Sunday, 2 April 2017
KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
written by miemie👄
0⃣3⃣
"Ko Saalihah? Wai mesa a rayuwarki baki da kunya ne, oh! Ni hajara naga takaina, Allah de shirya min ke" tana kaiwa nan ta miqa mata kwanon ta fice. Bayan ta gama hadin garo garonta ta jawo wata kujera daga inda tagama wanke wanke daxu ta zauna akai tana cin abincinta. Sallamar baaba ce ke tashy a gdan (yar abban Saalihah da Sa'ad) Saalihah na jin sallaman amman ko a jikinta ta amsa ma se gabzan abincinta take, dattijuwa ce wanda barata gaza shekaru 58 ba, ta iso daidai gaban Saalihah da tayi kamar bata san mutum na kanta ba tace "ke ynxu Saalihah kinajin sallama baraki amsa ba? Wlh asara ta kama mu a gdan nan, ba mahaifiyarki kadai ba har ni ace kanina ya haifi maras kunyar 'ya kamar ki"...budan bakin Saalihah wai "baaba da kin dan matsa gefe kinsan daga rana kka fito to wlh baran boye miki ba jikinki du warin zufa yake kuma kinga abinci nakeci, dan matsa gefe pls baaba" tana mgn nan tana toshe hanci, baaba ta zaro ido "shegiyar yarinya ni kke gaya ma ina wari? Wallah iskancin kin yafara wuce gona da eri" nan ta daga hannu zata mari Saaliha kamin kyaftawan ido takai bakin kofa tana mata gwallo nan ne umma tajiyo hayaniya tafito tana "lafya?" Baaba tace "wlh asara ta kamaki hajara da kka haifi wannan fitsararriyan yarinyan, ni dama da Ibro (abban Saalihah da sa'ad) ya ji magana ta da be auro ki tun farko ki haifo mana wannan tambararriyan 'yarkin ba," Saalihah dake bakin kofa takai lomar abincinta na karshe tace "oho dai baaba aje ayi wanka, daman nasani tun ba yau ba hassada kke ma umma na, kuma abbana na sonta saisa ya aurota ba yadda kka iya dashy inba rashin zuciya ba kije kema kiyi auren mana, aww ashe kin taba yin aure mijin ya sake ki ko sbd me oho? Awww ynxu na tuna sbd ke juya ce ko?" Ran baaba ya bala'in baci, "wallahi yarinyan Allah ya isa, Allah kwashe miki dukkan albarkatunki na duniya ameen!" Idanta tuni suka cike da hawaye umma na bata hkr "dallah kema matsamin anan ai duk kanwan ja ce KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...kedin be marabarki da 'yarki? Wlh bari ibro ya dawo tafiya zanyi baran zauna a gdan nan wannan tambararriyar 'yarki tasamin hawan jini ba," ta dawo da kallonta kan Saalihah "banyi jika da ke bane Saalihah amman kke gayamun mgn" a fusace ta shige daki tafara tattara kayakinta cikin wata ghana must go Saalihah kuwa na a bakin kofar "kiya ji dashy haka kawai kzo gdan ubana dan shinkafan da muke dan samu kibi ki sa masa ido, inda munada kudi fa? Ai nikega har cikin mu sekin shiga tunda baki barmu a talauci ba ma," umma ce ta matso kusa da ita "haba Saalihah taya zakiyi ma babarki mgn haka? Bafa sa'arki bace tafa girmi mahaifinki kinsan kuwa koda ban da rai ita zata kula daku bekamata ki gaya mata mgn haka ba, ynxu wuce kije ki bata hkr?" "Hakiri fa kkace umma? Ai saidai mu daga hannu mu gode ma Allah tunda ita dakanta tace zata tafi lokacin islamiya takusa ni zan fara shiri," tana kaiwa nan tashige daki. Bayan 30mins abba yadawo daga kasuwa kasancewar me gyaran erinsu agoguna hakan nanne "sannu da zuwa" umma ta amsa tayi serving nasa abinci, tace "malam kaje kaba ma baaba hkr tun daxu take shirya kayakinta wai tafiya zatayi ko abinci taki ci," bayan ya kai loma daya baki yace "zata tafi kuma? Zuwa ina? A dalilin meh?" Umma zata fara mgn kenan baaba tafito "a dalilin rashin kunya da fitsaran da 'yarka Saalihah tamin" tana mgn nan tana kuka "yarinyan bata da mutunci ibro ba kalan zagin da bata min ba dazu inda ba na danna zuciya na bane wlh da ynxu haka tana gadon asibiti" Saalihah data labe daga bakin kofa tana sauraronsu ta fasheda dariya, "ni ko ke? Ai kece zaki kare a gadon asibiti bani ba" nn taci gaba da goga kwallin dake hannunta a idanta tagama ta zagaya bakinta dashy***"haba hjy fatsuma ynxu fisabilillahi sbd Saalihah sekice zaki bar gdan nan? Saalihan dududu nawa take da zata kora ki? Amman kin bada ni wlh zo muci abinci dallah ki manta da zancen Saalihah," baaba tace "kaide kullum haka kakemun" nan ta kariso inda abba da umma suke tace da umma "dibo min abincin nima." Saalihah da Sa'ad ne suka fito daga dakinsu suna sanyaye da uniform na islamiyar su "sannu da zuwa abba," yawwa sannu "'ya'ya na nawa na kaina zaku je islamiya ne?" Sa'ad yce "eh abba," abba yasa hannu a aljihu yaciro wata kodaddiyar ishirin "hungo kasiya alawa dashi" ya amsa yana murna, "uwata Saalihah fa? Kema zaki sai alawan ne?" "A mana abba nidin ba mutum bace?" To hungo kema kafin ta amsa baaba tasa hannu ta wabje "wlh baraki sai alawan nan ba yau," dariya sosai Saalihah tayi "oh baaba tawa ta kaina kinsan ina ji dake sosai ai 'yar ishirin ce na baki mutafi Sa'ad, umma mun tafi" nan suka fice. Abba yace "Saalihah fa uwarmu ce Hjy fatsuma sesa nike mutuwan santa bansan komi ya sameta, gashi nan uwarki ta miki kyautan ishirin," tsuka baaba taja "wlh wannan Saalihah kam ba uwata bace dan uwata batada banzan halin 'yar nan."*** A islamiya a ajinsu Saalihah malam na karin karatu Saalihah na buga game a waya kafin ta hankara kawai taji sauqan bulala a baya wata uwa uba ashar ta dura "wlh toh daga yau an dena karatun islamiyan tuda dama nasamu na sallah, zaka zuba min wannan wayan engine a baya ajinka jaka ce ni?" Ledar da takesa littafafanta ta ja "azzalumi kawai Allah ya isa, a haka kuma zaka kare a malamin islamiya me albashi N5,000 a wata" tana kaiwa nan ta fice da gudu...
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment