Sunday, 2 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  0⃣4⃣


       Tana kaiwa izuwa bakin kofar gdansu ta ciro robe acikin jakarta ta shafa a qasan idanta atake ta soma hawaye tana shiga ciki tafara rusa ihu ita a dole tana kuka umma dake kitchen tana abincin dare ta jiyo karan Saalihah haka abba da baaba ma duk a tare suka nufo kanta cikin hanzari illa baaba data tsaya daga baya tana kallonsu, umma tace "ya haka Saalihah? Keda waye?" Abba yace "ummata keda waye ne?" Saalihah dake ta rusa kukan qarya tace "wallahi malam shu'aibu ne ya zuba min wayar engine a baya dan kawai inason in mai da wayata jaka," umma tace "kawai shine ya dakeki? Malam kaji mugu fa!" Abba yace "taho muje yau zansan waye gatansa a garin nan," baaba dake kallonsu tace "bawani wlh qarya wannan yarinyar take, dagani rashin kunyar data saba yi ta musu suka jibge ta kuma sunyi daidai, ba inda zakaje ibro kar kaje kaji kunya a banza," Saalihah taja majina sannan tace "shknan abba Allah ze saka min nide baran sake komawa islamiyan ba ai dama mun kusan komawa makaranta(ATBU)," umma tace "ai dama ba inda zaki sake zuwa daga yau haka kawai ya daka min 'ya a banza wlh dan kince kar aje ne in bahaka ba nida kaina zanje inci masa mutunci daman ai beyi kalan mutunci ba shu'aibun nan da kunnuwansa kamar satellite," abba yace "ya isa haka toh bar kuka ummata jeki huta a daki" tazo wucewa baaba tace "daidan ki knan" harara Saalihah ta watsa mata sannan ta shige daki ta dau tsumma ta goge robe din tare da fadin "Oh ni shegiya Saalihah." Se 6:15PM Sa'ad ya dawo daga islamiya abakin kofa ya hadu dawani gaye ya tambayesa "kaine Sa'ad ko?" Sa'ad ya gyada kai, gayen yace "toh kashiga kayi ma addarka mgn kace mata aliyu na mata sallama kaji? Hungo wannan" ya mika masa hamsin Sa'ad ya amsa "nagode baran kira ta" sanan ya shige "adda Saalihah! Adda Saalihah!" Yana kollamata kira, Salihah dake daki ta amsa da "meh? Meh? Kudi xaka bani kake kolla min kira haka?" Nanne ya kariso dakin, "wai aliyu na miki sallama a waje," Saalihah tace "ban ce maka duk wanda yazo akan machine kana ce masa ban gda ba? Eh? Dan banzan yaro kawai,"  "kiyi hkr adda Saalihah na manta ne,"  "dama ai that is what u are good at mantuwa da amalala fice min daga gani," hijabinta ta dauka ta fito yana tsaye a bakin kofar yana jiranta, sallama ya mata taki amsawa yace "haba Saalihah sallaman ma baraki amsa ba?" Budan bakinta wai "toh ai ba sallaman arxiki bane, dan arziki ne se in amsa ko ka taba ganin talauci yayi sallama an amsa?" Shiru aliyu yayi "toh yi hkr Saalihah Allah huci zuciyarki, ya kke?" Tace "abinda ya kawo ka knan, jin lfyta? Toh i'm fine thank you ni zan koma ciki,"  aliyu yace "haba Saalihah ya kke ma mutane haka ne? Kina yayyafa ma zuciyarki ruwa mana" Saalihah tace "to min wa'azi nd waye mutanen? Ai talaka ba mutum bane a guna, aliyu in kanason in kula ka kaje kayi kudi tana murza yatsotinta, bye!" tana kaiwa nan ta shige gda.**
         Washegary bayan sun gama karyawa Saalihah tana zaune a tsakar gda dawata mafici a hannunta tana fifita abba yashigo "Saalihah ashe nxt week zaku koma makaranta?"  "Eh abba" ta fadi, abba yace "toh shine baki gaya mana ba afara miki shirye shirye?"  "Toh ai abba naga ba kud'i ne kuma kasan ATBU'n nan akoi 'yan masu kudi," abba yace "haba uwata karkiji komi" dubu biyar ya ciro a aljihunsa "hungo wannan kuje kasuwa da umma kusiyo miki akwatin gauro da dan kayan abinci ko uwata? In shaa Allah zanyi aiki sosai nikuma in na kuma samun kudi akaro miki cafanin," amsa tayi tare da fadin "toh angode," abba na shigewa daki taja tsuka "mstww N5000 ce zata min cafanin zuwa babbar makaranta kalan inje a raina ni, I have to think of a way" nan ta shige daki taje ta dauko kayar sallan ta dake karkashin akwatinta tasa ta sha kwalya irin na kauyawannan aka yi ja gira da bakin kolli, aka zagaya baki da bakin kolli still sannan aka shafa powder'n bud'a jaka zainab dinnan fuskar tayi dadadau! Bayan ta daura kanta tayafa gyalenta sannan ta fice ba tare da kowa ya ganta ba bata tsaya ko inaba se New GRA, daidai gabar wata makekiyar gda mansion ta tsaya wanda bata ma san me gdan ba itade ta sallami me napep ta zauna daga dan nesa da gdan takusan 20mins a gun sannan wata prado tafito dagani mutumin gdan ne dattijo ne meh kimanin 58-60yrs gaban motarsa Saalihah tasha brake ya taka da karfi, wasu mutanene dasuke zazzaune a bakin wata shago suna kallonsu, honk mutumin yakeyi amman sam Saalihah bata ko motsa ba dan haka yafito daga motar yana masifa "mahaukaciya ce ke daza kizo gaban mota ki tsaya?" Atake Saalihah ta fara kuka "amman Allah ya isa alhj ynxu fisabillillahi seka gudu jiya in ne meka in rasa ka? Toh wallahi thank god amman kwatancen gdanka kabany kudina kokuma in tara maka jama'a anan." Dan yadda ran mutumin ya baci besan sanda ya kifa Saalihah da mari ba nan tafra ihu "jama'a kuzo ku taimakeni," mutanen dasuke zaune a bakin shagon du suka kariso suna tambayan lfya, kafin alhj'n yayi mgn Saalihah dake zubda hawaye abin tausayi tace "wannan mutumin ya kwana dani jiya yaki biyana kudin kwana ya gudu saisa nazo yabani kudi na ynxu," nan mutanen suka fara "haba alhj taya zaka kwana da ita baraka bata kudin ta ba?" Wasu suna fadin "ashede alhj'n banza ne toh wallahi kabata kudinta," alhj daya rasa me ke masa dadi yace "nawane kudin naki?" Saalihah tace "ya kake tambaya kamar bakasani ba? Ina akan dubu hamsin mukayi da kai," cikin motarsa yakoma ya ciro bundle din N500 ya miqa mata "hungo kinyi ma kanki," take Saalihah ta amsa  tana ma mutanen godiya, napep ta tsara ta fice mutanen gun kuwa se zagin wannan alhj suke kasancewar dama bayi da kirki ko kadan kansa da family'nsa kawai yasani*** tana isa gda ta tusa kudin cikin skirt nata umma tafito daga daki tace "ina kkaje Saalihah? Keda zamu fita kasuwa dake," Saalihah taja hannunta zuwa daki taciro bundle din kudin zaro ido umma tayi "ke Saalihah sata kka fara?" Shu'umar murmushi Saalihah tayi "ko kadan umma dogon zance ne kede ynxu muje kasuwa mu min siyayyan makaranta amman fa kar ki gaya ma abba daman ya bani dubu biyar daxu." Umma tace "toh barin dauko mayafi na"

No comments: