Saturday, 8 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemie👄
                  1⃣1⃣
       
         

            Haka kamar shushushsu Fudail ya kuma cikama Saalihah wata trolley da shopping su bint da phaary kam nasu ido ne. Bayan ya biya aka cika masu manya manyan shopping bags guda uku dam sannan ya basu lift zuwa hstl cikin wata shegiyar motarsa kirar benz M class, Saalihah nata jiran yace ta basa number'nta kokuma card nasa amman sam abin ba haka yake a gun Fudail ba, godiya suka masa sannan suka kira wasu almajirai suka shiga msu da kayakin cikin hostel.
       Khadeeja tana zaune a daki tana karanta wani handout tafara ganin ledojin da ake shigowa dasu tadau ko sabin roommates ma tayi can taga su Saalihah bata ce musu komi ba illa kallonsu da take. Bint tace "salamu alaikum tunda yau malamar tamu bata mana sallama ba," suka kwashe da dariya ita da phaary, Saaly kuwa se bude buden leathers din takeyi tana zazzage kayakin kan gadonta. Ba abinda babu aciki daga kayan wanka, man shafe shafe, cosmetics, turaruka, accessories komi akoi sannan kuma ga atamfofi da laces kusan takwas takwas, ga mayafai, harda shoes. Bint tace "shegge Saaly bamu lbr taya Fudail ya miki wanga sayayya?" Saaly tayi wata murmushi ta gefe sannan tace "kuna wasa da Saaly baby, yawwa nikam yau zamu gun jiyan nan? T boy yace yana son mu hadu." Phaary tace "kinji yar gary zuwa kam consider it done! Allah kaimu 2nyt." Itade khadeeja kai kawai take kadawa tana musu fatan shiriya.
      A wunin ranan Saalihah ta tattara atamfofi hudu da laces hudu ta wuce central kai dinki, acan ma takuma yin sauran siyayya kusan maghrib ta dawo gda suna idda sallan maghrib suka fara shiri se 9 suka gama suka ma malama sallama sannan suka fice zuwa gdan ranan. Kamar yadda gdan yake ranan haka ma yake yau can su bint suka hango wani guy dinda suka sani dan haka suka je gunsa Saalihah kuwa tana zaune ita kadai dan har ynxu su T boy basu zo ba wata budurwa ce tazo ta sameta hi, hello suka dan gaisa, kallo daya za'a ma wannan yarinya asan karuwa ce dan koda erin shirin dake jikinta wata armless top ce sede matsetstsen trouser kan nan ta baza masa attarchmnt Saalihah bata ma dau muslima bace sanda tace mata "suna na rukyy, tun daxu naga kina zaune anan ke kadai shine nace barin zo in tayaki hira dan haka kawai kka burgeni." Saaliha tace " thanks nikuwa Saaly baby suna na, wani nake jira har ynxu bezo ba," ruky tace "I see kafin wanda kke jiran yaxo why not kizo in kaiki gun frnds dina mana kinyi kalan mecin kasuwa," Saalihah najin haka tasan money things ne without a second thought tabi ruky.
        Zuwa wani daki a sama suka tsaya ruky tayi knocking sannan wata tazo ta budemusu dakin cike yake da 'yan mata da samari, waje suka nema suka zauna, ruky tace "a wani sch kke?" Saaly tace "ATBU," ruky tace "ayya nikuma state poly so daman kina zuwa nan often?" Saaly tace "no this is my second time," ruky tace "I see, so kina dan wani harka haka da maza ne?" Cikin rashin fahimta Saaly tace "ban gane ba" Ruky tace "ya kke haka kamar ba 'yar gari ba i mean kina kwana da maza a baki kudi?" Saalihah ta zaro ido a zuci tace "yau nayi gamo da karuwa" sannan tace "a'a," ruky tace "wai amman dadi da kudi sun barki a baya," Saaly tace "Allah ko?" Ruky tace "sosai ma kuwa" suna cikin wannan zance se ga wani alhj ga furfura nan tako ina, akayi wasa ma zeyi jika da Saalihah, dagani erin manyan alhaxai 'yan iska masu bin matan wajen nan ne, zama yayi kusa da ruky tare da tambayarta "wace wannan fresh babe din?" Ruky tace "Saaly sunanta," alhj'n yana washe hakora yace "sannu Saaly ba karya kin hadu" wani kallo Saaly ta masa har tsakiyar kansa ya jiyo kallon.
      Ruky tace "Saaly kinga wannan alhj'n? Shine me wajen nan bara a irga masu kudin bauchi guda uku ba a sa alhj na mata ba! Aciki ba" Saalihah money monger najin ance bara a irga masu kudin bauchi ba'a sasa aciki ba taji kawai she's ready tayi komi dan taci arzikinsa. Ruky tacigaba "i'll leave u two to talk ga card dina ki kira ni," Saaly ta amsa "toh bye!" Sannan ruky ta fice bayan bundle din N1000 da alhj na mata ya bata. Ya dawo da kallonsa kan Saalihah, da take masa wata shu'umar kallo yace "Saaly a ina kke?" Tace "ATBU," yace "wow yayi kyau kinga kamar yadda ruky ta gaya miki in har xaki bani hadin kai xakiyi kudi a gefe na" Saaly bata san sanda tafara lashe lips nata ba, tace "ai alhj karka damu am all yours," alhj'n ga yaji dadi sosai "ungo wannan" bundle din N1000 ita ma ya mika mata, zancen da kkayi anan kawai yamin dadi, Saalihah tace "alhj nawa gaskia kana burgeni nagode," wayarta ce ta soma ringing tana dubawa taga T boy ba tare da bata lokaci ba ta daga "hello? Kun iso ne?" On the other side T boy ya ce "eh baby tun daxu neman ki nake u where nowhere in sight," tace "toh gani nan zuwa" tayi hanging. Alhj "i'll get going frnds dina suna jira na," alhj yace "toh toh, wace erin waya ce a hannunki?" Saalihah tace "infinix alhj" alhj ya dado mata wata bundle din "gashy ki sai iphone da wannan ai kinfi karfin rike wannan" ta amsa zaro ido takeyi dubu dari biyu! No be play thing, "kaii alhj bansan ta ina zan fara maka godiya ba bani number'nka dan muna waya ko?" Alhj yace "mgnan ki daidai," nan yaciro card nasa ya bata tayi godiya sannan ta sauko downstairs inda suka hadu dasu T boy, phaary tace "ya haka ina kkaje?" Saaly wai nadan shiga bathroom ne, bint tace "ayya tun daxun T boy yake jiranki," Saaly ta dawo da kallonta kansa "sorry dear muje waje nan din is crowded yau naga," T boy ya waiga ya waihga yaga fa kwata kwata ba mutane ma yau sosai, yace "ahakan?" Saaly tace "mu fita mana," shi T boy besan wayo take son masa ba kar in alhj na mata yafito ya ganta. Ba yadda ya iya haka suka fita waje suka sha hira.

No comments: