Here is a book of mine I wrote in the year 2k16 some chapters are missing tho but I still wanna share it with you people so enjoy.
written by miemie👄
0️⃣1️⃣
'Yar budurwace me qimanin shekara 17, fresh graduate na Mu'azu High School (govt sch) wacce tasamu scholarship into ATBU dan ilimin da take dashy. Chocolate skinned ce sede kamar barata gama kai chocolate din ba amman kyakkayawa ce ajin farko, idanunta a lumshe suke yan daidai sede akoi hanci kam siriri kuma dogo wanda ya tafi da siriryar fuskarta, in ba wai an fada bane za'a dau pouting lips nata take dan haka suke, O shaped lips take da, tana da gashy daidan gwargwado wanda in tayi parking yana dan taba bayanta, doguwa ce tana da dan kauri daidai. Tana zaune ne a qarqashin murhu acikin gdan mahaifinta wanda kallo daya akayi ma gdan ansan talauci na dukansu, a unguwar zango dake jihar bauchi suke da zama. Banda talaucin dake dukan wadannan bayin Allah ga kazanta kamar ba gobe ko ina a gdan is littered da papers, wanke wanke yayi jugum duk kud'a suna bi ta dayan side din kuwa kayan wanki ne wanda ga dukkan alamu harda na amalala aciki dan yadda kud'aje suke waka a gdan, ga wata katifar da aka shanya kan rana wanda ta sha uwa uba amalala ko ina ajiki jirwayen fitsarin kwance ne kwata kwata gdan d'akuna uku ne a jare da kofofin metal irin na da da dinnan. Wannan budurwa dake cikin wata kitchen na gargajiya da aka kebe frm one angle acikin gdan ba kowa bace illa SAALIHAH, tana sanye ne da wata kodaddiyar atamfa erin zanin N1,800 dinnan wanda baida kala, riga da zani wani flay, gutsirin kwalin indomie ne a hannunta se hura murhun dake gabantan take idanunta da suke a lumshe duk sun k'ada sunyi ja amman sam wutan yaki ci kasancewar ba kalanzir na arziki aka sa masa ba illa laidojin da aka cika masa tsaki taja "mstwww wallahi Allah wadar din talauci dan durun uwan wutan nan tun daxu nike hurawa yakiyi toh wallahi nagaji in umma tazo ta aza girkin da kanta mtsw" nan ta jefar da 'yar kwalin dake hannunta ta fice izuwa inda loadin kayan wankin ke, "sa'ad dan banzan yaro kawai sa'ad! Sa'ad!" Kiransa take wane wanda zata basa kudi "na'am adda saalihah gani," daga wata daki ya fito yaro ne wanda bare gaza shekaru 8 ba da wando irin neaker dinnan bama kaya a jikinsa kasancewar zafin da ake papawa... "zo nan shege kai bakasan ka girma bako? Kullum cikin amalala ai wallah ajin ku na boko zanje in gaya ma 'yan ajinku kai amalala ne, gardi dakai ka tsaya kana fitsarin kwance ai kataho yau kai zakayi wankin nan shege kawai" zungura qeyarsa tayi wanda tasha malu har wani kamar mirror yake ga kan nan fari tas! tasa sa yayi soaking kayakin cikin wata ruwa me dauda wanda kalarta ya koma kamar anyi mixing ruwa da madara dan dotti dagani ruwn rijiya ne ahaka har suka fara wankin dawata sabulu me uban wari wanda ake kira da "Kenu" suna cikin wankin wayarta qirar nokia baby me torchlight tafara vibrating tana kai dubanta kan screen din taga "gajiyayye" tsuka taja "wlh wannan gajiyayyen gayen ya isheni ba warkardani zeyi daga wannan uwa uba talaucin datake damuna ba se uban kira dan ubansa shima," sa'ad dake daurewa kayan amalalansa besan sanda ya fara dariya ba kallo ta watsa masa "shege ma wa kake dariya? Da kanka kamar madubin gdan saloon" Nan yacigaba da harkan gabansa, danyen hannunta tagoga ajikin kodaddiyar zaninta sannan ta daga wayar ko hello din zamani babu "salamu alaikum" tace gajiyayyen gayen yace "wa'alaikissalam sarauniyar mata, gani a bakin kofa ki taimaka kifito pls" zata fara complaining yace "pls saalihah" yayi hanging tsuka takuma ja, "wlh yau zan koya ma yunusa hankali," sanda suka karisa wankin harda shanya sannan ta jawo wata hijabinta wanda da katon hoton M.A (governor in Bauchi) ajiki tasa ta isa gun langa langan bakin kofarsu taja ta tarar da yunusa yayi cross legging kafa ajikin bango yana jiranta irin babban gaye dinnan, ko gaishesa batai ba yace "sarauniyar mata knan," kallo ta watsa masa sannan tace...
No comments:
Post a Comment