Thursday, 13 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemie👄
                  2⃣3⃣



           "In auresa? Taya zan auri ya na umma? Kokinsan me kke fad'i kuwa? Ubanmu d'aya fa dashy taya zan auri yaya na? Taya umma?" Umma tace "tabbas nasan me nake fad'i Saalihah sbd alhj Ahmad ba MAHAIFINKI bane! Kamar yadda Fudail ma ba WANKI bane. Tuni Saalihah ta mike ta zauna, "ba mahaifina ba? Den waye mahaifina?" Umma tace "abbanki shine mahaifinki Saalihah". Murmushin dayafi kuka zafi tayi sannan tace "taya kkeso inyi believing abinda kka fad'a umma, how? kawai so kke ki wanke kanki amman kam abba na ba mahaifina bane, umma kin cuce ni har abada ashe ni shgya ce shine baki tab'a gaya mun ba? Allah ze saqa min kin raba ni da soulmate d'ina umma koda na mutu kisan kece sila!" kafin umma tasake fad'in komi Saaly taja jakarta ta fice umma nata kiranta amman sam bata juya ba, a guje baaba ta gudu ta lab'e, motarta ta shiga a fusace ta fice. Nan baaba tashigo site na Saaly taga yadda umma keta sharara kuka tace "kukan me kuma hajara? Yau dubun ki ya cika. Ai dama na gaya miki dole wataran Saalihah xata gano gaskia kuma barata tab'a yafe miki ba, gashi nan ynxu  dan abinda kka aikata shekaru da suka wuce kin jefa rayuwar 'yarki cikin kunci". Umma dake kuka tace "amman baaba aikema kinsan Saalihah 'yar ibro ce, jininsa ke running a jikinta 'yarsa ce ba 'yar alhj Ahmad ba". Baaba tace "haka kka gayamun hajara amman har yau ban yarda ba, wayasan ko kwantar da ciki kkayi time da ibro ya auroki sbd sanin kanki ne wata bakwai kka yi a gdan nan kka haifo Saalihah, koba haka ba?" Cikin kuka umma ta giada kai "hakane amman wlh Saalihah 'yar ibro ce dan Allah ki yarda dani". Baaba tace "oho dai ni bari ibro ya dawo in gaya masa daman tun kafin ya auroki na gaya masa ni ban amince dake  ba amman sam yak'i jina sbd ban basa kwararren reason ba. Hajara nasan ki tun kafin ku had'u da ibro nd ansha gayamun halin ki, dake da 'yarki saalihah bakuda maraba KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA, halin ki hak ta d'auko bata ragar komi ba abinda yasa kuma har yau ban gaya wa ibro halinki ba shine dan naga yadda yake sonki, amman tunda yau Saalihah ma ta gano gaskia yana dawowa zan irga masa komi shima yasani seya sawwak'e miki da ke da shgyar ki cuz a wajena Sa'ad ne kawai jini na!" Tana kaiwa nan ta fice.
             Ba abinda umma keyi se suka dakyar ta iya tattara kanta tayi d'akinta ta d'au wayarta ta kira Saalihah, tun isar Saalihah hstl take kuka koda dasu bint suka tambayeta meya faru bata tanka su ba sude a ganinsu ko fad'a tayi da Fudail, tana cikin kukan wayarta tasoma ringing dubawanda tayi taga umma wata tsuka taja sannan tace "me zaki gayamun umma? Kin riga kinyi messing min rayuwa nakega kashe kaina kawai zanyi duka mu huta", hka wayar tata ringing amma sam tak'i daukawa daga karshe ma kashe wayar tayi gabadai. D'ayan wayarta ta dauka ta kira ruky kan su had'u a gdan alhj na mata kasancewar yyi tafiya bai gari. Acan ko suka had'u Saalihah tace "ruky in damuwa suka miki yawa me kkeyi kiji kin sauk'o?" Ruky tace "giya mana gaki a gdan giya wlh blive me kka sha shar zaki nemi damuwan ki kirasa," Saalihah tace "but bansan nafara shaye shaye ni kashe kaina kawai zanyi sbd rayuwata batada ma'ana anymore" nan ruky tayi ma wani waiter mgn ya kawo musu giyan, ta zuba wa Saaly a wata wine cup "ungo sha bliv me duk damuwarki xasu gushe", da kyar Saaly takai baki bata ciro ba kuwa sanda ta kwankwad'e tas! Ruky ta dad'a kara mata ta shanye sannan ta buga cup din kan table wani gani gani ta farayi take tasoma suratan banza tana dariya "wai ashe Fudail d'ina yaya na ne sesa nake sonsa sosai ashe", ta dawo da kallonta kan ruky "ai xan iya auran yaya na ko?" Ruky tace "what are u saying Saalihah? Fudail saurauinkin ne yayanki?" Saalihah tace "aww baki sani ba? Ai ubanmu d'aya uwa muka raba, ashe umma ta ba mutumiyar arxiki bace da kke gani na haka banida uba".... Haka tata suratan banza ruky na sauraronta can tayi assisting nata ta kaita motarta tamata resting kujerar. Bacci me kyau Saalihah tayi se caan ta tashy.
          Kanta kawai ta rike tana wani erin kallo, ruky dake chatting tun daxu tace "Saaly, har kin tashy?" Saaly tace "ya haka me mukeyi anan?" Ruky tayi murmushi "ya baki ji duk worries naki sun tafi ba? Saaly tace "sosai ma wlh me kka bani?" Ruky tace "giya mana da me zetafi miki da damuwa". Salati Saaly keyi "hba ruky taya xaki sani shan giya? Abubuwan da suke kaina already sun min yawa", ruky tace "abinda ban gane har ynxu ba shine mahaifinku d'aya da Fudail?" Saaly ta basar tayi kamar bata jita ba dan haka ruky tasake nanata abinda ta fada nanne Saaly tace "wace erin banzan mgn kke? Bayan kin sani na sha giya ai ba surutun da bazanyi ba", ruky tace "is that so? Believe me Saaly baran fad'a wa kowa ba tell me what is happening". Ta bud'e baki zatayi mgn kawai kuka yafi karfinta kuka takeyi sosai ruky tayi hugging nata tana bata hkr haka ta irga wa ruky komi  ta mugun bawa ruky tausayi takuma buk'ace ta datayi kokari ta cire san Fudail kawai a zuciyarta dan kuwa iyayensu barasu tab'a yarda da aurensu ba.
          Tana isa hstl ta kira Fudail dayazo ya dauketa zasui wata mgn kan tana jiransa ba gardama ya amsa da "toh" bayan 20mins ya iso a bayan gari ya tsaya. Fudail duk ya k'osa yaji me zata gaya masa. Fitowa tayi daga motar shima ya fito sannan ta juya masa baya tuni tafara zubda hawaye, baki na b'ari tace "Fudail my..my..br..brother, you are my brother!" cikin rashin fahimta ya dawo gabanta "what are u saying baby?" Murmushin takaici tayi "am not ur baby anymore Fudail am your SISTER", har ynxu fudail be fahimta ba jijjiqata yasoma yi "what are u saying Saalihah? Kamar ya am your brother? Talk to me!" hannunsa ta sauke daga rikon daya mata "dalilin dayasa daddy yace ban masa ba is bcuz am his daughter, fudail we are sharing thesame father". "Noo noo" abinda yake ta fad'i knan "dis cant be true Saalihah u can't be my sister" tuni idanunsa suka cike da hawaye hugging nata yayi tightly yana kuka tana kuka sannan ya skota yasa hannu ya goge mata hawaye "listen to me carefully Saalihah no matter what I'll marry you, I don't care ko ke sister na ko ba sister na ba keep that aside, kina sona ko?" Kai ta giada masa yace "nima ina sonki isn't that all that matters?" Nanma takuma giada masa kai yace "then kibar kuka haka ya isa kinji?" Haka ya mai da ita hstl, a fusace yake driving yana isa gda ya nufa straight parlour'n daddy yasamesa zaune akan kujera yana karanta newspaper, Fudail "ka dawo ne?" Sede kallon fuskarsa da yayi yaga idanunsa duk sun kad'a sunyi ja gawani erin numfashin daya keyi kamar zaki

No comments: