Thursday, 13 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemie👄
                  2⃣7⃣



             "Daddy'n Fudail karkayi blaming d'ina kan abinda na maka kasan nayi hakan ne dan ina sonka, nasan ko a babu ina da cikinka a ynxu kaga da haka abbanka dole ze yarda ya mana aure, much love"
         "Zafaffun hawaye ne suka soma zubo min what does she mean? Tana nufin mun aikata zina knan? Innalillahi!... Tun daga ranan ban sake sa Hajara a ido na ba nikuma ban gaya ma kowa abinda yafaru tsakani na da ita ba. Hanki na na mayar kan iklima soyayyarta kuwa ba karamin burgeni yake ba duk yadda tayi ka fara sonta sam kak'i kullum cikin tambayana kake ina anty Hajara.
          ONE MONTH 5 DAYS LATER;
 GIDAN MALAM GIDADO;
     Ana sauran wata biki na da mummy'nka knan. Fitowa daga bayi Hajara tayi se share bakinta take da alaman amai ta kwararo dab da shigowar ummanta knan. Nan tayi kanta "Hajara! Ya haka? na lura tun kwanaki hud'u da suka wuce kike amannan lfya daiko?" K'arfin hali Hajara tayi sannan tace "eh umma kawai nikega zazzabi ne", "d'ago ki kalleni" inji umman Hajara da fad'i sam Hajara tak'i dagowa dan karfi umma ta d'ago kanta kallon cikin idanta kawai tayi tahau salati kafin Hajara ta hankara umma takai mata mari, "shikenan kin gama dani Hajara ciki? Ciki fa? A ina kka samu ciki? Wayyo ni Jummai kin gama dani". Hajara dake kuka tace "dan Allah umma kiyi hkr ki rufa min asiri kar abba yasani wlh kasheni zeyi, dan Allah ki rufa min asiri".
         Ras! Mgnan ya fad'a kunnen abba daya dawo daga gonansa da sauri yashigo ciki ya samesu, "menake ji jummai? Waye keda ciki?" Shiru both Jummai da Hajara sukayi, tsawa ya daka wa Jummai "mgana nake miki ko sena illata ki tukun xaki gaya mun?" Hajara se kad'a kai takeyi wa umma da nufin kar ta fad'a masa pls, hannu abba ya d'aga ze mari Jummai nan tace "dan Allah kayi hkr malam wlh nima yau nasani ciki 'yarka takeda".  "Meh??? Ciki? Wata 'yatan?" Ya dawo da kallonsa kan Hajara dake ta kuka "Hajara! Ciki!" Mari ya kaimata nan umma tashiga kare 'yarta tana basa hkr tunkud'ata gefe yayi sanda ta fasa goshinta kan wata kujera, daya kapa dukan Hajara sanda yaga bata numfashi nanma be bari ba ihu umma tarigayi sanda makota suka shigo suka karb'e Hajara data jima da suma, ruwa aka yayyafa mata cikin ikon Allah ta farfad'o se jiri takeji ga jinin dake bulbula aduk wani sassan dake jikinta.
          Abba na huci yace "wlh kinji na rantse billahillazi sena kasheki a gdan nan waye ke da zaki kawo min cikin shegen gda? Duk zuri'ana ba shege ba shegiya seke zaki kafa record to wlh qaryan ki ba'a haifeki ba!" d'aki ya nufa ya d'auko wata adda yanufo kan Hajara dakyar aka iya karba'an addan daga gunsa. "Waya miki ciki nace? Waye?" Shiru tayi tana kuka wani wawan ball yayi da ita batasan sanda takira suna na ba.
          Nan yasata a gaba suka taho gdanmu. "A yadda 'yan unguwa da umman Hajara suka bani lbr knan!" A lokacin kuwa ina zaune da kakanka a parlour muna hira se can me aiki yama abba sallama kan ana nemansa a waje tare muka fito abin mamaki  sega abban Hajara da ita tsaye a gefensa se kuka take zubawa ga jikinta duk yayi shatin zana yana zuban jini. Kafin kakanka yayi mgn abban Hajara cikin b'acin rai yace "wlh alhj dakai da d'anka baku isa ba bayan kunk'i auran 'yata se d'anka yama 'yata ciki? Wlh baran yarda ba ko mu rufa wa juna asiri mu masu aure kokuma in kai k'ara kotu dan baran yarda ba" Kakanka yace "wai me kake fad'i ne malam gidad'o sanin kowa ne 'yarka shahararriyar karuwa ce wayasani ko cikin d'aya daga cikin 'yan iskanta ne zata lak'aya wa d'ana k'azafi toh wlh tun wuri kuje ko nemo wanda yama 'yarka ciki, dan nasan d'ana ba mazinaci bane". Jin yadda kakanka ke ta defending d'ina ya sake karya min zuciya ina me nadaman mesa na shigo da Hajara cikin rayuwata!

    beeenovels.mywapblog.com

No comments: