Saturday, 8 April 2017
KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
written by miemie👄
1⃣0⃣
Jiranta su bint sukayi tagama cin abincin sannan suka dawo hostel rage kayakin jikinsu sukayi, suka zauna kan gadon Saalihah. Ta tambayesu; "nikam waye wannan Fudail da duk kuka kidime daga ganinsa?" Phaary tace "ynxu bakisan Fudail ba? Ai nakega ko malamar dakinmu zata san Fudail. Mahiafinsa minister ne a wshington yayi karatu inda ya karanta petrochemical engineering",..bint tayi interrupting "course din manya kkeji!" Phaary tace "gaya mata de," Saalihah tace "toh dan minister fa kkace? Toh meyakeyi anan bayan yagama karatunsa a washington as said." Bint tace "masters yakeyi anan ai kinsan ATBU suna kokari ta engineering sosai sesa ya zabi nan din," Saalihah tace "oh ayya," phaary ta miko mata wayarta "ungo kalli pictures nasa kiga, daga instagram nayi screenshot swiping one by one Saalihah takeyi kyau da swags na Fudail yana tafiya mata da imani "mutum sekace black american omg!" Bint tace "ahtoh Fudail din kkeji!" Saalihah tace a zuci "lalle kuwa i'll do whatever it takes kazamo nawa Fudail!"
Can da yamma ta kira gda suka gaggaisa dasu umma ciki harda baaba. Da daren ranan around 9:30PM su phaary suka gama shiri cikin wata shgyar lace data sha dinki gawani makeup da suka sha sunyi kyau sosai, bint tace "Saaly ya haka? Bazaki bane?" Saalihah tace "ai baku gayamun inda zaku ba," phaary tace "kinada case wlh" ta matso kusa da ita "sekinsa malamar can tafara mana wa'azi ne?" tana mgn nanne tana kallon khadeeja datayi jugum tana kallonsu... "Ofcourse gun mutanen mu zamu mana oya kishirya halan kema kiyi new catch a gun." Ba gardama bale musu Saalihah ta zabura ta dau daya daga cikin sabin dinkunanta tasa suka cancare mata kwalya sannan suka fita daidai gabar wata makekiyar gda suka tsaya bint ta sallami me napep sannan suka shiga ciki disco light ne kawai suke haske wajen ga karar music har heart beat na mutum samary da 'yan mata ne ko ta ina suna aikata haramun! Kujera suka nema suka zauna basu jima da zuwa ba wasu samaruka guda hudu suka nufo inda suke wanda ga dukkan alamu sunsan su phaary ne dan wani shafa su dasuke, itade Saalihah ta tsaya tana kallon ikon Allah, can daya daga cikin guys din yace "wow wace fresh babe din can?" Yana nuni da Saalihah datake kallon wani direction. Bint tace "frnd inmu ce Saaly sunanta." Karku manta duk da karfi suke mgnan kasancewar disco dayake tashy acikin gdan.
Guy din yace "wow erinsu nakeso" nan ya bar gunsu bint yaje ya zauna kusa da Saalihah datayi kamar bata gansa ba hannunta kawai taji ya riqe yana ma wata erin karuwan kallo bata san sanda zuciyarta tafara bugu ba "'yan mata kinyi kyau!" Daurin kan ta take tabawa tace "thanks," yace am "T boy" itakuma tace "am Saaly" yace "nice name bari a dan kawo mana wine mudan sha ko?" Saalihah tace "no need i dont feel like drinking," yace "ohh so u must be new here"...haka a hankali suka soma hira can yace bariya dan shiga bathroom, yana tashy Saalihah ta jawo wallet nasa budewa tayi taga dubu daddaya ne sabi pil aciki zaro ido tayi tana lashe lips nata da harshe, wallet din tsundum tasa cikin jakarta tana ganin T boy na dawowa ta mike tafara "ke kidawo?" T boy ya kariso inda take yana "lfya?" Tace "kabar wallet naka anan wani baki?" T boy ya gyada kai, Saalihah tace "shit! Wlh ynxu wata tazo ta dauka wai nata ne inata kiranta kuma taki dawowa tafice da gudu," da gudu T boy ya leqa waje amman ina ba sign na kowa haka yadawo Saalihah tace "ya kasamu ka kamata?" Yace "a'a manta kawai daman befi 70-80k bane a ciki," Saalihah ta hade miyau tare da fadin "baho kawai, ashede nasamu kudi" azuci. Dawowa suka yi suka cigaba da hirarsu har se can 11:30PM sannan phaary tace zasu tafi guys din suka basu lift acikin wata range rover'su har gaban ATBU suka kaisu sannan T boy ya miko ma Saalihah bundle din N500 "ga wannan ko baby, kidan sha ruwa dashy nd this is my card give me a call..." Wani fari fari da ido Saalihah keyi take ta amsa tana masa wata erin kallo me ratsa jiki "thank you seka jini" sannan suka fice su kuma suka shigo hostel kofar dakinsu suka gwada budewa amman a rufe, phaary tace da bint "ba akoi key a gunki ba? Bude mana man," nan ta duba jakarta amman bata gani ba tace "gosh! Ai na manta ban dauko ba daxu." Phaary tace "kai amman ko! Ai semu san nayi ynxu dan frm all seeing wannan malamar tayi bacci ynxu" haka sukata knocking da kyar khadeeja ta jiyosu tazo ta bude musu tana tambayar Saalihah "daga ina haka?" Kafin Saalihah tayi mgn bint tace "daga club wani abu ne?" Khadeeja tace "ba komai sannunku" tanufa kan gadonta ta kwanta wuta su Saalihah suka kunna khadeeja tace "ynxu fa to 12 taya zaku kunna mana wuta bayan kowa na bacci?" Saalihah tace "sallah zamui khadeeja," nanne bint da phaary suka tuna basuyi sallah bama nan da nan sukayi dungura tashy suka idar. Har ynxu khadeeja na jiran su kashe wutan amman wani sabon party ma suke son bude wa a dakin, phaary ta kunna wata waka a wayarta tare da kure volume din tana bi can bint ma tasa baki haka khadeeja baiwar Allah takasa bacci a ranan. Kudaden da samarukansu suka basu kowa tafara counting nata Saalihah ta tashy da 120k, sauran kuma100k.
Washegary bayan sun fito daga lectures 12:45PM suka sake gyara makeup nasu sannan suka fice jifatu za'ayi shopping. Su Saalihah sabon shiga yau tafara zuwa shopping mall a rayuwarta. Daman ta yi saving number'n T boy a wayarta dan haka ta kirasa, kafin ta fadi sunanta ma yagane itance bayan sun gaisa T boy yace "Saaly ai na dau baraki kirani bane ko kin raina 50k din tho nima be kamata inba wa babbar yarinya kamarki 50k ba sede 100k yayi sama ko?" Budan bakin Saalihah "aikam kamar kasani kaine na mijin daya fara bani 50k but kar ka damu nan gaba se ka gyara," T boy yace "toh ngd sosai da kka min uzuri, zamu hadu yau ma?" Saalihah tace "i'll think about it..." hira kadan suka dan taba Saalihah tace "am a little bit busy ynxu zan kira ka anjima" yace "tam" sannan tayi hanging tana juyawa suka hada ido hudu da Fudail dayake mata wannan shu'umar murmushinsa me narkar da zuciya da alama yaji duk wayar da tayi. Waigawa tayi taga su bint suna ta shopping abinsu, daya daga cikin trollies din Fudail yaja tare da fadin "be my guest" yana me mika mata hannu, hannun ta tasa akan nasa ya rike sannan suka fara shopping din tare ko ince ya fara mata shopping dan duk abinda yagani kwasa yakeyi kamar baho. Dam ya cika trolley din yana tambayarta "Saaly a kara miki ne?" Saaly tace "duba da kyau shopping din ze siye ni?" Fudail ya duba ya duba da kyau sannan yace "I don't think so, lets fill another trolley!"
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment