Thursday, 13 April 2017
KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
written by miemiebee👄
2⃣1⃣
Daddy yace "anan bauchi take?" Saalihah tace "eh daddy" ya wayince "ohhh kama ne knan dan ni wanda na sani a jigawa take, toh barin bar ku tare, mummy'n fudail ta fita nakega da kyar had'uwanku yayi". Saalihah tace "ba komai daddy", nan ya fice d'aki sede ya kasa zama gu d'aya se safa da marwa yakeyi a d'akin yana fadin "ya Allah karka tona min asiri haka, ya Allah banason d'ana Fudail yasan abinda na tab'a aikatawa for all these years yana respecting dina yana gani na da mutunci how will he feel in na tinkare sa da wannan mgn? Ya Allah ka cire son wannan yarinya daga zuciyarsa dan am sure 'yar hajara ce wannan!"
Hira suka d'an tab'a Saaly taga de mummy ba zuwa xatayi ba tace Fudail ya mai da ita hstl, hakan kuwa sukayi. A cikin mota Saalihah tace "sweetheart dont u think akoi wata boyayyen al'amari behind this, come to think of it ur dad knows my mum", Fudail dake driving yace "sosai kinga kuwa baramu sha wahalan had'a kansu ba cuz it seems like sun san juna", Saalihah tayi shiru dan haka Fudail yace "why the silence baby? What is it?" tab'e baki tayi sannan tace "no baka ganeba har ynxu, yadda daddy yayi exclaiming sunan umma is not just about sun san juna, I can feel it akoi wata boyayyen al'amari dabamu sani ba. Muje a sun san junan ma, taya?" Fudail yace "come on baby dont think like that kkasan ko childhood frnd tasa ce, mayb sunyi primary sch tare" Saaly tace "no sweetheart umma bata tab'a attendn sch ba" Fudail yace "baby mubar komi wa Allah ina isa gda xan tambayi daddy komi in details kema ask umma, okay?" Kai ta gyada masa daganan basu sake fad'in komi ba har ya kaita gaban hstl yafito ya rakata har bakin kofar dakinsu sukayi hugging sannan ya fice itakuma ta shigo. Ba kowa a d'akin kayan jikinta ta rage ta dau wayarta takira umma bugu d'aya biyu umma ta d'aga bayan sun gaisa Saalihah tace "umma nikam kinsan wani alhj Ahmad??" Salati kawai umma keyi a hankl takasa fad'in komi, dan haka Saaly tace "umma? Bakijina ne?" Da kyar umma ta iya bud'e bakin tace "eh bana jinki, hello? Hello?" A haka ta katse wayar, daga nan koda Saaly ta kuma trying kuma bai shiga dan umma kashe wayar ta tayi gabad'ai!
Wayar ta rungume tana salati "a'a dis can't be happening Saalihah barata tab'a sanin abinda na tab'a aikatawa ba, Ya Allah karka tozartani a idan 'yata haka. Tsaya, taya ma Saalihah zata san alhj ahmad? Kode wani alhj na daban take referring to ba alhj ahmad danasani ba." Wata zuciyar tace "uhn uhn Hajara karkiyi decieving kanki". Salati take ta nanatawa****
"Yawwa Fudail har ka dawo?" Inji daddy da fadi, Fudail ya amsa da "yes father, dama akoi wata tambayar da nikeson maka in ba matsala," daddy yace "wat does my son wants? nima inason muyi wata mgn da kai". Cikin rashin fahimta Fudail yace "mgn? To am all ears..." Daddy yace "umarni zan baka ba shawara ba Fudail nd dole kayi biyayya dashy, though daman baka tab'a sab'a wa d'aya daga cikin umrani na ba. Batun wannan yarinyan da kake son auran ne YOU CAN'T MARRY HER!" zabura fudail yayi "whaattt? Why?? Why won't I marry her? A dalilin kanada wanda xaka had'a ni da ita ko meh?" Daddy yace "calm down Fudail nd respect ur words am ur father taya xaka na min mgn haka? Sit down". Da kyar ya zauna yace "father pls karka min haka pls, me Saalihah ta maka da zaka ce baran aureta ba?" Daddy yace "bata min komi ba nide kawai bata kwanta min a rai bane..." Fudail ya katse sa "a'a father ban san ka da wannan hali ba ever since frm childhood duk abinda nakeso shi kakeso kaima baka tab'a k'in abinda nakeso ba se yau, how? just tell me father what is it? I promise i'll understand u". Daddy dake mgn zuci yace "noo son baran tab'a iya fada maka ba sirri na ne bekamata in sanar dakai ba", nan yabar mgn zucin yace "believe me son ba komai kawai ni bata kwanta min a zuciya bane". Fudail kuwa tuni yasan akoi abin dubawa cikin wannan lamari just as how Saaly ta fada masa d'axu. Ba tare da ya kuma fad'in komi ba ya nufa d'akinsa a fusace, daidai yana barin parlour'n mummy ke dawowa ko mgn be mata ba da sauri ta karasa parlour'n "alhj ya haka? Yau kai da d'an gaban goshinka ne kukayi fad'a?" Daddy yace "zauna iklima(mummy)", nan ta zauna.
Yace "ko zaki iya tuna Hajara?" Iklima tace "ai baran tab'a mantawa da wancen shgyar data kusan shiga tsakaninmu ba", daddy yace "ba abinda na tambayeki ba knan inkuma kishin da kka saba yi anytime nakira sunanta zakimin shiknan tashi kiyi tafyar ki". Iklima tace "a'a alhj dan Allah yi hkr ka gayamun wani abu ta maka?" Daddy ya leqa kofar ya tabbata ba kowa agun sannan yace "'yarta Fudail keda niyan aura kuma kinsan..." Iklima ta katsesa "whaattt? Innalillahi, ai bareyi mu barsa ya aureta ba dole mu hanasa. But wait, alhj taya kasan cewa ita yarinyar 'yar hajara ce?" Daddy yace "taya baran gane ba bayan kaman da sukeyi, banbancin shekaru ne kawai amman kaman su kam ya b'aci kamar an raba kara". Iklima dake salati tun daxu tace "ni shknan matan nan barata tab'a fita ta bar min kai ba, tunda bata samu ta aureka ba shine ta turo
'yarta ta auri d'anka wato, to wlh bata isa ba! In shaa Allahu haka bare faru ba I'll do whatever it takes in hana aukuwan wannan aure dan kuwa ko muslince muka bari sukayi auren nan muma da namu zunubin cuz they are SIBLING (BROTHER ND SISTER!)"
Daddy yace "lower ur voice pls banason Fudail yaji wannan mgn kamar yadda tun da yake yaro be tab'a sani ba bana son ya tab'a sani, this is my secret banason Fudail yasani". Iklima tace "toh alhj ya zamui ynxu? Ni nasan Fudail da taurin kai wlh inba wano kwararren reason muka basa ba bare tab'a yarda ba, what do we do now?" Daddy yace "koda sharri yakamata muyi ma yarinyan dole muyi cuz we can't allow him to marry he's own SISTER! yanzu kede kije ki kwantar masa da hnkl ki nuna kwata kwata kema yarinyar bata kwanta miki a rai ba". Iklima tace "lalle fa alhj kana magn sekace ni na tsuguna na haifi Fudail, sanin kanka ne Fudail bai tab'a sauraron abinda na gaya masa ba tun yana d'an yaro. Dan har yau gani yake nice silar rabuwarka da mahaifiyarsa duda a ynxu bata raye still be dena kallo na ahaka ba". Daddy yace "it still doesn't matter kiyi iya kokarinki ki shawo kansa, am asking of u plz" iklima tace "toh alhj katka damu barin gwada masa mgn".
Site na Fudail ta nufa wanda shima babban mansion ne na kansa upstairs, sallama tayi bisa kofar d'akin sam yaki amsawa dan haka tasa kai wani harara ya watsa mata "me kuma kke min a d'aki? Ni na baki permission na shiga?" Bata tanka sa ba tanemi waje ta zauna "Fudail my son, yanzu daddy'nka ke gaya mun kan ka kawo Saalihah daxu..." shiru ya mata ta cigaba "a gaskia baran boye maka ba Fudail daddy yace bata kwanta masa a rai ba nd base on how ya yake mgnar duda ban ganta ba nima naji bata kwanta min ba". Dariya ya b'arke da "lol ke asuwa? Da Saalihah ta miki da bata miki ba it wont change a fact". Iklima tace "Fudail nasan baka tab'a jin magana ta ba but believe it or not ina sonka nd I'll want only the best for you kabi shawarar daddy kar ka auri Saalihah u might end up cheating urself bahaushe yace abinda babba ya hango koda yaro ya hau kan tudu bare hango ba, believe me its for the best". Fudail ya taso ya zauna yana kallonta sannan ya kirata da "mummy" abinda be tab'a ba dan da tsiraran sunanta Iklima yake kiranta tun yana d'an yaro. Cike da zumud'i tace "na'am son" Fudail yace "you've akways wanted to be a mother to me ko?" Kai ta gyada masa, yacigaba "nd I've never allowed u to do so right?" Nan ma kai takuma giada wa yacigaba "zan iya baki that opportunity now but under one condition". Iklima tace "wani condition knan Fudail?" Yace "tell me the truth mesa daddy baya son na auri Saalihah? nd kema mesa kke goya masa baya? cuz da Saalihah tazo nan bawai shirin batsa tai ba abaya tasa nd cikin ladabi da biyayya ta gaishe da daddy, taya zece bata kwanta masa a rai ba?"
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment