Saturday, 29 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  4⃣1⃣



        Tana k'are maganan a zuci ta cigaba da abinda takeyi a wayarta ba tare da tace dashi komi ba. Gaye kam ba seya sakeyin sallaman ba nan ma bata ansa shi ba se akaro na uku ne ta d'ago idanunta batare da ta amsa sallamar ba. Ta k'are masa kallo head-to-toe taga wasu gajiyayyun slipper da suke kafafunsa ma tukun, ga wandon jeans dinma duk ya kod'e bayan kallon bakwai saura quarter data k'are masa ne ta bud'e baki tace, "bawan Allah fisabilillahi kayi ma kanka adalci ka dubi girman manzo, yadace bujaki talaka irinka yamin sallama in amsa? Be fair nd just plz tsakaninka da Allah". Gayen yayi shiru kamar bareyi mgn ba can seyayi murmushi dan batai k'arya ba shid'in talaka ne.
     Cikin tattausar murya yace, "mesa baraki amsa sallamata ba yake kyakkyawa?" Saaly datakai bango dan haushi tace, "aww tambaya na ma kake mesa baran amsa ba? Toh bari kaji amsoshi bama amsa ba, firstly ure not my taste, biyunsa bakada kud'i kuma bakayi kalan meyi ba koda nan da shekaru ne, na uku kuwa baka kwankwad'i boko ba, na hudu kyan ka bemin ba wannan hanci naka yayi tsayo dayawa ga 'yan kunnuwa dala dala kai! kawai kamin fillo fillo dayawa".
     Murmushi ya saki har senaga ya k'ara kyau ga dimple dan ko matashi ne me k'warjini kuma fa nada kyau daidai gwargwado iskancin Saaly ne kawai sede bara a had'a kyansa dana Fudail nata ba, amman kam shima masha Allah d'an dogo dashy kalan skin nasa golden haka. "Naji duk dalilanki amman ai bani na halacci kai na ba, naji ni talaka ne but kinga..." Yasa hannu ya ciro Jamb form wanda da alama ynxu ya siya "...ynxu zan cika inason nayi karatu nazama cikakken d'an boko. In nayi haka zaki yarda dani aiko kyakkywa? Bazawar dariya ta saki.

   "Ahhh lalle d'an saurayi kafa had'u ynxu d'imeme dakai seynxu xaka rubuta jamb? Har kana tunanin ka k'are degree kasamu aiki? Aiko da kyar sbd degree holders sunyi yawa ynxu ba lalle ne mutum me degree yasamu aiki me kyau ba sede in xakayi proceeding to masters nd ban tunanin zaka iya kai karatu har can meanwhile kana expecting ina in ta zama da sunan ni saurayi na yaje neman ilimi knan komeh? Shawara zan baka, da hakura kayi kaje jamb office ynxu in zasu iya ma refunding kud'inka tun wuri ka bude 'yar sana'a amman dekam boko ba naka bane" ta k'are maganar tare da watsa masa harara.

   Dukda kalamun data fad'a mai sun masa zafi but akoi some amount of truth aciki amman seyaji kawai ta k'ara masa k'arfin guiwan neman cigaba da karatun neh. Wata murmushin ya kuma saki "yake mekyau dan Allah kitaimaka min wlh duk wani abu naki burgeni yake, yau na fara ganinki amman senaji kamar na dad'e da saninki kodashike dama akace shi so haka yake, inhar nayi karatu xaki yarda ki soni toh wlh zanyi, ynxu semu cika min form dinnan kowani course kkeso inyi xanyi, wlh acikin d'an k'ank'anin lokaci naji na kamu da sanki, plz ki taimaka ko sunan kine ki sanar dani" Saaly tace "really now? Zan gaya maka suna na saboda kar inkaje wani gu ana zancen Saaly baby kace baka santa ba yazamo k'auyenci, Suna na knan Saaly baby".

   "Wow nice name nikuwa Suleiman suna na, so Saaly gayamun wani course kkeson nayi?". Murmushi tayi "Sule kake ko meh nafa gaya maka karka ma fara b'ata lokacinka akaina dan ko da kake ganina ynxu kayakin dake jikina am very sure koda za'a tara duka arzikin da zuri'anka suka mallaka had'e da naka baraku iya siyan koda gashin dake kaina ba to talk more of motar da nike hawa. Ni ba class inka bace, kaje ka nemi talaka 'yar uwarka kuyi soyayya. In baka sani ba kasani yau a rayuwata na tsani talaka, bana k'aunar kasancewa da talaka. Kaga mijin da nike da niyan aure hatta mota ya siya min tell me this sule, xaka iya sayamun mota? Am sure no sbd ko 'yar waya ma baraka iya siyamun ba then mesa zan b'ata lokaci na akan bujaki talaka kaman ka? Abeg tun wuri ka tattara gajiyayyun slipper naka kabarmin gaban gda".

    Suleiman daya jima beji erin wanga munanan kalamu ba yaji har kolla nasan ciko masa a ido yayi k'arfin hali yace "ba'a under estimating d'an adam Saaly, kisani you may drive your boss today nd your boss may drive you tomorrow, haka duniya take, bekamata ki k'yank'yami talaka ba a dalilin meh? Kuma komin kud'i da dukiyr da mace keda bata fi k'arfin na miji ba. Na yarda ni talaka ne amman wayasan future'n da Allah ya tanada min nan gaba? Dan Allah kiyi hkr koda number'n wayanki ne kibani".

     Saaly tace "yau Allah ya hadani da chewing gum dayafi Yunusa maita waishi Sule". Humm kawo wayarkan insa maka number'n" ta fad'i hannu yasa a aljihu yaciro wata gionee wacce screen nata tasha cracks kambu sekace an daka sakwara akai. Dariya taje kamar ba gobe.
         Karka gayamun wannan itace wayar ka? Shi sam cin mutuncin da take masa be damesa yace "eh itace" tana dariya tana mganar "Allah sarki sule kana ganin rayuwa fa! Sosai sosai..." Ungo ta mik'a masa wayar "ai in number na tashiga wayr nan nawa ya k'are dan nima cracking zan soma, by the way kace kanason in zab'a maka course da zaka karanta ko?" "Eh ya fad'i" cikin jin dad'i hannu ta mik'a "bani form d'in da pen" nan yasa hannu a aljihu ya ciro pen ya bata tare da form d'in daidai tsakiyar form d'in daga sama daidai kan iadanunsa tasa hannu ta yage har k'asa takuma yagawa haka tata kacan canawa a gaban idon Suleiman daya bud'e baki wangalau cike da mamaki yana kallon d'anyen aikin da Saaly ke masa haka tayi kuci kuci da form din sannan ta hura masa a jiki da fuska.



beeenovels.mywapblog.com

No comments: