Thursday, 13 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  2⃣6⃣



           Washegarin ranan na raka abba gdansu Hajara a bakin kofa na tsaya shi kad'ai ya shiga bayan 'yan mintina yafito da murmushi fal a fuskarsa, nace "abba ya haka?" Murmushin yakemin sannan yace "gashi nan iyayenta mutane ne masu mutunci kuma nasamu 'yan unguwa duk sun bata shaida me kyau sbd haka na amince zaka iya auran Hajara" ba karamin dad'i naji ba bayan nayi dropping nasa a gda na taho gdana nasami Hajara na baka abinci bayan data gama na tura ka d'aki sannan na gayamata wannan great news d'adi taji sosai. On the other hand kuwa se pushing aure na ake da Iklima, mummy'nka nada hnkl sosai Fudail ba ruwanta fulani girl ce me kunya koda da muka fara had'uwa naji ta kwanta min a rai saidai nafison Hajara kanta. Akoi randa har gda takawo min visit nida kai tare da kawo mana abinci kala kala alokacin bana gda ina office kaikuma kana sch. Hajara tasamu a gda bayan sun gaisa ta tambayi Hajara ko ina gda, Hajara tace a'a nafita office amman ke waye dinsa ce? Iklima tace "wife to be na..." Bata k'are maganan ba Hajara ta tsinke ta da mari as how yadda masu aikina suka ban labari knan nan taci mata mutunci sosai tare da d'au alwashin seta kasheta duk sanda ta yarda ta aureni  haka cikin kuka Iklima takoma gda taje tasamu abba ta gaya masa dan har kai sanda Hajara ta fasa mata.
         Ina a office abba yamin waya tin daga yadda yake mgn na gano akoi matsala nan da nan na iso gda ganin goshin Iklima da d'auri yasa nayi gaggawan tambayar meya faru? Da murya cike da b'acin rai abba yace Hajara ce ta mata abinda kake gani, abinci takai maka da d'an ka Hajara taci mutuncinta haka shin ta kyauta knan? Tana nuna mana ne kawai zata iya illata ta fiye da haka ko ma takasheta bayan anyi muku aure, kuma sanin kanka ne Iklima marainiya ce baran yarda wani ya cutar min da ita ba, a gaskia Ahmad in har Hajara barata canza ba i have no option than to stop u frm marrying her, hakuri na riga bawa abba da Iklima kan zan mata mgn in shaa Allah zata gyara ahaka muka rabu. Isa na gda nasameta tana maka fifita kana bacci kasancewar ba mai a gen nepa kuma sun d'auke wuta tana gani na tabar abinda takeyi ta tareni sede taga yau ba walwala a tattare dani, "zauna" nace da ita nan ta zauna nace "ynxu Hajara abinda kkama iklima daxu kin kyauta knan? Harda ji mata rauni? Me hakan waito? Kinsan a dalilin abinda kkayi abba yace bare bari in aureki ba..." Kuka tafashe da tana had'a ni da Allah tana bani hkr kan barata sake ba sharrin shaitan ne har number'n iklima na bata ta kira ta tabata hkr. Daga nan ba'a sake jin kansu ba dama ita iklima bata da matsala. Kaikuwa koda dana gaya maka zan auri Hajara baka nuna ka damu ba hasali ma dad'i kaji sbd kamar yadda takesonka haka kaima kakesonta sede sam kuma bakkason iklima wanda nima bansan dalilin hakan ba!
       Kasan yadda time ke flying ana sauran 3 months bikinmu kasancewar duka had'a su zanyi a lokaci d'aya wani abokin abba daga unguwarsu Hajara ya tinkari abba ya irga masa irin banzayen halaye na Hajara dakuma abinda tayi na biyan 'yan unguwansu kud'i dan su bata sheda mekyau koda da abba ya kirani ban iya na masa karya ba gaskiar zancen na fad'i masa but nayi promising nasa kan in na aureta zata canza zata dena duk wani abnda takeyi mara kyau, yayi hkr daya barni in aureta is like jihad ne dan ko a muslince Allah zeyi rewarding d'ina abinda abba be tabayi ba yayi ranan ko saurarona yakiyi yayi making final decision nasa na fa'in baran auri Hajara ba naci kuka a daren ranan.
        Koda datazo aiki washegary ban gaya mata ba amman duk yadda nayi in boye mata yanayin da nike ciki na kasa sbd she reads me like a book. Haka ba yadda na iya sanda na gaya mata komi, kukanta tasha sosai amman sam zuciyarta bata kariya ba ta d'au alwashin tunda abba yak'i yarda da ita by the time take dauke da ciki na dole ya yarda amana aure.
      Dukda banji dad'in rabuwa na da Hajara ba amman ina iya kokarina dan cire santa a zuciyata, itama haka take nuna min kan ta hak'ura dani amman ina ashe trap take had'amun bansani ba.
          Rana d'aya ina kwance a d'aki na na wula duniyar tunani, Hajara tamin sallama kamar 'yar arziki kan inje inyi having lunch bayan na fito na zauna tayi serving d'ina abincin har zata tafi nace tazo ta zauna muci tare zama tayi amman tak'i ce ashe kam tasan me tasamin aciki. Ina ci ina yaba hali irin nata yadda ta d'au lamarin komi ta mika wa Allah, murmushi tamin sannan tace "ai matar mutum kabarinsa daddy'n Fudail in har matarka ce ni ko ta yaya xaka aureni, nide ynxu addu'a ta d'aya ne Allah baku zaman lfya yasa Iklima ta kula min da Fudail" ba karamin jin dad'in kalamun Hajara nake ba. Ban gama cin abincin ba nasoma jin jiri tin daga nan ban sake sanin komi ba. Tsintar kai na yi akan gado ba kaya a jikina salati kawai nahau yi wata wasika nagani bisa gefen gadon na bude nasoma karantawa kamar haka;....


  Posts are now available on the blog       beeenovels.mywapblog.com

No comments: