Saturday, 8 April 2017
KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
written by miemiebee👄
0⃣6⃣
Tafiya suka soma a hankali yake driving very gentle AC na huran saalihah har wani bacci bacci ta soma ji, yace da ita "gashy ban san sunanki ba," bayan hamman datayi tace "Ummi suna na," guy din yace "i'm Ibrahim, so a nan area'n kke?" Saalihah tace "a'a nazo gdan aunt dina ne," Ibrahim yace "ayyah ta ina zamubi? Saalihah tace "nxt corner din zamu shiga," Ibraheem yace "wow ashe muna layi daya dake," azuci Saalihah tace "meneh? Layi daya? Yau akeyinta"...wayarsa ce tafara ringing, "excuse me" ya fadi sannan ya daga "hello ya ka gama laundry dinne?" On the other side mutumin yace "eh honourable dan gdan chairman"...ras maganan ya fada kunnen Saalihah da tuni gumi yafara qeto mata ita da take cikin AC, tace a zuci "yau kashin Saalihah ze bushe i have to think of a way, what do I do now?" Tana cikin mgn nan Ibraheem yace "ummi pls zaki danyi yi hkr zanje in amso kayakina a wani dry clean anan yanzu ze rufe shagon ko gdan naku na kusa ne in saukeki?" Saalihah tace a zuci "ka saukeni kokuma asiri na ya tonu?" "a'a muje no problem" yace "yawwa" sannan ya juya kan motar adaidai gaban wata dry clean dake dutsen tashy ya yi parking tare da fadin, "ina zuwa" tace "toh" ya bar motan ma a kunne sanda ya shige shagon sannan saalihah ta fara bude bude cikin motar har tasamu wasu kudade masu uban yawa N1000 ne sabi ta diba masu yawan ta bar masa k'adan tace "wai ashe uban nawa nada kud'i sosai, yi hkr dan samari kanada sunan mahaifina banso maka haka ba kawai banida option ne, nasan inda kaine a situation dina motar gabadaya zaka sace" tana kaiwa nan ta fice amotar da gudu ta tsari napep a daidai shagon daxu ya sauketa tace da me shagon "gashy mallam kaatin daxun ne ashe mtn ka bayani nikuma glo nikeso," me shagon yace "toh ai akoi glo din ma" a zuci Saalihah tace "ji maye ni kudin nikeso ba katin ba" yana dubawa cikin ikon Allah se ba glo din wata hamdala Saalihah tayi "toh bani kudin kawai zan duba wani shagon" ba yadda ya iya haka ta mayar masa ya bata N3000, daman keke napep nata na jiranta se unguwan zango tayi.
Bayan Ibraheem ya amso kayakinsa ya matso kusa da motan se bega ummi ba (dan haka tace masa sunanta) yace "toh ko ta dan fita sayan abu ne baran jira ta" yayi kusan 10mins a gun yaga de ba shadow'n ta yana bude inda yake ajiye kudadensa dan ba ma me dry clean din kudinsa yaga shar an kwashe tas kwata kwata N5000 tarage masa***isan Saalihah gda ta tsaya a wata shago ta siya katin mtn na N400 tace "'yar dubu biyar dana rage maka zata dan rage ma bakin ciki" tayi wata shu'umar murmushi sannan ta shige gda**** Ibraheem ya ma rasa daga ina ze fara ihu ashede barauniya ya kwaso, N2000 ya mika ma meh laundry din sannan ya koma gda yana meh ja ma ummi (Saalihah) Allah ya isa!, ya bi gdajen arean kap amman ba ummi, ummin da aka nuna masa ma ba ita ce ta daxun ba.
Zama tayi ta soma irga kudin a dakinta yakama N45,000 Saalihah tace "ko a babu zanje in siyo zannuwa indan dinka kamin abude makaranta, nd waya ma ai yakamta in siya waya," nan ta irga dubu ishirin ta ajiye a gefe "wannan na waya, ragowar kuma na kaya."
Bayan ta idar da sallan la'asar taci abinci ta fita se central ta kwashi zannuwa irin y'an N2800 dinnan guda hudu a gun tasamu tailor erin tailorn zamaninnan suka daidaita kan ze mata dinkin kan N2000-N2000 haka tabasa advance akan nxt week zata zo ta karba. Daga can ta wuce faridah comminication ta siyo wata Infinix sabuwa pil! Sannan ta dawo gda, su umma suna zaune a tsakar gda tamusu sallama, baaba tace "daga ina kuma Saalihah?" Saalihah tace "ji baaba de wata kawata ce ake suna agdansu shine naje acan fed lowcost," umma tace "toh sannu da zuwa" Saalihah ta shige dakinta, daman da wuta nan da nan ta ciro wayar ta sa sim nata ta hada sa a charging.
Around 6:15PM Sa'ad ya dawo daga islamiya yau ma kamar ranan ya hadu da yunusa a bakin kofa, yunusa yace "Sa'ad dan ma Saalihah sallama kaji?" Sa'ad yace "a'a wlh ba ruwana tace in mutum yazo akan bajad kar in kira ta," yunusa yace "tohh haka tace? kace mata tayi hkr tafito dan Allah," Sa'ad yace "uhm uhm fa zata dakeni," yunusa ya basa hamsin "ungo barata dake ka ba," Sa'ad ya amsa "toh" yashiga ciki abakin kofar dakinsu da Saalihah yatsaya yace "adda Saalihah wani na miki sallama a waje," Saalihah dake danne danne a sabuwar wayarta, tace "da me yazo?" Sa'ad bema ji tambayan da ake masa ba yace "laaa adda Saalihah kinyi waya ne?" Pillow ta wurga masa "shegen dogon baki tona min asiri kaji dadi dan banza kawai nace dame yazo?" Sa'ad yace "nima bansani ba, adda Saalihah to kibany dayan wayarkin," Saalihah ta kyal kyale da dariya ai baran baka ba se randa kadena amalala," Sa'ad yace "toh wlh zan dena," tace "dan banza ashe dama dagan gan kakeyi, naji zan baka sauran kaje ka gaya ma umma ko abba ko wancan baabarka me hassadan kan nayi sabuwar waya gaka abinda zan maka," Sa'ad yace "baran fada ba" ya fice yana tsalle adole za'a basa waya. Gyalen daxunta ta yafa ta dau infinix nata harda sa earpiece a kunne ta saci hanya tafito ita a dole ajeborr ta na fitowa waje taga yunusa wata tsuka taja "dama kaine shine Sa'ad yace min besanka ba lalle zanci ubansa yau," yunusa yace "haba Saalihah mesa kke haka ma wanda yakesonki ne? Walaqanci fa ba abar yi bane, kawai dan zaki shiga babbar makaranta seki fara walakanta mutane" Saalihah tace "toh malam yunusa kaga can?" Tana nuni da yatsa "masallaci ce in wa'azi kakeson yi sekaje can kayi harda loudspeaker akoi aciki yadda duk 'yan zango zasu jika," yunusa yace 'ni bahaka nake nufi ba" ynxu ne ya hango wayar hannunta yace "Saalihah waya kkayi?" Tayi kamar bata jisa ba erin hot babe tana jin waka a earpiece dinnan. Sanda yakuma nanata abinda yafada sannan taciro kunne daya eh sabuwar wayace, yunusa yace "toh yayi kyau a ina kka samu?" Saalihah ta qyal qyale da dariya "yau ni Saalihah ina ganin ikon Allah irin ga barauniyar nan ko? Harda wani a ina nasamu to sacewa nayi yunusa, dama mutane haka suke, bakada kudi ba a barka ba ka fara samun budi still barasu barka ba, toh ynxu kam ko wayoyinmu aka hada za'a san niba class dinka bace, nafi karfin class naka ynxu yunusa ga can gdansu ameenatu kaje ita kan zata kula ka bansan sake ganinka abakin kofar gdan nan, dan abin kunya ce ace babbar yarinya kamar ni ina tsayuwa dakai," tana kaiwa nan ta shige gdah
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment