Sunday, 2 April 2017
KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
written by miemie👄
0⃣2⃣
"Ya akayi?" Da fuskar nan tata a tamke, "haba sarauniyar mata yau ba gaisuwa kuma ga fuskar nan a bace haka, meya faru pls? Banson ganinki a haka"... Ta katse sa "baka son gani na ahaka?" Kai ya gyada mata tacigaba "toh seka daina zuwa gu na, ai tun ba yau ba na gaya maka baran taba kula kaba sekayi kudi, dubeni da kyau"... tana me juyawa "zubin masu kudi ne dani, me xanyi da talaka bujaki kamar ka?" Yunusa daya wangale baki yana kallonta yace "haba Saaliha ya kke mgna haka, arzikinnan de nufin Allah ne bakisani ba halan bayan munyi aure Allah yayi mani budi"... katsesa takuma yi "toh yamaka budin mana ynxu, nide na gaya maka daga yau kada ka sake tako gajiyayyun slippers naka" tana kallon slippers nasan "ka tako gdan nan" ta juya zata shige gda yunusa yace "amman kisani kema 'yar talaka ce be kamata ki 'kyamaci talaka dan uwan kiba" kallo ta watsa masa "baran musanta kaba sbd kayi gaskia ubana talaka ne amman yadace inci miyan kuka a gdan ubana sannan injeni gdan wani in kuma ci? A rayuwa akoi change so kaje kayi kudi nikuwa na maka alqawari zan aureka" tana kaiwa nan ta shige gda. Baby nokia'nta ta dauka tana buga snake xenzia can data fadi ta ajiye taje ta jido ruwan rijiya ta fara wanke wanke, wayyo xanso kuga wanke wanken walaqancin da Saaliha keyi sekace ba kwanukan da za'a ci abinci a ciki ba, Sa'ad ne yafito daga daki yana rike ciki, "me ke damun ka kaikum" ta tambayesa a takaice, yace "yunwa nakeji ya Saalihah," dariya tayi sosai "qyar, qyar, qyar, qyar yunwa kakeji? Toh babu abinci kajira umma ta dawo ta aza mana," Sa'ad da har ynxu be sake cikinsa ba yace "ya Salihah ba kullum ke kke mana abinci ba," bata san sanda ta fusata ba "toh shegen yaro nakiyi yau semuga meye za'a mun wlh karka bata min rai akan wannan talaucin dayake damuna in sassaba maka," shiru yayi ya koma daki yasoma kuka har bacci yayi awon gaba dashy... Da wanke wanken walaqnacin har ta gama. Daidai 2:15PM umma ta dawo, kallo daya na mata nasan cewa umman Saalihah ce dan wani erin mahaukacin kaman da sukeyi wane an raba kara, banbancin su shekaru ne kawai sekuma da haske dan umma ba baqa bace erin ruwan tarwadan nan ce, sallama tayi sannan ta ajiye rogowar kayan miyan dake kanta dagani me siyar da kayan miya akan table ne, Saalihah naji taki amsawa seda umma takuma yin wata sallaman sannan tafito ta amsa ko sannu da zuwa babu, umma tace "ina dan auta na?" Saalihah tace "gahi can yayi bacci bayan kukan yunwan daya gamayi" tana maganan ne tana buga game na bounce, cikin rashin fahimta umma tace "yunwa kuma a dalilin meh?" Saalihah data turo O shaped lips nata tace "a dalilin ba abinci man umma, murhunkin yaki kamawa nayi nayi amman sam yakici ba kalanzir enough," umma ta wangale baki tana kallon ikon Allah "lalle Saalihah wallahi Allah shryeki yanzu sbd Allah tun safiya Sa'ad be kuma cin abinci ba? Kuma ko kunya bakiji ba kina cemin wai wutan yaki kamawa dan ba kalanzir? Eh Saalihah?" "Eh mana umma ai gaskia ne ba kalanzir.." tafara guna guni "ni wlh talaucin nan ya isheni"...umma data jiyota tace "seki kashe kanki ai matsa min anan" tabi ta gefenta taje dakyar ta iya ta hura wutan ya kama ta aza girkin farar shinkafa ce, yana nuna ta sauke tasa mai da gishiri da yaji taje ta ta da Sa'ad dake bacci ta miqa masa godiya yamata sannan ya wanko bakinsa ya zauna ya gabza garo garonsa, can umma ta jiyo qara a kitchen tana leqawa taga Saalihah na diban shinkafan a kwanonta itama, "ke Saalihah! Me kke yi?" "Diban abinci mana umma" nan tagama diba taje ta fara sa mangyada kwanon hannunta umma ta wabje "ai barakici abincin nan yau ba tunda bake kka dafa ba," atake ta soma shakwaba "umma dan Allah kiyi hkr wlh yunwa nikeji," "kinsan kinajin yunwan shine kka ki hura wutan ki dafa?" "Wlh umma yaki huruwa ne" tana me goge yar kwallar data matsosa dan dolensa ya fito, umma tace "ni da na hura ai ba mutum ce ni ba ko?" Saalihah da fitsara wai "to ai umma ke kin saba da wahala...
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment