Thursday, 13 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  2⃣2⃣



            Nan fa iklima ta soma raba ido dan bata san wace amsa zata basa ba, Fudail yace "is there somethng ure not telling me?" Take "tace a'a fudail wace erin mgn kuma kake?" Fudail yace "ba sekin min karya ba iklima, there must be somethng ure not telling me in bahaka ba taya daddy zesan sunan umma'n Saalihah? Taya yasan sunanta hajara? Answer me!" B'ari ta soma "ni..ni.. nima bansani ba fudail halan ta mata kama da wata classmate nasa ne amman believe me fudail daddy'nka besan umman Saalihah ba". Fudail yace "i've heard enough barmin d'aki nd kisani before I wasn't so anxious in auri Saalihah but sbd abinda ke da daddy kukeyi kun sa na k'ara santa nd kun kuma k'ara min karfin guiwa kan aurenta!" yana kaiwa nan yaja pillow ya kwanta.
           Saalihah kuwa takasa samun sukuni shes so eager tasan komi, dalilin kiran umma data tayi bai shiga yasa ta kira Fudail kaman me jiran ta kira ya d'aga tace "sweetheart kasamu kayi mgn wa daddy?" Fudail yace "listen to me carefully baby..." nan ya irga mata komi Saalihah harda 'yar kollarta yace "but I assure you ina kan bakata na neman aurenki baby, I'll do whatevr it takes kizamo tawa, ke tawa ce saalihah so don't worry urself, okay?" Saalihah da tuni kuka yafi karfinta tace "okay sweetheart thank you", Fudail yace "toh kukan me kuma? Stop crying okay? Ya kin samu kinyi wa umma mgn?" Saalihah ta ce "a'a ina kiranta network ya soma seizing", fudail yace "really? anya ba abu take son b'oye miki ba?" Saalihah tace "I've suspected as much nima cuz tun data d'aga wayar har muka gaisa bata ce bata jina ba se sanda na tambayeta ko tasan daddy tace min wai ntwrk ba kyau". Fudail yace "wannan abu akoi abin dubawa, baby kinsan me nakeso dake?" Ta kad'a kai wane fudail na gabanta sannan tace "no"  yace "gbe kije gda kiyi all u have to do se umma ta gaya miki komi okay?" Tace "as u wish sweetheart" ahaka sukayi sallama. Da tunanin wannan abu both Fudail da Saalihah sukayi bacci.
        Washegary ko lectures bata je ba wanka tayi tayi breakfast ta d'au motarta se zango adaidai gaban gdansu tayi parking ta shiga yau ko kwalyan arziki batai ba attarchmnt dinma ba'a sa yau ba! D'akin umma da abba direct ta wuce bata d'au ko zata sameta ba sbd ko taje kasuwa amman se ga umma xaune tana kallon wata hausa film "ahhh Saalihah ta sannu da zuwa, karki gaya mun wata hutun kuka kuma?" Saalihah tace "a'a nazo ne muyi wata mgn" nan fa gaban umma yasoma fad'i dan wani erin kallon da Saalihah ke mata, k'arfin hali tayi tace 'wace mgn knan Saalihah?" Kafin Saalihah tayi mgnar baaba tashigo d'akin kallo Saaly ta watsa mata sannan taja hannun umma "muje site d'ina", binsu baaba tayi da kallo kofar parlourn ta ta bud'e da key'nta suka shiga ta rufo k'ofar sannan ta dawo da kallonta kan umma da keta raba ido tace "umma nasan jiya bawani ntwrk daya d'auke miki karya kka min dan haka yau nazo gda ki gaya mun gaskia umma karki min karya waye alhj Ahmad?" Baki na b'ari umma tace "alhj Ahmad kuma? Ni yau na fara jin name dinma, mesa? wani abu ne?" Saalihah tace "no umma sanda nace miki kar kimin karya dan Allah am asking u waye alhj Ahmad?" Umma taja hannunta suka xauna duk wannan mgn da sukeyi baaba na lab'e a bakin kofar tana jinsu.
       Umma tace "Saalihah ban gaya miki bane, bansan sa ba ko karya kkeson inmiki? Wai tsaya ma tukun, mesa kke tambayana ko waye shi?" Saalihah tace "sbd d'ansa Fudail wanda nakeson aura ya kaini gdansu jiya, shi alhj Ahmad din yace sam baran auri d'ansa ba nd yana gani na ya kira sunanki umma, tell me waye alhj Ahmad, me had'inki dashi? Me kka tab'a masa dayake blaming d'ina for ur mistakes, talk to me umma! Ko kinsan yadda nakeson Fudail? Wlh in ban auresa ba den rayuwata batada ma'ana", nan ta fashe cikin wata matsanancin kuka. Baaba dake lab'e tace "dama nasani dole wataran Saalihah zata gano gaskia dole wataran asirin Hajara ze tonu"*** umma tama rasa me zatace wa Saalihah dan wani erin kukan da Saalihah keyi.
         Duk setaji she's sorry for her, ji take kamar tayi reversing duniyar back then tayi correcting mistake d'in. Da kyar ta iya bud'e baki tace "ba haka bane Saalihah listen to me kinason Fudail bawanda ya isa ya hanaki aurensa se Allah, listen to me carefully; abbansa yak'i amincewa dake ne sbd ya d'au kedin... Sekuma tayi shiru Saalihah tace "well? Ki fad'a mun mana" umma tace "sbd ya d'au ke 'YARSA ce Saalihah!"
         Zabura Saalihah tayi tare da dafe kirji "what!? Umma? Ni? 'Yar daddy'n fudail innalillahi wa inna...." Bata k'are salatin ba ta sulale kasa nan umma ta tarota "Saalihah! Saalihah!" se tapping nata take a kumatu amman sam Saalihah bata ko motsa ba toilet ta nufa duk kayan cikin bangidan bata iya amfani dasu ba wajen sink ta nufa tata tab'e tab'enta amman sam ruwan yaki fitowa se hawaye take can data sa hannunta a karkashin  famfon sink d'in se ruwa yasoma fita nan ta d'au wata cup a bangidan ta tara ruwan acikin, tafito da gudu ta zuba wa Saalihah a jiki take ta soma tari, umma ta riko ta tana bata hkr. A hankali Saalihah ke mgn "shknan umma kin gama dani a rayuwa, kin cuceni umma zaki kasheni dan nasan ciwon zuciya ce zata kamani eventually in mutu, ko da ban kamu da ciwon zuciya ba I will rather commit suicide in kashe kaina in huta tunda Fudail BROTHER na ne UBANMU D'AYA, ba aure a tsakaninmu, wayyo Allah! ka kasheni in huta. Yanzu da wa na nata soyayya nabarsa yana tab'ani anyhow, haba umma kin cuceni a rayuwa umma. Wlh baran iya yafe soyayyan yaya na Fudail ba sede in kashe kaina kawai in huta in ban auri Fudail ba den bansan what else will I have to live for ba most of all abba na danakeso ni ba 'yarsa bace? Innalillahi! How could you umma? I shud have known yadda duk abinda nakeyi dukda kinsan ba abu me kyau nake ba baki tab'a min fad'a ba ashe halinki na dauko KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA... Sede ni ban tab'a kwanciya dana miji ba" ta cigaba da kukanta me runtse jiki. Umma dake sauraronta tana zubda zafaffun hawaye dan ba karya cikin abinda Saaly ta fad'i. Ta rungumota "no Saalihah 'yata kibar mgn haka, kbr magn bnza, mgnan kashe kanki be taso ba kina son Faudail dole ki auresa!"


      To masu karatu what is umma trying to say? Tana nufin zata aura ma ya kanwarsa kokuma ya?

No comments: