Saturday, 8 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


written by miemiebee
17
B'akin ibraheem na rawa yace "u..um..ummi?" Saalihah ta juya
dama ta juya hagu, tana pointing da kanta tace "ummi? Ni"
Ibraheem yace "karki raina min hankali mana bake nataba
dauka cikin mota na kka sace min 47k ba?" Me shagon yace
"eh? dubu arba'in da??" Ibraheem yace "eh wlh ita ce",
Saalihah tace "haba malam taya zakazo kana accusing dina of
stealing ur god damn 47k, na maka kalan barauniya ne? Nifa
ban tab'a ganin ka ba se yau" Haka abu kaman wasa jama'a
suka taru ciki harda alhj'n da Saalihah ta taba laka masa
sharrin kwanciya da ita, yace "tabbas wannan yarinyan zatayi
sata dan nima ta tab'a min sharri", nan fa akace sede ayi
police station da Saalihah. Tuni ta fashe musu da kuka ta
sauka har kasa "shikenan umma kin gama dani, wani sa'in
zama 'yan biyu bala'i ne tabbas baran karyata abinda
wadannan bayin Allah suke accusing d'ina of ba sbd inada
wata twin sister ummi itace, ita ta sace maka 47k naka,
takuma ma wannan alhj'n sharri, ummi ta kasance 'yar da
mahaifinmu ya tsine mata, sbda cikin data tab'a shigo masa
dashy gda tundaga lokacin ummi tashiga duniya, ana yawan
kawo complain ma abban mu ace nayi wani b'arna amman
sam ba ni bane believe me in baku yarda ba barin kirata ynxu
kuji", saura sukace "a'a ba sekin kirata ba" saura kuma sukace
"se an kira" number'n ameenatu datayi saving da twin sis ta
kira bugu d'aya biyu ameenatu ta d'aga Saalihah tace "hello
ummi?" Ameenatu najin ance mata ummi tace anniya twin sis
yane? Wani case din na kuma saki aciki? Se hkr fa' Saalihah
dake kuka sharkaf sharkaf tace "haba ummi shin yaushe xaki
shiryu kidena abinda kkeyi? Kisan fa zaki mutu", Ameenatu
tace "in wa'azi kika kira kimin ngd save it banso", Saalihah
tace "ina kk ynxu kina gari?" Ameenatu tace "shgya twin sis ai
baran gaya miki inda nake ba wayasani ko kina tare da
polisawa, shaa bana bauchi ynxu haka ina jos". Saalihah tace
"Allah shryeki ummi" nan ta katse wayar tace da mutanen
"kunji me tace, kuyi hkr on her behalf pls". Alhj yace "ba komai
Allah kare aukuwan na gaba" haka ibraheem ma ya fadi, ahaka
aka watse a wajen daidai nan ruky ta dawo, gdansu suka
karasa suka gama tattauanawa sannan Saalihah ta dawo hstl,
ameenatu takira tamata godia tare da mata alqawarin dubu
ishirin, ameenatu tace "aii karki damu aiki kam ynxu na fara,"
Saalihah tace "yawwa 'yar gari".
"Gurls yau da kashi na ya bushe ina ibraheem da wancan alhj
dana tab'a baku labarin d'anyen aikin dana tab'a musu?" Suka
amsa da "eh" atare nan ta kwashe labarin komi ta basu, bint
tace "shegge Saaly kamar yadda na gaya miki da gas nake
binki, aikinki na kyau!" Khadeeja dake sauraronsu tace "haba
Saalihah kisani in Allah ya rufa miki asiri yau bare miki ba next
yakamata kisani abinda kkeyi ba daidai bane". Saalihah tace
"oh ni Saaly ynxu gurls dan Allah nayi da malama?" Phaary
tace "I don't think so" nan suka qyal qyale da dariya.
Mu kwana mu tashy ba wuya Saalihah kam sede abinda ya
karu sata kam sekace wanda tayi degree, kud'i Saaly keda
sekace me aiki dan in akayi wasa ma tafi wani me aikin. In
tayi broke shine 1mil ne cikin bank acct nata.
Alhmdllh acikin ikon Allah sun samu sun gama 1st semester
nd duk ba me carry over cikinsu, se tattara kayakinsu suke
za'aje gda hutu. Bankwana sukayi sannan driver'n Saaly yazo
yabata ride har zuwa gda yau kam wata lace ce a jikinta ta
daura kai as usual bata sa ko gyale ba taciro dogon
attarchment nata ta tsakiyan daurin wanda ya sauko har
tsakiyar bayanta! Koda tashiga bata ga kowa a tsakar gdan ba
Sallama tayi sannan Sa'ad yafito "oyoyo adda Saaly!" Nan
sukayi hugging umma ma tafito, haka baaba ma sannu dazuwa
suka mata "shine baki gaya mana xakui hutu ashirya miki
d'akin ba yau" inji umma da fadi. Saalihah tace "ba komai
umma, Sa'ad tayani shiga da kayakin nan ciki" hakan kuwa
akayi tana shiga d'akin zarnin fitsarin Sa'ad ya bugeta "haba
Sa'ad ynxu fisabilillah baka bar fitsarin kwance ba? Taya zan
iya kwana cikin dakin nan? Umma! Umma!" "Na'am Saalihah"
nan ta iso dakin "ya wani abu ne?" Saalihah tace "haba umma
ynxu ko magani baraki siya ma Sa'ad dan yadena fitsarin
kwance ba? Wlh ni baran iya kwana a d'akin nan ba ni gaskia
yaje yasamu baaba su fara kwana zan gyara d'akin nan yazama
nawa ni kadai". Umma tace "haba Saalihah autan nawa kkeso
in barsa ya kwana da baaba bayan sarai kinsan bata kaunarsa,
gaskia a'a keda se hutu zaki na zuwa ai hkr xakiyi". Saalihah
tace "toh shknan tunda bara'a barmin d'akin ba dama akoi fili
a tacan d'akin baaba d'aki na zan d'aga a gun yadda bame
amfani da ita se ni". Umma ta zaro ido, "Saalihah gini zakiyi?
Da wani kud'in?" Saalihah dake murmushi tace "kede ki tsaya
kiga ikon Allah". La'asar nayi ta idar driver ya kawo mata abinci
bayan tagama ci tafice zuwa gdansu ameenatu inda ta bata
20k as promised sun d'an taba hira sannan tarako Saalihah.
Isanta gda taga abba na alwalan fita sallan maghrib gaishesa
tayi ya amsa da fara'arsa tace "abba akoi abinda zkayi da filin
dake can?" Tana nuni da yatsa abba yace "a'a saidai in
nasamu kud'i zanso in daga gini a gun". Saalihah tace "yawwa
abba zan iya d'aga gini agun?" Cikin rashin fahimta abba yace
"gini fa kkace Saalihah? Da wani kud'in?" Saalihah tayi
murmushi "abba na knan, ina aliyu na? Shi yace ze gina min
ciki da parlour amman in ka yarda dake mun taho tare dashy
daxu yaga filin, kuma yace wid time ze mana renovating gdan
ma gabadai!" Abba yace "ahhtoh ba matsala madallah kice ina
masa godia, naji haushin rashin had'uwan da bamui dashy ba,"
tace "zaku had'u someday dont worry kayi sauri kar kayi latti I
can hear an fara kiran sallah". Abba na ficewa baaba tafito
daga gun buyarta dagani tajiyo duk abinda suka ce tace "lalle
Saalihah bakijin tsoron Allah, ynxu abin naki harya kaiga karya
wa mahaifinki? Uhn uhn Saalihah karki bari duniya ta daukeki",
kallo Saalihah ta watsa mata "d'adina dake knan baaba kina
son abu kina kaiwa kasuwa, d'adi fa kkeji kan zanyi
transforming naki into a mansion anyways if this is ur way of
saying thank you, you're welcome. Ki shirya a dakinki zan
kwana yau tunda ke baki amalala cuz Sa'ad ya bata dakin can
da fitsarin kwance"

No comments: