Sunday, 2 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  0⃣5⃣


        Tasamu Saalihah a waje suka tsari napep se central market, sayyaya sukayi sosai ba dama, kayan kwalyan nan kam Saalihah ta dibesu wata second hand akwati suka siya mata guda biyu da 'yan kayan abinci seda wata 'yar risho, da dan kayakin sawa irin dogayen nan wanda ake dinka wa a kasuwan nan, se bayan azahar suka dawo gda alokacin abba da baaba suna zaune a tsakar gda kayakin Saalihah da umma ke shigo dasu, bakin abba da baaba a wangale bayan da suka gama shigo da kayakin, abba yace "hajara! Wannan kayaki fa daga ina? Da dubu biyar din kukayi siyayyan nan?"  Toh fa anzo wajen umma ta kalli Saalihah da itama kallonta take sannan ta qirqiro wata karya "ai adashe na kwashe nakuma ranta kudi gun maman abba shine muka hada da dubu biyar daka bata mukayi wannan siyayya" abba yace "aihoo toh masha Allah yayi," baaba kuwa cewa tayi "fa ban yarda da wannan zance ba daman kina adashe shine bansani ba, inma sata kukayi zamu sani!" Harara Saalihah ta watsa mata dataga abba na kallonta seta wayince "kai baaba wace erin sata kuma" nan taciro dari daga cikin change daya rage mata, "hungo ki dan siya goro kici ko baaba ta takaina?" Amsa baaba tayi "Allah de sa ba kudin sata bane," daga tsakar gda Saalihah ta karisa da kayakin dakinta tace "yawwa yanzu na faso gari, in bahaka ba kawai se in dauki akwatin gauro, banza akwatin gauron nan de inje dashy babbar makaranta ai na kwabar, ni ynxu baran je gdansu ameenatu ta koya min amfani da wadannan kayakin kwalyan naji tace antinta nayin kwalyan kudi" nan tasasu cikin wata jaka ta fice zuwa gdansu ameenatu.*** "ke dallah ba hira ce ta kawoni ba ni ki koya min ya ake amfani da wanga abubuwa" tana mgnan tana zazzage kayakin akan wata sallaya, ameenatu tace "shgya! Yaushe kka paso gari haka?  Waya siyo miki?" Saalihah tace "kin fara koh? Long story, Ni koya min amfani dasu tukuna kinsan nxt week za'a bude makaranta dole in cancare ko zan samu wani d'an alhj inci kudi inbar kudi a inda take!" Tapawa sukayi ameenatu tace "shgya Saalihah bakici sunan kiba, aikinji dadi wlh naso cin babbar makarantan nan amman Allah beyi dani ba," Saalihah tana wining wata jan baki tana mgn "ai karki damu Allah sa hakan shi yafi alheri".... Nan ameenatu ta fara nuna ma Saalihah amfanin each nd every item suna cikin yi antinta me makeup ta dawo itama ta shiga koya ma Saalihah saidai matsalar giran Saalihah acike take bare yi tana concealing ba saidai amata carving, anty tace "amikin?" Saalihah tace "ba gayu bane kwashe 'yan banza innallaha gafurur raheem," nan anty ta mata carving giran amman ba karya yadda aka rage giran yayi kyau sannan aka zana mata artificial akai, duk anayi tana lura yadda itama zata iya zana ma kanta, ya bala'in mata kyau nan da nan ta canza, aka koya mata applying eyeshadow, lipstick, eye liner, mascara, blush dade sauran makeup items. Bayan da aka gama Saalihah tayi godia sannan ta dawo gda tana shiga sukaci karo da umma, umma tace "Saalihah? Me wannan a fuskarki, dodo kka koma?" Saalihah ta turo baki "dodo fa kkace umma, ke ba'a ce miki dodo ba seni," umma tace "ai wasa nike miki Saalihah ta amma fa kinyi kyau"... Saalihah tace "yawwa umma ta, kinci dari biyar" nan ta mika ma umma N500, umma ta amsa se kallon fuskar Saalihah har ynxu take tace "bade girarki kka aske ba Saalihah kinsan ko sarai haramun ne ko?"  "Toh meh umma? Duk acikin gayu ne kuma ai innallaha gafurur raheem," tana kaiwa nan ta shige daki umma da aka bari da baki a bud'e ta daga hannu sama "Ya Allah ka shiryar min da Saalihah Ya Allah kar kasa ta bi hali na bannason rayuwarta ta kare kamar nawa" itama tana kaiwa nan ta bi bayan saalihah izuwa dakin ta sameta se shirya 'yan kayakinta take, tace "Saalihah oya gayamun a ina kka samu dubu hamsin?" Saalihah ta taso ta duba waje taga baaba batta nan sannan ta dawo ta labarta wa umma komi tatas! Salati umma kawai keyi "ynxu Saalihah baikijin tsoro wannan mutumi ya miki baki ko ya turo miki 'yan sanda?"  Dariya tayi sannan tace "to aina ze sake ganina? Ai sede a lahira dan beyi kalan wanda ze shigo zango ba," umma tace "still Saalihah abinda kkayi be dace ba taya zaki bata masa suna haka?"  "Toh toh umma uwar wa'azi dallah taya dubu biyar zata min shopping din makaranta, ynxu danayi haka ba gashy nasamu duk abinda nikeso ba, karki damu Allah ze yafemana kurakuranmu... hmm hmm" tana shinshine "ya nakejin warin kona? Anya ba abincin ki bane take konewa? Jeki duba umma," umma zatayi mgn Saalihah tace "zefa kone kinsan halin baaba sarai" badan tanaso ba ta fice Saalihah dake ninke kayakinta tace "wlh umma in kema wa'azin zaki na mun zan dena gaya miki harkoki na haka kawai se gani adole yar talaka da akwatin gauro a ATBU hehehehe lallae kuwa bani Saalihan ba sede in wata" tana gama ninke kayakin ta duba wayarta taga ba kud'i harta dau hijabi ta ajiye kuma "naci wannan kwalya kuma in aza hijabi akai? Ai na kwabar knan" wata tayani gantalinta ta dauko tasa irin tumtum na acuci dinnan ta fice (Ni miemie nace Wa'iyya zubillah) tana tafiya tana rangwada kowa ya ganta seya sara mata ga ukwun nan ba dama, erin gajiyayyun samarin zangon nan se "sss...sss" suke mata amma kanta a sama ko kallan yan banza batai ba, dan neman mgn erin na Saalihah ga shops dayawa a unguarsu amman taki siyan katin agun sanda ta karisa har federal lowcost sannan ta tsaya a daidai wata shago data ga anyi parking wata mota itade motar ta mata kyau amman bata san meh sunan ba ta gefen motar tabi tana satan kallon motar sannan ta karisa izuwa shagon, wani matashi ta gani wanda shima yazo siyan abu ne kallo daya ta masa tasan wancan hadaddiyar motar tasa ce, Saalihan data zo siyan katin dari amman dan bagu tace da me shago "abani airtime na N750 mtn," cikin wata karuwar murya wannan matashi kuwa jin yadda ta kashe turancin airtime instead of recharge card ba karamin burgesa tayi ba, kasancewarsa mini alhj yace da me shagon "bata na N1500 guda biyu," Saalihah datasan dis was coming tayi kamar bata ji sa ba, me shagon ya miqo mata na N1500 guda biyu nanne tace "ya haka bana N750 nayi requesting ba?" Me shagon yace "ai wannan alhj'n ne yace a baki" nanne ta juyo da kallonta knsa tana wani fari fari da ido "toh thanks" ta amsa ta fice nan yabiyo bayanta "miss why not kishiga mota ta in kaiki gda, bekamata ace kyakkyawar mace kamar ki ta taka da kafa ba pls be my guest." Toh fa anzo wajen! Mgnan zuci Saalihah keyi "wululu ka kaini gda kokuma in tona ma kaina asiri? ai ba yadda za'ayi kaga wancan langa langan kofar dake gdanmu, let me think of a way ina gdan chairman dinnan, wlh can zaka saukeni," nan tabar mgn zuci sannan tace "inda zance is not far frm here, karka damu" haka wannan matashy yata insisting har sanda ta yarda ya bude mata kofar sannan ya zagaya shima ya shiga yana kunna motar wata AC ta hura Saalihah, Saalihah da ba'a saba shan AC ba se anje competition ta gyara zamanta daram kan kujerar yadda AC'n zena samunta sosai

2 comments:

Unknown said...

Godia muke sis, Allah ya kara basira.

ummey abubakar said...

thanks sis....we are waiting for the continuation plss