Saturday, 29 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA


      written by miemiebee👄
                  3⃣2⃣



     Bayan har ta shiga gda se kuma ta sake fitowa ta iske Yunusa tsaye yadda ta barsa mak'udan kud'ad'en da ita kanta bata san yawansu ba ta watsa masa "I think this will help sobber you up kasani ni ba class naka bane". Fewww ta wuce ciki umma tafara k'olla ma kira tana shiga d'akinsu da abba can tajiyo muryan umma daga d'akin Sa'ad da sauri ta nufa inda take ganin yadda idanun umma suka kumbura, yasa tafara jero mata tambayoyi, "ya haka umma? Kuka kkayi ne? Lfya dai ko?" K'arfin hali umma tayi tace "lfya qlou Saalihah ta daga ina haka?" Sede Saalihah bata yarda da abinda umma ta gaya mata ba dan haka taja hannunta suka zauna tsakar gda.
        "Gayamun umma meke damunki, keda baaba ne?" Kai ta kad'a mata da nufin a'a. "Toh meh?" Tuni kuka yaci karfin umma "Saalihah abbanki ya kora ni daga d'akinsa duda an gano gaskian al'amarin ynxu amman sam yak'i ya yafemun mucigaba da zama kamar da". Zabura Saaly tayi "whaat!? Taya? Ynxu ina zakije?" Umma tace "d'akin Sa'ad na koma", nan Saaly takama hanyan shiga d'akin Sa'a dan ciro kayakin umma. Umma ta rik'o hannunta "me kke shirin yi?"  "Me kuwa umma? Kayakinki zan tattara miki ki koma d'akin abba..."  "A'a Saalihah dan Allah ki rufa min asiri wannan punishment d'ina ne dole nayi hkr" ba yadda Saaly batai da umma ba sam tak'i daga k'arshe tace toh su koma site nata mana nan ma umma tak'i bundle na N1000 ta bawa umma sbd zata koma sch gbe nan ma da kyar umma ta amsa.
        Site nata ta nufa ta bud'e drawer'n da take ajiye kud'ad'enta baki wangalau na bud'e dan kuwa karamin bundle dake gun shine na N200 daga na N500, N1000 se $50(dollars) gasu nan dayawa ba adadi. Tsuka taja "mstww ni wlh ban san ina zan kai wannan kud'ad'e ba, ni tsaya ma na bank acct na miliyan goma sha nawa nema? Oho dai! Ni ynxu sabon acct zan bud'e in ajiye wadannan dan ko har ynxu credit card na wancen shashashan alhj'n akoi kud'i aciki duk uban siyayyan da na rigayi kud'in be k'are ba..." had'a kud'ad'en ta somayi gu d'aya tana cikin yi umma tayi sallama kamin tace meh umma tariga taga kud'in da sauri ta nufo gabanta tana me nanata salati da hannayenta biyu aka! "Saalihah! Meh..meh wannan? Kud'i haka? Dan Allah ki rufa ma kanki asiri ki rufa min nawa ki maida kud'in nan inda kka samosu, innalillahi!" Saalihah dataci fuska tace "meh haka umma? Ce miki akayi kud'in sata ne? To ai nima ba nawa bane adana Fudail yabani in masa in bahaka ba ina zan samu kud'i me yawa haka? Karki damu bama nawa bane..."  "Uhn uhn fa Saalihah" inji umma da fad'i Saaly tace "aw baki yarda ba knan? In kira miki shi ne kiji daga bakinsa?" Nan ta d'au wayar kamar dgsk umma tace "a'a tunda haka kkace seki adana masa da kyau ai kar wani abu ya b'ata ko yya?" Tana murmusawa tace "kar ki damu umma barin aiki driver ya siyo mana dinner ko?" Umma tace "a'a bari zan dafa mana", Saaly tace "a'a de ke ynxu kije ki huta kinji umma? Karki damu".
         Har umma takai bakin k'ofa seta tuna da wani abu ta juyo "yawwa Saalihah ina kanwar abbanki hajja bintu wacce take lagos dinnan?" Saalihah tace "ohhh! eh nagane ta wani abu ne?" Umma tacigaba "daxu mukayi waya da ita take cemun wai yaushe zaki shiga babbar makaranta cike da mamaki nace mata ai kina lvl 3 ma ynxu ko?" Saaly ta giada kai umma tace "eh wlh tace akoi kwancen kayan da takeson baki kina ado dashy a makaranta, ai hajja bintu akoi kirki wlh". Daga bisani kawai Saaly ta fashe da dariya "kwance? Ni in sa kwance? Heheheh wonders never end! Ai seki cemata inada saurayin dake siyan min duk abinda nikeso ta rik'e abinta kawai". Umma tace "haba Saalihah ya kke mgn haka a da d'in ba tana kawo maki ba kuma kina sawa, mesa kke haka ne?" "Toh umma dan Allah budurwa kamar ni se insa kwance wlh duk fad'in duniyan nan banga kayan da baran iya siya ba koda kuwa da da zaren silver yadin gold aka d'inka". Nasiha sosai umma tamata daga karshe tace "toh naji zan amsa in an kawo" umma bata kai da fita ba abba ya dawo gda yana k'olla ma Saalihah kira.
        A tare suka fice da umma tare da masa sannu da zuwa a takaice ya amsa ba tare da ya kalli umma ba "yawwa mahaifiyata gashi nan 'yarki ta kawo miki kaya hajja bintu dake lagos, kin gane ta aiko?" Shiru Saaly tayi sanda umma tad'an bigeta a hannu sannan tace "eh nagane ta maman amal ba? Ya take?" Abba yace "qlou wlh gashy seki dudduba" hannu ta mik'a ta amsa tare da mai godia nan suka koma cikin site nata da umma. Maghrib suka idar sannan umma ta zazzage kayakin bisa gadon Saaly ga kaya fa ba dama ciki harda supopi guda biyu da holland d'aya sannan kananun zannwa guda uku da takalma biyu da mayafai rage kayakin kawai xatayi shknan. Haka Saaly ta k'are ma kayan kallo sannan ta fashe cikin wani erin dariya tsayuwa umma  tayi tana kallon ikon Allah daga bisani tace "ke Saalihah me haka? Se abbanki yafito yaganki haka ne? Ki kama kanki mana",  tana dariya tana mgn "ynxu dan Alllah umma wannan kayaki kukeso insa inshiga dasu cikin ATBU? Ni Saaly baby da ake ma kallon ajebour, Lol lalle kam una try oo nikam tayani tattarasu dan ba wanda yamin anan sede in ke zaki ragesu na baki kyauta itama baaba in tanaso seku raba".
       Umma bata sake fad'in ko k'ala ba tattara kayakin tayi waje dasu can bayan isha driver ya kawo musu abinci bayan sun gama ci a tsakar gda kowa yayi d'akinsa. Abba kuwa koda ya tambayi Saaly ina take samun kud'i ce masa take Fudail ne ke bata.
         Washegary bayan ta isa sch ruky ta kirata "ammata yane?"  "Qlou qlou fa na gaya miki kuwa? Fudail nd I aren't sibling, aure tsakani na dashy consider it done baby!" ruky tayi exclaiming "wow! naji miki dad'i kice ynxu xaki cigaba da rocking rayuwarki", Saaly tace "sekin fad'a ne daman ina da niyan kiranki ma yau shin akwai harka kuwa?" Ruky tace "sosai wani alhj ne xetaho daga abuja yau cemin akayi range rover latest model yake hawa". Saaly data soma tand'e jan bakin bakinta tace "ke haba de?" Ruky tace "ai ki bari kawai Allah kaimu tonight", Saaly tace "ameen yau nayi arxiki dan zan ma wannan alhj d'anyen aikin da ban tab'a ma wani mahaluk'i ba!"
     Ni miemie nace "wani erin danyen aiki knan???"


 
   beeenovels.mywapblog.com

No comments: