kyau inada kud'i amman ace kullum nike kiranka, nike binka bumper to bumper in ban kiraka ba bakka kirana wlh dan kawai ina sonka ne" nan tayi dialing har ta tsinke be d'aga ba se a karo na biyu ya d'aga
beeenovels.mywapblog.com
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment