Saturday, 29 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  3⃣3⃣



         Tana ajiye wayar su bint suka dawo daga lecture room bayan sun gama gaisuwa da hugging malama khadeeja ta shigo nan Saaly ta miqa mata hannu suka gaisa se making fun of her suke. Nan ta zazzage masu duk wani abinda yafaru a tafiyanta duk suka mata murnan kasancewa da Fudail nata, khadeeja dake sauraronsu tace "ashe de like mother like daughter ne ba laifinki bane Saalihah amman da zaki taimaki kanki tun ynxu kar kixo ki k'are kamar ummanki".
      Bayan saurayin phaary yazo ya daukesu fita cin abinci da bint, Saaly nata shiri an sha brazillian hair dinnan samansa bak'i kasa kuma ja, ga makeup dinnan tagama k'warewa yanzu se feffeshe designer turarukan ta take khadeeja dake kallonta tun daxu kamar TV tayi gyaran murya "Saalihah naji duk abinda kka gaya masu bint daxu kuma nima namiki murnan kasancewa da Fudail naki amman don't u think is about time kema ki gyara al'amuranki kar ki kare kamar ummanki? Ki dena biye wasu bint wlh kaiki xasuyi su baroki", kisani a ynxu Fudail na nunawa yana sonki amman duk sanda yagano d real you dakuma irin mutanen da kke al'amura dasu wlh ze canza..." Dakatar da ita Saaly tayi tare da d'aga mata hannu "wait! Wait! Malama kinsan in akoi abinda bai shiga na shine wa'azi sbd haka kima bar b'ata lokacin ki incase u dont know kisani yau, ni Saaly a yau zan fara rocking rayuwata tunda ga ummata da ta tab'a yin zina ma Allah ya shiryar da ita bale ni, nida ban tab'a ba, haka kurum ki hanani sakat mtsw pls I beg of you khadeeja kidena shiga min harka" tana kaiwa nan ta d'au wayoyinta "insu bint sun dawo kice musu mun fita da Fudail"***
          Se can bayan maghrib Fudail ya rakota har bakin kofar hstl tare da mata shopping kamar hauka wanda ita kanta batasan me zatayi dasu ba, jibgesu tayi bisa kan gadonta dalilin wayarta dataji yana ringing dubawanda tayi taga T boi zuciyarta ce ta hau bugu gashi tana da inda zata right now.
       Fuska taci ta d'aga "hello baby, ya akayi?" On the other side yace "lfya kullum inta trying wayarki bata shiga lfya daiko?"   "Wlh a'a baby kasan har yau umma ba lfya ynxu haka wai sede a kaita Egypt a mata aiki gashi kud'in wajena bare isa ba sesa kajini shiru 2 days kai na ne yayi zafi". T boy daya fusata yace "haba Saaly shine baraki kirani ki gaya munba? Ynxu nawa kike nema?" Jan bakin bakinta ta soma tand'ewa sannan tace "inada N200k a wajena N300k nake nema" T boy yace "ahh to ba matsala karki damu ynxu zan miki sendn yaushe ne tafiyar kun?" Tace "thanks ko baby zan gayawa umma, tafiyan ko gata ne haka". Ahaka tayi hanging tafad'a kan gadon phaary da suka zura mata ido daga bisani bint tace "Allah babegurl you too much ke! Ai irinku ake nema kuna gara maza wlh N300k abinki". Hira suka soma kafin Saaly ta soma shiri nan alhj na mata ya kirata itama ynxu kam harda guntun kukanta, tamasa bayani sak yadda tama T boy sede shikam tace masa ko sisi ma batada N700k ya mata sendn shgya Saaly ta tashy da 1mil acikin 'yan mintoci.
      Bayan sun gama wayan taci wanka akasha matsatsun english wears ga brazillian hair dinnan dogo har k'asan kirjinta tamasu ba-bye sannan ta ja motarta se inda suka saba jiran alhazan su nan ma tasake feffeshewa da turare ta gyara makeup nata sannan sukaje sahun gaba ita da ruky wasu manya manyan rides ne guda biyu suka yanko corner'n d'aya range rover fara tas d'aya kuma wata prado daidai gaban d'unbin emmatan suka tsaya sukayi winning glass bayan da suka k'are ma emmatan kallo me prado ya kira ruky sid'ak ta wuce suka fice me range rover kuwa Saaly ce tamasa dan ko kallon motarsa kamar yadda sauran matan suke battayi hasali ma wayarta  take ta danne danne a ciki honk yamata sam tak'i d'agowa duda tasan da ita yake haka ba yadda ya iya yafito da angansa an ga magidanci saidai ba babba bane bare gaza shekaru 42-44 ba isowa yayi gabanta bayan sun daidaita ta bisa suka fice sauran karuwan wajen se tsine ma Saalihah suke a dalilin meh? Su da gasu farare kullum suna kwante se ita baqa, baqan ma me bleaching ni miemie danake jinsu nace ai mace ba fari bane hadewarta, wasu Allah nabasu fari jini ne gun maxa!.
            A daidai gaban hysaan meet nd beverages ya tsaya dan siyo musu kaji su d'an motsa baki Saaly na ganin ya shige ciki ta soma bud'e bud'e cikin motar ko zata samu credit card ko kuwa kud'i haka tata dube dubenta bataga komi ba tsuka taja "mstww ka d'au kana da wayo ko Aseem? (Sunan me motar knan) lalle kuwa ure playing with fire sekayi regretting kin ajiye kud'in da kayi a mota yau, Saaly zata maka aiki".
            Tsallakowa tayi xuwa driver's seat daman yabar motar akunne dan AC juya key tayi ta taka accelerator phewww!! ta gudu da motan  bata tsaya ko ina ba se wani gun kanikanci daman me gun mutuminta ne motar tabasa nan danan aka cire plate mumber aka ma motar penti yakoma black yadda koda Aseem yaga motar akan hanya bare gane nasa bane. A wajen tabar mai motar ko zuwa jibi in painting ya bushe seta siyar. Shiko Aseem yafito da ledoji biyu k'atin k'atin a hannu yanemi motarsa Range rover ya rasa motar da kap bauchi basu fi a irga ba, yau akeyinta fad'i kawai yayi a k'asa sumemme. Motarta ta biye ta d'au ta taho hostel.
        Washegary da safe bata je ko lectures ba bayan tayi wanka ta shirya ta fice zuwa wajen kanikancin, danladi na ganin hjyarsa yabar duk abinda yake ya nufo wajenta "ina kwana hjy?" Space dake fuskarta ta ciro "lfya qlou d'anladi ina motar ne?"  "Gata can acan hjy" ya fad'i. "Yawwa nikam in za'a siyar da wannan mota nd nawa za'a siyeta?" D'anladi yace "gaskia wannan mota babbar motace hjy range rover land rover 2016 ce nima yau na fara ganinta a reality, dakyar kisamu me siya a bauchi kinsan bauchi ba wajen kasuwanci bane gomma ko kano ko abuja", Saaly dake sauraronsa tana nodding head tace "kace nada tsada, kamar nawa kake gani knan?" D'anladi yayi gyran murya sannan yace "kinga inhar sabuwa pil acikin leather ne to ana sayarwa $84950 a naira kuwa N21,237,500 (miliyan ishirin da d'aya da naira dubu dari biyu da talatin da bakwai da d'ari biyar). Tuntub'e me rai da lfya Saaly taci dan ji take kamar a mafarki. "Miliyan ishrin da d'aya fa kace d'an ladi?" Tana me kepkepta ido



    beeenovels.mywapblog.com
     Pls zaku d'an jini shiru kwana biyu due to some issues in shaa Allah the moment evrythng is back to normal zan cigaba, love you all...

No comments: