Thursday, 13 April 2017
KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
written by miemiebee👄
2⃣5⃣
"Kamar yadda kasani asalinmu fulanin yola ne ko?" Fudail ya giada masa kai, daddy ya cigaba; "kamar yadda Allah ya mallakamin kai kad'ai haka nima nake a gun kakaninnka, kakanka na bala'in so na komi nakeso shi yakemin tun ina d'an yaro ban tab'a neman abu na rasa bayan dana k'are sec sch yace sam sede ya kaini abroad inyi karatu dan kakanka yana da kud'i sosai shanayensa sun kusan d'ari, danginsa kam sukace sam basu yarda ba basu so, ai ba'asan fulani da yawuce yawuce har kasar waje ba, kunnen kashi ya musu ya turani London inda nayi degree na harda masters acan na had'u da mummy'nka Allah jikanta ya gafarta mata", "ameen" fudail yace. "Tin randa na fara kallonta naji ina sonta, dana mata mgn kuwa batayi shunning d'ina ba daga nan muka zamo frnds time d'in nakusa gama masters itakuma takusan gama degree da wasa wasa soyayya me karfi yashiga zuk'a tanmu bayan da akayi hutu ta dawo bauchi dan 'yar nan ce, nikuma nakoma yola. Iyayen mu muka samu duk muka gaya musu abinda ke zuk'atanmu take iyayenta suka yarda mata kasancewar itace autarsu duk yayunta sunyi aure nikuwa kakanka ya yarda min amman banda umma (kakar fudail ta mace) da danginta sam suka ce bara'a auro musu bare ba dole se dangin fulani in bahaka ba afasa auren as how kakanka yasaba shunning nasu haka ma yayi wannan karan yayi pushing thru da maganan auren ahaka har akasa mana date sede umma kam suratan yau daban na gobe daban.
Koda da abba yace a ina mukeson zama nace yola haka na gina mana wata hadaddiyar mansion in aka shigo unguwar ma dashy ake kwatance dan kyawunsa. Biki na 'yan gayu aka mana da marigayiya cikin so da kaunar juna sede tunda aka mana aure umma ta tare damu a cewarta zata na kula damu ne sede abin ba haka yake ba, takura wa margayiya take, ko numfashi mummy'nka tayi setace ba haka akeyi ba nikuwa inason mummy'nka but I can't say no to my own mother, kullum mummy'nka cikin complaining umma takeyi dan har hakurinta ya k'are nikuma nata bata hkr abin beyi getting worst ba se time da take da cikinka, umma kullum cikin d'ura mata jika jike take wanda bawai sunada relevance bane, kafin margayiya ta haifo ka duk ta rame ta lalace nima abin ya isheni dan haka nasamu umma na mata mgn cikin dabara da girmamawa kan taje gda ta huta for the meantime in margayiya ta haihu seta dawo sam tak'i wai so nake na korata to ba inda zataje.
Lokacin da aka haifeka ma ban kasar kwata kwata time d'in na tafi morocco labari masu aikin gdana suka ban cewar umma tak'i kai margayiya asibiti a gda ta haihu cikin azaba da wahala raina ya bala'in b'aci dan haka nayi confronting umma a ranan ta riga ja wa margayiya Allah ya isa a cewarta asirce ni margayiya tayi in bahaka ba baran tab'a iya gayamata harsh words dana fad'i mata ba. Kanada shekara uku a duniya nasaka a makaranta, duk da sanin cewa mummy'nka bata jin dad'in zama a gdan amman ya na iya da umma ta? Dole se hkr, abu fa se worst yake getting rana d'aya na dawo daga tafiya na shiga d'akin mummy'nka abinda ngani ne yamun razana ni..." Sekuma yayi shiru. Fudail yace "tell me father ai ba karamin yaro bane ni.." katon gardi naga kwance a gefenta, Fudail sunanta dana kira ne ya ta da ita daga baccin datake tana juywa taga wannan mutumi dake kwance a gefenta ihu ta saka nan umma ta fito ya haka? Innalillahi kwarto ynzu Ameena maza kka fara kawowa kina kwanciya dasu dan mijinki yayi tafya tuni idanun mummy'nka suka cike da kolla tafara rantsuwa tana kuka kan wlh ita batasan da shigowar wannan mutumi ba haka umma tasata a gaba ta mata tsinannen duka niko ban hanata ba sbd abinda tamin taya zata kawo min namiji gda su kwanta a d'aki na kan gado na for that matter take na bata saki uku tare da mata Allah ya isa kan abinda tamin itade batayi admitting guilt d'inba umma tace sam se anje kotu a jefeta ni na roki umma data rufa mata asiri tayi hkr, washegary kap nasa aka tattara mata kayakinta tabar gdan baran tab'a mantawa da erin kukan dakayi ba lokacin.
Bayan shekaru biyu da rabuwar mu da margayiya wani labari mara dad'i ya iskemu nacewar ta rasu due to plane crash da akayi frm Nigeria to Ghana, nayi kuka sosai dan koda bamu tare da ita ina sonta, ina mutuwar san mummy'nka fudail a lokacin kuwa umma na gadon mutuwarta itama dan wani rashin lfyr data ta fama dashi nakusan wata 6 anan na gaya mata kan Ameena ta rasu kuka take sosai wanda ni kaina yaban mamaki to kukan me kuma zatayi? Dama tana sonta ne? Ai in wanda ka tsana ya rasu sede kayi rejoicing nan umma tagaya min wasu maganganun da har yau in na tuna dasu se inji zuciyata tana min k'ona ina regretting sakin mummy'nka danayi, wai ashe ita ta kawo na mijin da muka gani a d'aki tare da mummy'nka dagangan dan ta cimma burin seta fidda ita daga gdan, k'azafi ta mata fudail, your mum was innocent mummy'nka bata tab'a cin amanata ba kuka nayi sosai har se da aka rikeni a asibiti dan ko abinci nabar ci, bayan na samu sauki akacemun umma ta ta rasu amman tace dan Allah na yafe mata, duda abinda tamin uwa uwace nan take na yafe mata.
Kaikuwa cikin shekaru biyu dakayi ba uwa duk senaji tausayinka ya kamani dan kullum cikin tambaya na kake daddy yaushe mummy zata dawo? Tunda ynxu umma ta rasu bame kula min dakai nasa anemo min nanny'n da zata na kula dakai ina dawowa daga office kuma seta tafi ni na kula dakai. Wannan nanny ba kowa bace illa HAJARA! (Umman Saalihah) a gskia baran boye maka ba son, Hajara mutumiyar banza ce, irinsu ne matan da tsinuwan Allah ke tabbata akansu in bawai ta shiryu bane ynxu, abinda yasa ban koreta daga aikin ba shine dan yadda take sonka take kuma kula da kai, duk shiganta na batsa ne akoi sanda wani abokina yatab'a zuwa gdan ya ganta take yace mun in sallameta ya irga min duk erin banzayen halayenta na bin maza, sata da sauransu. Nikuma tsoran koranta nake kar na rasa waze kula min dakai, kasan mata da sharri bansan ya akayi ba kawai naji inason Hajara kodan yadda take exposing jikinta min ne bansani ba nide kawai naji ina son in aureta koba komi in na aureta zata dena yin abubuwan datakeyi zata shiryu kuma tadena bin maza, ga kuma yadda take sonka tamkar ita ta haife ka. Soyayya me karfi ce ta ratsa zukatanmu dukda ban cika san abinda take min in muna tare ba sbd abu kadan seta kama hannu na abu kad'an ta shafa ni nide nasan inasonta nd am willing to take risks haka ta takura min muyi muyi muyi aure nima nagaji da zama lonely rananda na shirya zuwa gayawa kakanka a ranan ya kirani shima kan akoi wata maganar dayakeson muyi. Da la'asar ranan alhamis baran tab'a manta wannan rana ba kakanka yace min yamin mata wata 'yar uwata mummyn'ka knnan Iklima, wanda yakeson in aura tunda tin rasuwar margayiya yau kusan shekaru hud'u ban sake mgnan aure ba yagaji da gani na ahaka nikuma I can't say no to my dad duk yadda nakeson Hajara haka na soma yayyafa wa zuciyata ruwan sanyi dan bin umarnin mahaifina!
Washegary Hajara ta taho aiki as usual da safe dan shirya ka sch nan na isketa da maganan sam tace min ita wlh barata yarda ba seta aureni ai ni ba yaro bane da zan bar mahaifina yana gayamun abinda zanyi, na miji dani ace se mahaifina ne ze gaya min abnda zanyi? Gaskia na bada ita meh meh meh haka ta ta cika ni da suratan banza kasan mata a koda yaushe sun san yadda xasu bi da mutum daga k'arshe tayi convincing dina cemata nayi kar ta damu.
Bayan na taso daga office nabiya gda nasamu abba cikin ladabi da biyayya nake masa maganar; Abba bawai zan sab'a maka bane baran boye maka ba akoi wata Hajara 'yar gdan malam gidad'o da muka jima muna san juna da ita kasancewar itake kula min da Fudail ma ynxu a gaskia ina sonta kuma inasan in aureta shin abba in zaka amince bayan ka aura min Iklima daga baya se in auro Hajara that is in ka yarda. Abba na nasona sosai nan ya amince min amman da sharad'i kan zeje yayi bincike kan ta da iyayenta nan take zufa suka soma k'eto min cuz nasan 4sure ana gayawa abba halin Hajara bare amince ba toh ya zanyi? Gda na koma na gaya mata yadda mukayi da abba takuma amince da hakan saida nace mata abba yace zeje yayi bincike a kanki kuma kinsan kap 'yan unguwanku bara su baki shaida me kyau ba, leave that to me ta fad'i kasancewar tanada kud'i dan samarukanta da alhazan ta suna bata tabi gda by gda a unguwansu tana rabawa mutanen kud'i kan in anzo tambayan halinta duk su bata shaida me kyau, as everythng works with money duk suka amince da bata shaida me kyau...
Posts are now available on the blog beeenovels.mywapblog.com
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment