Saturday, 8 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  1⃣2⃣


          To 12 su bint suka fito,   T boy da Saay kuwa hira sukeyi abinsu, dan ko T boy yamata admitting yana sonta ita ma take tace tana sonsa. T boy da gang nasa ne sukayi dropping nasu, wasu kattin shopping bags guda biyu T boy yaba Saalihah, godia tayi sannan sukayi goodnight wa juna suka wuce hostel. Yau ma haka suka hana khadeeja bacci, bayan da saalihah ta zazzage kayakin taga shopping ne sosai ciki harda bundle din N500 guda biyu. Tace a zuciya "ko a yau na bar ATBU nasamu na kaina! Shgya naira daga Saalihah zuwa Saaly!" Haka sanda tagama cika kayakin cikin wardrobe nata tho saura ma sunki shiga dan yawan kayakin Saalihah ynxu.
         Washegary ita dasu phaary suka je suka siyo mata iphone 6 sabuwa pil tahada wayoyinta yazama biyu ynxu sabon sim ta saya tasa acikin iphone din suna isa hostel ta hada wayar a charging. Infinix inta ce tasoma ringing dubawanda tayi taga yunusa wani dariyan mugunta tasake tukuna, su bint da suke gefenta sukace "emmata ya haka?" Tana dariyan tana mgn "yunusa nefa, wai kirana yake"...phaary tace "lol talaka da maita to me zece miki? Ko besan kedin hjy bace ynxu?" Saaliha tace "bede sani ba tukuna lemmi inform him" sanda call din yakusa tsinkewa sannan ta daga "hello?" Yunusa on the other hand yace "sarauniyar mata ya kke?" Dariya tayi sannan tace "I was fine before naga call dinka," yunusa yace "haba Saalihah shin yaushe zaki san ina sonki ne?" Warning mtn suka soma masa "hello? Ina zuwa zan kiraki"...nan call din ya tsinke take Saalihah tayi calling nasa back "ayya yunusa ynxu ko kudin kati bakka dashy, bari zuwa anjima in na fita zan maka sendn just as charity" kafin yunusa yayi mgn ta katse wayar "shashasha kawai." Alhj na mata takira bugu daya biyu ya daga "hello alhj nawa na kaina," yana jin muryarta yagane itance, "Saaly baby ya kke?" Ta amsa da "qlou, you?" Yace "yadda kke" "dama na kira ne kayi saving number na." Alhj yace "toh Saaly baby ki huta lfya, duk sanda wata matsala ta taso miki feel free ki kirani ki gaya mun kinji my baby?" Saaly tace "wayyo alhj na sisa nake sonka, Allah bar min kai" ahaka sukayi sallama. Bint tace "shgya wani alhj kuma kkasa samu?" Saalihah tace "ina gdan party da muke zuwa?" Su ka gyada mata kai tace "toh ai wannan alhj'n ne me gurin!" Phaary ta zabura "ke dan Allah alhj na mata fa knan, ke bint baki sansa bane?" Bint tace "na sansa mana shgya Saaly kina wuta muna binki da gas bama petrol ba!"
        Kwanaki da dama sunja yau kimanin 3 months knan. Saalihah kam sede abinda ya karu goga rayuwarta take sekace ba muslima ba, ga sata kamar ba gobe duk inda taje setayi sata, saidai duk iskancinta a shafe shafe yake karewa bata taba barin abu yashiga tsakaninta da samarukan ta ba haka sugar daddies nata ma. Ga wani farin data kara dan mai tafara gogawa, attarchment ma sawa take dan rashin godiyan Allah. Duk wanda yaga Saaly baby seya sha mamaki.
      Kasancewar yau public holiday Saalihah tadan shirya kayakinta set biyu cikin wata karamar trolley'nta taci kwalya sosai dawata hadaddiyar doguwar riga a jikinta data sha stone work daura kanta tayi ta ciro wata jan attarchmnt daga gefe ya sauka a bleacaccen fuskarta data sha foundation ta sakeyin pau! Ga wata anniya jan bakin data sha. Side bag da takalmi sak colour'n kayan tasa sannan ta toshe da dark sunglasses dan ranan da akeyi. "Toh babies i'll get going se gbe na dawo" hugging nasu tayi one by one tana musu peck a kumatu, taje zatayi hugging khadeeja, khadeeja tabata hannu Saalihah tace "oh ashe malama ce ke sorry oo bye se nadawo" tana fita bakin gate na ATBU ta kira alhj na mata "hello alhj nawa na kaina gashy fa nafito banga motar ba kuma kasan ana rana sosai," alhj yace "wannan driver nason in koresa wato, taya ze bar min Saaly baby a karkashin rana?" Suna kan wayan sega wata bmw fara tasha tinted ta karaso gaban Saalihah driver'n yyi wining glass "hjy sorry pls wanke motan aka tsaya yi saisa na bata lokaci" yafito ya bude mata kofar baya yasa jakarta a booth. Tace da alhj "shknan ma gashy nan ya iso, i love you" sannan tayi hanging shiga tayi, driver'n ya rufe har gaban gdansu dake zango ya kaita yazo shiga mata da akwatin tace "a'a bari shknan u can go" wata bakar leather ya miqa mata "gashy inji alhj tsaraba wasu mama," amsa tayi tace "toh kace masa thanks" tana bude ledar taga bundle na N500 guda uku harshe tasa akan jan bakinta tana lashewa tana wani fari fari da ido sannan ta karasa taja langa langan bakin kofar gdansu tashiga ciki. Baaba da umma da sa'ad suna zaune a tsakar gda kaman daga sama suka ga Saalihah. Duk suka zabura baaba tace "Saa...Saalihah?" Umma tana "Saalihah kece kuwa?" Sa'ad na "adda Saalihah?"

No comments: