KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
written by miemie
15 part 1
Haka tata changing waje amman sam ba background daya
mata, daki takoma takira ruky suka sha hirarsu can takira bint
suka gaisa harda phaary dake suna tare, xafi ne ya dameta a
dakin dan haka tafito waje ta shinfida wata sallaya tazauna,
baaba ma na bakin kofar dakinta tana shan iska, basu ce da
juna komi ba. Can ishi ya addabi Saalihah kitchen ta nufa
dakyar ta iya tashah ruwan randan adole ita ta saba da faro
ruwan gora. Iphone nata ne yasoma ringing da sauri ta karaso
taga abdool na kiranta kafin ta daga infinix dinma tafara
ringing shikuma aminu ke kira murumushi tayi sannan tadaga
duka biyu "seni shgya Saaly baby" ta kalli baaba dake kallonta
itama jinki dan kina kallo na barin daga bane, swiping tayi ta
daga duka calls din at a time. "Hello dear?" Tace, Abdool yace
"baby ya kke?" Aminu kuwa cewa yayi "daxu nazo hostel naku
baki nan, lfy?" Saalihah ta rasa wata amsa zata basu can tace "
hello? Hello? wlh dear ntwrk ba kyau kuma ina dan wani abu
kadan ynxu anjima zan kiraka bye!" Baaba tace "lalle Saalihah
waya biyu kke amsawa a lokaci daya?" Saalihah tace "meh?
Ko kishin farin jini na kke, samari suna sona se in kisu?" "Allah
shryeki toh, kuma bakiga shabiyu ya wuce bane? Baraki aza
mana girkin rana ba?" "Qyal qyal qyal! Ni kkeso in hura wancan
tsinannen murhun? Da nake Saalihah ma ban hura murhun can
ba sedana zama Saaly? Lalle zancen kkeso" tana kaiwa nan ta
shige daki ta soma hada kayakinta.
Bayan azahar umma ta dawo daga kasuwa alokacin Saaly ke
fitowa daga dakinta yau kuma wata abaya tasa erin wanda tun
daga sama a buden nan tasa wata top da pencil trouser taciki
seta daura kanta da gyalen ta ciro attarchmnt nata ta gefe
tasha wasu mahun hills.
Tace "yawwa umma har kin dawo? Dama tafiya xanyi the
driver shud be here by now.." Bata gama mgnan ba driver yayi
honk. Umma tace "toh Saalihah ta ko abinci barakici ba zaki
tafi?" Saalihah tace "karki damu umma zan tsaya a hysaan
chicken in siya kaza in ci" tana mgnan tana kallon baaba.
Dama already ta irga dubu goma ta mika wa umma "gashy
kidan siya koda maltina kina sha, ga wannan" dubu daya ta
mika mata again "kibawa Sa'ad in abba yadawo kice masa na
tafi" nan tayi hugging umma, umma ta mata Allah kare sannan
ta fice.
Har gaban ATBU driver ya sauketa a daidai lokacin Fudail yake
fitowa daga sch nan suka had'u ya tambayeta kotaci lunch
tace "a'a" yace "oya love lets go nd eat" shi ya fito ya bude
mata gaba tashiga ya amshe akwatintan yasa a booth sannan
suka fice. Acan suna hirarsu na masoya se yaba kyan Saalihah
yake ita kuwa tana blushing ahaka sukayi having lunch nasu
cike da soyayya, bayan da suka gama ya tambayeta koda
abinda takeso tace shes fine. Har bakin kofar dakinsu ya kaita
yabata peck a kumatu abinku da shaidanu sannan yayi
tafiyarsa, Saalihah kam takasa rufe baki dan murna tunda suke
da Fudail be taba burgeta kamar yau ba, sansa taji tanayi like
nva before. Koda tashiga bakowa a dakin har malama
khadeeja ma batanan. Kayan jikinta ta rage sannan ta kira alhj
na mata suka gaisa tace "alhj na wlh wayata aka sace ynxu
dawowa na frm welcoming back sim dina". Alhj yace "toh ai
wannan ba abin damuwa bane ynxu zakiji alert" Saalihah tace
"kai alhj kar ka damu akoi dayan ai a hannu na" alhj yace "ai
na gaya miki kinfi karfin infinix, ynzu zakiji alert" "kai baby na
nagode sosai Allah bar min kai," yace " Saaly harda zolaya ne,
nine baby?" Saaly tace "alhj nawa knan ai tamkar jariri kake a
idona ni ban ganin tsufanka ure a baby to me" alhj yace
"gaskia zancen ki ya cancanci kyauta" haka sukata hira
saalihah nata cika ma alhj kunne da karyan banxa ahaka sukayi
sallama. Ko cikakken 5mins da gama wayar basui ba alert
yashigo na tana dubawa taga N200k. Kiransa tayi ta masa
godia yace "ba komai ko Saaly ta, yau zamu iya haduwa?
Kinsan har na fara missing kyakkyawar fuskarki" Ta amsa da
"sure my baby ba matsala Allah kaimu yau akoi wankan da zan
maka na musamman" alhj yace "toh Saaly baby ina jira nikuma
akoi kyauta na musamman da zan miki nima"
Can da yamma around 5:45PM su phaary suka dawo bayan
sun gama hugging Saaly tace "yawwa yau zani gdan alhj na
mata ko zaku?" Bint tace "eh sosai mah, jiya bamuje ba ai"
Saaly tace "toh se ku shirya ko ameenu yace zeyi dropping
dinmu" Phaary tace "yawwa yar gari". Around 9:15PM bayan
har sun gama shiri suna jiran ameenu, ruky ta kira Saaly "hello
Saaly babban harka ya taso akoi wani alhj'n da zezo daga jos
yau kibar duk abinda kkeyi ynxu kizo" kafin Saalihah tayi mgn
ruky tayi hanging. Ta rasa nayi "shin nabi su phaary ne kokuma
naje kiran ruky, kai gaskia kiran ruky dan kowani kiran ruky
alheri ne a gareni".
"Gurls somethng more important came up in aminu ya iso
kawai ku tafi koda kun hadu da alhj na mata kuce masa inada
project ne gbe sesa ban samu zuwa ba". Phaary tace "toh but
meya faru?" Tace "in nadawo zaku sani bye!" Ta fice napep ta
tsara yakaita inda suka saba haduwa da ruky as usual 'yan
mata ko kuma in ce karuwai sun jeru a bakin layi suna jiran
adauke su kwana. Ruky ta kira a waya "emmata gashy na iso"
ruky tace "toh gani zuwa" nan suka hadu.
No comments:
Post a Comment