Saturday, 8 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


     BY MIEMIEBEE
PAGE 14


    Ameenatu tace "haba Saaly baki masa yayi yawa ba kuwa? Wlh yunusa na sonki" wani kallo Saalihah ta watsa mata "so na? Erinsu T boy, alhj na mata, abdul, aminu d.s suce suna so na se shima yace yana sona, Nayi adalci knan? Ai yunusa kam sede erinsu ku  nikam na masa wuta dayawa." Ameenatu tace "mgnar ki dutse Saaly, to na raka ki baran koma gda" ahaka suka yi sallama. Saalihah na shigowa gda taga abba a tsakar gda yana xaune da baaba a gefensa. Sallama tayi amman sam taga fuskar abba ba walwala a zuci tace "hegiya baaba fatsuma har kin gama kulle kullenkin knan karki damu Saaly baby zata warware komi!" Nufowa tayi gun abba ta gaishesa cikin ladabi da biyayya, abba yace "haba uwata, me haka? Erin tarbiyyan dana  baki knan, dubi harda gashin doki a akanki, kinsan ko Allah ya tsine ma duk wanda tasa gashin wani abu a kanta."
         Saalihah ta qyal qyale da dariya "yanzu abba har ka yarda da abinda baaba ta gaya maka? baaba fa bata san me wannan ba, gashi na nefa wani mai na saya wanda yake ta da gashy shine fa gashin yayi tsayi haka" abba yace "toh mesa gashin ja ba baki ba?" Saalihah tace "oh! abba na, dying nayi mana ai ana dying gashy har purple ma kwanaki na mai dashy." Baaba tace "wlh ibro karya take kar kaji mgn wannan makaryaciyan." Saalihah tace "ynxu baaba nice makaryaciyan? Abba dubi fa dubu biyar na bata amman tana cemin makaryaciya tun ba yau ba nasan baaba bata sona kuma ba wai wani laifi na mata ba, am doing all I can dan tasoni amman sam taki." Abba yace haba hjy fatsuma, Saalihah fa uwarki ce kuma harda kyautan dubu biyar ta miki kke ce mata makaryaciya gaskia banji dadi ba," yadawo da dubansa kan Saalihah "amman uwata yanaga kin kara fari ko mai kka fara shafawa?" Baaba tace "ahtoh zaka fada ai!" Saalihah ta watsa mata harara tace "mai kuma abba, kasan wani foundation da ake siyar wa dubu goma a kasuwa? Toh shine fa in ka shafa se fuskarka tayi fari amman kana gogewa ze dawo kalan da, haba inyi bleaching."
        Abba yace "ai nasan da hankalinki 'yata toh ya karatu?" Ta ciro wallet nata tana irga kudin tace "alhamdulillah ina sa kai sosai abba, ungo wannan dubu talatin ne mijin dake son ya aure ni ne yace in baka," hannu na bari abba ya amsa 'dubu talatin? Min? Toh nagode Allah saka da alheri ya tabbatar mana da alheri. Yaushe xaki kawo mana shi mu gaisa," Saalihah tace a zuci "anzo wajen." "Haba abba ai ba haka akeyi ynxu ba seyaga kamar so nake ya turo mude barsa dakansa ze xo kuma ai bamu jima dashi sosai ba," abba yace "toh shknan nagode ko uwata, Allah miki albarka" yana kaiwa nan ya shige daki.
                     Saalihah ta dawo da kallonta kan baaba "ande ji jiki toh gashy na warware komi" ta watsa mata harara sannan tayi dakinta. Around 2:15PM umma ta sauke abincin rana jollof din shinkafa ne ba nama ba komi salam dinsa. Sa'ad ne yakawo ma Saalihah abincin tana bude wa harda toshe hanci "me wannan?" Sa'ad yace "abinci mana adda Saalihah" Saalihah tace "kai kar ka sake cemin Saalihah gajy? Adda Saaly xakana cemun, fadi inji."  Sa'ad yace "adda Saaly" tace "yawwa dan gari ga dari biyar kaje kata shan alawa dashy" ya amsa yana tsalle tsalle. Wayarta ta ta bude ta kira driver'n da alhj na mata ya bata da ya siyo mata fried rice da chicken plate hud'u, "toh angama" yace. Bayan 20mins se ga honk a bakin kofar gda gyalenta ta yafa ta fita ta amsa tare da mika masa kudin sannan ta shigo ciki ta nufa dakin abba ta ciro takeaway "daya ungo abba, umma kema gashy baaba kam bata iya cin erin wanga abinci ba sesa ban siyo dake ba. Uumma ga wannan na Sa'ad inya dawo seki basa." Abba daya bude yaga wata makekiyar kazan dake masa sallama yace "Saalihah daga ina kuma?" Tace "shide wandakeson aure nanne ya turo driver ynxu ya kawo mana abinci." Abba yace "Allah sarki dan albarka ya sunansa?" Take Saalihah ta hada suna a brain nata "Aliyu sunansa," abba yace "toh kice masa mun gode, hajara jeki juye wannan shinkafan a tukunya ko zuwa gbe semu dumama mu karya dashy ynxu de bari muci wannan ta gayun." Baaba tace "lallai Saalihah nice ban iya cin abincin gayu ba wato?" Saalihah tace "eh mana baaba kefa da bakinki kika gaya mun, shaa in kinaso seki sami abba kuci tare amman de karki taba na umma." Abba yace "bismillah muci hjy fatsuma."
       Dakinta ta koma taci abincinta ta kora da maltina sannan ta dau wayarta yanzu Fudail in ban kirasa ba bare kirani ba wlh da kasan yadda nakesonka da baraka na min haka ba upon all wanda suke fadin suna sona kai kawai naji ka kwanta min a rai bansan ya zanyi kafara sona ba Fudail. Barin duba last seen naka muga nan ta hau whatsapo tga last seen nasa 3mins ago"... Kiransa tayi direct har ta tsinke be daga ba se a karo na biyu "hello Saaly" ya fadi tace "Fudail wato in ban kiraka ba u have no intentions of calling me ko?" Hayaniya sosai akeyi a inda Fudail yake data kasa kunne setajiyo muryan mata, "Fudail ina kake right now?" Fudail yace "gda mana why do u ask?" Tace "qarya kake gashy nan duk hayaniya wace bitch dince kusa dakai kuma, haba Fudail kacemin fa zaka barbin mata." Fudail yace "toh kedin kinbar bin maza ne? Kowa yaci duniyar sa da tsinke kawai let me be," Saalihah tace "toh ai kaima kasan ina sonka sauran kawai ina kulasu ne dan banason walakanta mutane, but deep inside my heart kai kadai nikeso." Fudail yace "toh ai kema kinsan I love you stop worrying yourself you are the only one my love i'll call u back later," yyi hanging.
         Can dare around 9:30PM NEPA suka dauke wuta, dan fankan dake hura Saalihah yadeba gashy ta saba da AC ybxu cuz dakinsu na makaranta AC suka siya suka sa, haka tata dura ashar da daren ranan ita barata iya ba da kyar tasamu mafici ta dan rage hanya se kusan to 2 tayi bacci dan waya da samarin da take tayi.
              Washegary! Se 11:20AM Saalihah ta tashy daga bacci toilet ta fada ta yi brushing sannan tafito da sleeping dress nata a jikinta taga baaba na xaune a tskaar gda tana karatun Qur'ani kallo ta watsa mata sannan ta nufa kitchen taga dumamen shinkafan jiya wata tsuka taja tafito tana wank tura baki, har ta kai izuwa kofar dakinta baaba tace "Saalihah" banza tayi da ita Saalihah bake nake kira ba" sanda ta kira sunan sau hudu sannan Saalihah ta jiyo "meh meh? Nifa suna na ba Saalihah bane in bara kice min Saaly ko Saaly baby ba to dont mind calling me" tana kaiwa nan ta shige daki tabar baaba da baki a bude, sbd tasan both abba da umma basu nan sesa take ma baaba rashin kunya iya san ranta. Wayarta ta dauka ta kira driver daya siyi mata breakfast chips nd egg kamar jiya bayan 20mins ya iso tabasa kudin sannan ta zauna a tsakar gdan tana cin chips nata ko tayi wa baaba batai ba nd sarai tasan baba anyi kwadayayiyya kadan ta ragar ma Sa'ad. Takoma daki tayi wanka tasa wata atamfarta holland data saha dinkin gayu ta cancare kwalya tayi daurin ntwrk ta ciro attarchment natan kaman najiya sannan ta leko bakin kofa inda rana yake tana kokarin daukan hoto sede ina background na gdan na bata mata selfie'nta (lol) tsuka taja "wannan wani erin gda ne ace ko background me kyau na posing ma babu mstw wlh ni yau zan tafi kekuma baaba ya da kallo haka? In kyau na miki just admit it ki gayamun ba ki tsaya kina kallo na kamar gunki ba," tana mgnan ne tana seta canon cameran dake hannunta ko zata dan samu background me kyau ta kashe hoto!

No comments: