Saturday, 29 April 2017
KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
written by miemiebee👄
4⃣0⃣
Ta juya ta hango Fudail a jikin wata shago da bottled water a hannunsa se wanke hannunsa yake, wajen ta nufa itama tama me shagon sallama tare suka amsa dashi dawani abokinsa tace, "tambaya nake dan Allah, ko kunsan wata Saalihah Ibrahim anan?" Me shago da d'an uwansa suka kalli juna sannan a tare kamar robot sukace, "kai gaskia a'a hjy, bani tunanin akoi Saalihah anan layin". Ni miemie nace, "shege money!"
Fudail dake tsiyaye ragowar ruwan faron a k'asa ya juya yace, "can u pls stop the act? Just admit ur guilt kinzo kina wani koran kunya da hauka mtsw wlh xan tafi ynxu ki tsaya anan kiga in ban tafi na barki ba" yana kaiwa nan ya fice direct zuwa motarsa. Ikleema ta dawo da kallonta kan samarukan "dan Allah ku fad'a min gaskia ba wancan bane gdansu?" Tana nuni da tsohin gdan su Saaly. Me shagon yace "kai! Gaskia a'a can ba gdansu, gdansu... Tuna min mana maza" saurayin yace "abdullahi ba" me shagon yace, "yawwa abdullahi ai kuma kinga ni na juma anan ina neman kusan shekaru biyar bansan wata Saalihah a layin nan ba..." Ta bud'e baki zatai mgn taji Fudail ya kunna mota ba shiri ta kwashi gudu! Allah da batai gudun ba da gogan namu yatafi ya barta.
Koda tashiga bece mata komi a motar ba ita keta suratan duniyarta se rantsuwa take masa kuma har ynxu ita tana kan bakarta seta gano Saaly***
Motarsu na barin unguwar Saaly data lab'e daga wani lungu acikin motarta ta ciro dark sunglasses (gilashi) data toshe dasu tana ganin drama between Fudail da so called mummy'nsa ta kwashe da dariya harda hawaye "hehehehhe in bakasan Saaly baby ba ace kayi kauyenci kasanta kuma ace kayi gwaninta! Lol ai dama kamar nasan haka ze faru nafasa renovating gdan muka koma old GRA kawai". sannan ta soma chewing gum dake bakinta, a hankli take maganar. Tace, "Allah sarki baiwar Allah akace in baka iya kama b'arwo ba se b'arawo ya kama ka, ke ynxu wani d'idd'irin ne yasaki? Neman gindin zama gun Fudail d'ina to kisan kina b'ata lokacinki ne no one messes with Saaly baby!"
Tana kaiwa nan ta kunna motarta tayi driving zuwa gaban shop da Iklima tayi tambaya tabasa dubu biyar su raba da abokinsa sannan ta zarce gdan su malam taba sa dubu biyar matarsa ma haka 'ya'yansu kuma dubu d'ai d'ai suka mata gdy ita ma tamusu sannan ta komo motarta se sabon gdansu! Bayan tayi parking motarta a wajen da aka tanadar ta shige ciki.
Fudail kuwa ko da dasuka isa gda bece ma Ikleema komi ba yajirata tafito daga motar sannan yabi bayanta bayan ta kaiga parlour'n daddy yace, "tsaya can" cak ta tsaya ya k'olla ma daddy dake d'aki kira nan daddy yafito, "my warrior ya haka? Meya faru?" Fudail dake ta watsa ma Ikleema harara yace "gata can daddy, talk to her haka kawai ina zaman xamana dan ta tozartani ta daukeni mukaje zango wai acan su Saalihah suke da zama takaini wani rakwab'abb'en gdan da inba a NEWS ba ban tab'a gani ba wai gdansu Saaly ne muka shiga mutumin gdan da matarsa suka cimin mutunci..." dubi nan yana nuni da kayansa da yage... "har kaya na sanda ya yage". Daddy daya gama sauraron Fudail ya dawo da kallonsa kan Ikleema tare da fad'in "wai haka Ikleema? Mesa zaki kaisa gdan wasu da sunan gdansu Saalihah? Kinsan kuwa neman aurenta yake..." Ikleema ta bud'e baki zatayi mgn Fudail ya katse ta "ni kawai daddy ka mata mgn ta dena shiga harka na tun ba yau ba takeson had'ani dawata 'yar uwarta wai ita Asma'u..." Daddy ya katse sa "ur tongue Fudail, she's your mother. Naji xan mata mgn". Ba tareda cewa komi ba ya zarce site nasa. Ikleema kuwa daddy yamata hannu data zo suka shige d'akinsa danyin mgn***
Saaly kuwa na kwance kan tapkareren gadonta se sana'arta na waya da samari takeyi AC'n d'akin yayi sanyi sosai se sha'aninta take tama manta tanada carry over har biyu a sch. Cuz she's got no worries ynxu, aure tsakaninta da Fudail is considered done!
Washegary tun 10:30AM ta tashy tayi wanka da snacks dake fridge a d'akinta ta karya ta zauna gaban dressing mirror ta ja makeup kit nata wanda ke ajiye a gefen dressing mirror d'in danagani sanda na razana dan girmansa na tab'e baki sekace makeup artist wanga jakan makeup! Gashi kuwa na Elizabeth Arden ne, babban designer ne yafi mac tsada. Ta kwashe awa biyu tana abu d'aya wai shi kwalya. Dadau! tafito d'ankaren nan gawani foundation datake shafawa take take dawowa baturiya. Ta k'are ta bude one side of her wardrobe inda take ajiye brazillian hair nata dan ba d'aya ba biyu take dasu ba dayawa kawai. Ta d'aga wannan ta ajiye, ta d'aga wancan ta ajiye can taciro wani brownish black tasa yako bala'in mata kyau. Ni kaina miemie sanda na sara mata! Dama wani tsinannen fitted gown daya cire cleavage (k'irjinta) a waje ne a jikinta.
Sannan ta feffeshe da turarukan da sunfi goma a gaban mirror d'in. Nan tasaci hanya tafita dan battason abba yaganta da wannan shiri. Har tafito waje ba wanda ya ganta kasancewar ta back door tabi se taci karo da baaba. Baki wangalau baaba ta bud'e har da zatace, "Saaly wannan wace erin shiri ne?" Seta tuna tana mganan da be gami Saalihah ba ynxu se a dena siyan abincin turawa da ita. Kup! Ta rufe bakinta Saaly ce tayi breaking silence d'in tare da fad'in, "daga ina baaba?" Baaba tace "nad'an zagaya ne gskia wannan gda akoi kyau, kaaiiii! Amman kinyi kyau gashin nan kamar ki bani". Saaly dake blushing tace "kaii baaba ngd ungo dubu biyu asai goro". Hannu na rawa baaba ta amsa "amman ngd 'yata a dawo lfy". Har saaly takama tafiya seta dawo tace "ehem in abba yace ina naje kice masa gdan k'awata". Baaba tace, "toh angama! Saalihah"
Sede data fita bata ga motan Abdul Hamid dake jiranta ba tsuka taja tanemi waje ta zauna a bakin k'ofar. Ko cikekken minti 5 da zama batai ba wani wai shi gaye dagani a unguwar yake, yazo ya wuce ta gaban Saaly dake ta danne danne da wayarta kome ya dawo dashy? Nakega had'ewa da cinyewar da Saaly ta yi ne ya dawo dashy. Nufowa yayi gabanta nanne ta d'ago kai sanda ya sako baki dan kyau irin na Saaly sannan cikin murya me dadi ga me sauraro yace "Assalamu Alaikum yake me kyau".
Saaly bata san sanda wata bazawar dariya ya kubuce mata ba, a zuci tace, "daman ynxu ana irin wannan sallaman ne in anzo zance gun budurwa lol lalle kuwa wannan yaro ya rainani!"
beeenovels.mywapblog.com
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment