Saturday, 8 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemie👄
                  1⃣3⃣



          Saalihah ta ciro sunglasses din tare da kada kanta attarchment din nawani dama da hagu, baki wangalau su umma suka bude suna kallon ikon Allah anya kuwa wannan ce Saalihar su? Daga bisani Saaihah tace "wai meh haka sekace yau kuka soma gani na, kai Sa'ad zoka kaimin wannan akwati daki" har ynxu bakinsa a bude yaja akwatin izuwa daki. Saalihah tace "wai umma harda ke kema? Dama baaba kam ashirye naxo mata dan tun ba yau ba tana min hassada balle ynxu danayi kayan hassada dayawa semu san ya zatayi, da Allah baaba rufe bakin kiga fa digan miyau kke" a zuci tace "nasan abinda ze rufe miki baki" wallet nata ta ciro ta miqa wa baaba dubu biyar "ungo inji saurayina na baki nasan matsalarki kenan kudi, amshi mana?" Nanne baaba ta rufe baki ta amsa ta irga "dubu biyar? Toh angode amman saalihah kece kuwa?" Saalihah tace "a'a ba baaba fatsuma ce" wayarta ce ta sona ringing, tana dubawa taga T boy, ba kunya ta daga agaban su umma "hello baby yanzu shigowa na, i'll call u later."
           Baaba tace "naga wani farin da kka kara ne ai kuma a baqa nasanki". Saalihah tace "toh baaba gayawa duniya bleaching na fara ni wlh kka cika min kunne ynxu zan sa driver yazo ya daukeni inje in sauka a htl, kai Sa'ad fito min da akwatina".
           Umma ce tace "haba Saalihah share baaba da Allah shigo shigo sannu da zuwa," dakin Saalihah suka shiga umma tace "Saihah gya min meke faruwa?' Tana taba attarchmnt na Saalihah, Saalihah ta kau da kanta "me haka umma? Bar taba min gashy mana," umma tace "ni hajara ina ganin ikon Allah Saalihah yaushe kkayi gashin nan? Gashin doki nefa akanki, uhn uhn Saalihah kibi duniya a hankali bansan rayuwarki ta kare miki kamar"...sekuma tayi shiru "kuma baki kai haka haske ba, dubi? Fuskarki bata fi nawa haske ba ynxu mai kka fara gogawa?" Saalihah data cike tam ynxu tace "gaskia toh tfiya zanyi" taciro iphone nata nan ma umma ta tsaya tana kallonta dan inba ance waya bane bara'a zata wayan bane dan wata porche data sa masa, wayar umma ta amsa "haba Saalihah ta takaina, meyayi zafi da zaki tafi? Kawai ai banyi tsammanin haka zaki dawo gdan nan bane"...dubu ishirin Saalihah ta irga wa umma "ungo kema inji saurayina yana gaishe ki," umma zata yi mgn Saalihah tace "barin dan huta ko umma? Anjima semui mgn" da wayo ta tura umma waje tayi wata ajiyar zuciya.
      "Oh! ni Saaly mehaka dan Allah?" mirror taciro a jakarta tana kallon fuskarta "wai na canza dayawa ne? Mstww barin je gdan su ameenatu ita kadai zata gaya mun gaskia."
               Fitowa tayi daga dakin setaji muryan baaba a dakinta dan haka ta nufa kofar dakin sidak sidak ta kasa kunne tana sauraronta. Baaba tace "ynxu ke hajara kina ganin abin da kkeyi kina kyautawa knan? Kibar 'yarki tanayin abinda taga dama, kiganta sekace ba yar muslima ba kuma kina nan zaune kinajin dadi wlh in bakiyi wasa ba se yarki ta ninka abinda kka aikata da kke kamar ta." Saalihah tace wani "abu knan?" Tade cigaba da sauraron baaba amman sam baaba bata ambata abinda umma tayi back then da take da shekaru kamar Saalihah ba. Dakin ta shiga "to baaba uwar hassada naji komi, ki xageni ki zagi uwata amman in na baki kudi kuma ki amsa, Allah de ya sauka, umma ni xani gdansu ameenatu sena dawo" umma tace Allah kare " 'yata" amin tace sannan fa fice se taku take bazawa kan hanya duk 'yan unguwar sun kasa ganeta, daidai gaban gdansu ameenatu ta tsaya tayi sallama sannan ta shiga ameenatu na wanki a tsakar gda taga Saalihah itama kamar barata ganeta ba ta farko, tsalle ta daka "Saalihah! oyoyo" dagudu tayi hugging nata "yaushe a gary? Shegya Saalihah kyau knan wannan gashin fa? Kut ji wani kamshin da kkeyi ke wlh daba dan mun saba ba wlh da baran ganeki ba, kin ganki kuwa kawa? Sekace daga america."
          Saalihah tace "kai! da Allah banson zolaya fa mushiga daga ciki nan rana." A dakin ameenatu suka xauna ameenatu tace "barin kawo miki ruwa," Saalihah tace "no dont bother daga gda nake," ameenatu tace "kar ki gaya mun haka kka shiga gda iyayenki suka ganki," Saalihah tace "lol toh meh? Ai ni barin munafurta iyayena na ba, kinga dama umma batada matsala, abba kuwa be waye ba in nace masa gashy na ne yarda zeyi, wannan hegiyar baaba fatsuman ne". Ameenatu tace "a kullum ina gaya miki bakici sunanki ba Saalihah," Saalihah dake murmsuhi tace "ai yanxu na tashy daga Saalihah na koma Saaly baby," ameenatu tace "ban mu kashe"...haka sukata hira Saalihah naba wa ameenatu irin barnan da ta aikata, datazo tafiya tabawa ameenatu dubu biyar, ameenatu ta amsa tana mata godiya. Suna tafiya tare kasancewar ameenatu na mata rakiya se wata bajad tasha gabansu daga idon da Saalihah zatayi taga  yunusa, kallonta yake sekace yau ya soma ganinta "mallam ya haka? Kazo kasha gaban mutane da machine bama mota ba, ko so kake ka nuna min kayi machine Allah sarki to atsufar lfya sede naga kamar tyre'n gabanka a sace yake" dubu biyar ta irga tasa masa a cikin basket na gaban machine din "kaje kayi paci dashy change da ya rage kuma kasa kati," ameenatu da ta tsaya kallon ikon Allah, Saalihah tace "muje ko ameenatu?" Yunusa ya rasa na fadi yace da kansa "wannan itace Saalihah? Saalihan dana sani? Gaskia kinfi karfina ynxu badani ba auranki duk yadda nakesonki dole inja da baya, Allah xabar ma kowa mafi alheri!"

No comments: