Friday, 24 March 2017

‘YAR GATA CE!

 BY MIEMIEBEE
PAGE 71
March 2017




  _Where is the Most Sweetest Angel of them all? MY SUPER STYLISH BITCH. Just in a swift motion kika zame YAR GATAN MIEMIEBEE, know that I am head over hills in love with you, ina godiya da kalan soyayyar da kike nunawa ZAIMEEN🔥 and YGC🎀 in whole. You guys are always on my mind Mio 17 Babe Cute Xarah, Ashnur Pyar (indian Babeh) and Queen Meemi. A big shoutout to you Lovers #OneLove💞 Team YGC!🎀_

  ***
      Life moved on, cikin Zeezee se dad'a girma yake a hankali a hankali. Two weeks d'in ya k'ara mata, cikin two weeks d'innan Zeezee ji take just like a Queen se abinda takeso Al'ameen yake mata.
  Tun ana saura kwana biyu Al'ameen ya koma Abj Zeezee ta soma kumbure-kumbure, shi kuwa binta yake a hankali saboda condition nata. Murmushi ma ta d'auke yi masa. A ranan da ze tafi ya d'ago akwatinsa dan shirya kayakinsa ciki. Dama on normal basis Zeezee ke tayasa su shirya atimes kan ma ita ke shirya masa ita kad'ai amman banda yau. Juya mai baya tayi tana kwance bisa kan gado Tana game abinta.
   "Princess?" Banza da shi tayi sanda ya tako har zuwa gabanta, take ta gwada juyawa wanda tuni ya kama hannunta. "Princess yau bazaki tayani shirya kayakina ba?" Baki ta tura mai tare da had'e rai without saying a word. "Haba mana Princess ke shikenan kullum muna abu d'aya kenan?"
   "Ni ka sake min hannu bacci nake ji."
  "Bacci? Yaushe kika fara bacci by 8pm?"
  "Yau" ta fad'a a takaice.
   "Bazaki tayani ba kenan?"
  "Eh mana ni banason ka tafi meyasa zan taya ka shiri?"
  "LOL toh shikenan zanje in had'a abu na." Har ya miqe seta rik'o hannunsa tare da jansa da iya k'arfinta seda ya fad'a kan gadon a gefenta. "I don't want you to go." Ta fad'a tana lumewa jikinsa, hugging nata yayi gagam.
  "And I don't wanna go either." A hankali ta raba jikinta daga nasa ta miqe "muje mu had'a maka."
  "Kin huce?"
   "Nop kawai zan taya kane bana son ka gaji kai kad'ai is better mu gaji together." Pecking forehead nata yayi sannan suka k'arisa gun wardrobe d'in. Sede wani hanzari ba gudu ba yau Zeezee ta lura da yawan adadin kayakin da Al'ameeen keta iba.
   "Sweetheart kayakin nan na zuwa ina ne?"
   "Abj of course."
   "I know I mean sunyi yawa."
  "You think so?" Yayi maganan chan ciki ciki wane me 6oye abu yana susan back head nasa.
  "Sweetheart you're hiding something away from me." Ta fad'a bayan dogon nazarin da tayi.
   "I'm not Princess."
  "Toh mesa kake iban kayaki dayawa haka? Shekara zakayi ne achan d'in?"

      "Shekara kuma Princess? Saboda incaseties ne kawai."
  "Ban yarda ba, zaka jima ne ko? Maybe dan k'ara maka sati biyun da sun kayin ne sukayi demanding prolonging stay naka achan d'in am I right?"
  "What are you talking about Princess kin d'auka wai ni tafiyan nan dad'i yake min ne? 2 months kawai zanyi in dawo."
  "Are you sure My Soldier?"
   "In shaa Allah." Murmushi kad'an ta saki masa a yayinda shima ya miyar mata but deep inside tunanin ya zeyi ya 6ullo mata da al'amarin yake yasani shi da ya sake dawowa se nan da 3 months ko fiye da haka ma. Suna hira suna shirya kayakin har suka gama suka watsa ruwa sannan suka kwanta cozy under the blanket.

    Kamar yadda Zeezee ta saba ko wani tafiyan Al'ameen se tayita kuka haka wannan karan ma, ko rakosa waje ta kasa, everlasting kiss ya bata sannan wa baby'nsu ya fice. Tun safiya ta kama kuka har seda bacci 6arawo yayi gaba da ita se bayan Azahar ta tashi inda ta tarar da several missed calls nasa. Seda ta idar da Sallan ta dawo ta kirasa.

   "Hello Princess?"
  "Na'am Sweetheart kunyi landing lafiya?"
  "Lafiya, kinbar kukan haka ko?"
  "Ai zan soma sabo yanzu."
  "Yi hak'uri Princess banason ki samun little Princess d'ina a damuwa."
  "Shine ni ka tafi ka barni, akwai damuwan daya kai wannan ne?"
  "I'm sorry kinji? Zan dawo soon enough."
  "Wallahi gidan ba dad'i inba kai."
  "Ko zaki koma gun Mama ne toh?"
  "Nop no need mun kusa resuming school ai probably next week."
   "Oh god no! School ze sake stressing min ke out."
  "Toh ya muka iya?"
  "Allah bada sa'a okay? I love you rananda bakiya jin dad'i ba sekin fita lectures d'inba stay at home and rest."
  "Okay My Soldier zan fita gidan Lubiee, am I permitted?"
  "Ina kika kai kunneki d'azu da nake ta ce miki na baki izini kije duk inda kikeso just don't stay late at night?"
   "Ina ta kuka zaka barni ina kuwa na jika."
  "Uhm toh ni na baki izini kinji?"
  "Toh thank you, bari in shirya."
  "Toh ki gaishe min da mother in law na."
  "Toh Afrah zata ji bye, I love you."
  "I love you more" ya fad'a tare da hanging. Nan da nan ta shirya ta wuce gidan Lubiee, chan suka had'u da Omar ma inda suka ta hira kaman ba gobe se kusan Maghrib ta dawo gida.

   Life moved on, in a week time su Zeezee 'yan 300level suka koma school,  sosai ta miyar da hankalinta ga karatu, anytime she is less busy kuwa zata kira Al'ameen nata ko tayi mar video call suta hira. Baby'n su na nan cikin k'oshin lafiya sam bata wasa da appointements nata. Ahaka fa har sukayi spending 2 months apart nan Hajiyar ta soma matsawa Al'ameen da yaushe ze dawo at first k'arya ya mata yace zuwa next week ze shigo saboda besan ta ina ze soma sanar da Zeezee ba. Haka har satin ya cize be dawo ba nan ma ta sake kiransa harda 'yar k'wallarta, and again ya sake yi mata k'aryan in 5 days time ze dawo. Kuka ta fashe mar dashi ita she can't take it anymore she needs him, shikuma ya sanar da ita sauran masa 3weeks infact 4weeks saboda 'yan gun aikin nasa sun mai prolonging zaman nasa for a week more ya kasa. Da k'yar ya samu ya lalasheta ta yarda akan cewa in five days time d'in ze dawo.
   Al'ameen ya shiga damuwa sosai saboda besan kuma wani k'arya ze sake shiryawa Zeezee ba next time if she calls, he don't think he can keep on the pretense also, is better ya sanar da ita su yita ta k'are.

 _5 days later... exactly ranan da Al'ameen yace ze dawo._
  Sanin daman idan har ze shigo yana sanar da ita kokuwa idan beyi bama bayi wuce 3pm be dawo gida ba yasa Zeezee ta yafe lectures na ranan, even though ta tashi ba seti saboda leg cramps dake ta kamata kasancewar cikin nata yayi girma ba laifi getting to 6 months now. Hakan besa ta kwanta ba aiki sosai tayi ranan abinda ya kama kan shara, mopping, goge-goge sannan ta girka favorite na Al'ameen tuo da miyan ganye, tayi setting dining itama ta d'au wankanta tasa wata doguwar rigarta daya mugun amsan figure'nta da d'an k'aramin cikinta dake 6ullowa idan tasa loose kaya. Rabonsu da waya tun jiya, bata damu da kiransa ba saboda tasan mostly rananda ze dawo ba'a cika samun wayansa ba. Tun 2pm data idar da Sallah tayi zaune a parlour tana jiran dawowan Al'ameen sede shiru. Abu fa kaman wasa har 4:30pm Al'ameen be shigo ba by now kam tayi giving up tasan baze dawo ba he just tricked her daya ce mata ze dawo yau, toh why? Duda Tasan zargi zunubi ne kuma ba halin Al'ameen bane kula mata amman se raya mata shaitaan ke da Al'ameen ya fara cheating ne akanta. Time da zeyi tafiya yace 2 months zeyi, yazo yace ze k'ara sati yazo yace 5 days yanzu gashi yau d'inma ba alamansa. With this thought running on her mind kawai seta fara kuka a rayuwa bata son tayi sharing Al'ameen da wata, tasan its so selfish ta fad'i hakan amman she can't help it, tana sonsa fiye da tsammanin kowani d'an Adam. Wani sa'in har kishin 'yan uwansa Aysha da Salmah ma take ganin how they are free with him, barin Aysha dake auta har cinyansa tana d'alewa to talk more of side cheeks she can't handle them. Kuka ta shiga yi sosai tana shessheqa, in the process wayanta dake gefen ta ya shiga ruri kaman karta duba don haushi amman ta dage ta leqa gani tayi Al'ameen na kira.

   Shima tun safe ya kasa samun peace of mind, ko aiki ya kasa fita yau saboda beyi fulfilling promise daya d'au wa Princess tasa ba, yasan sarai she is mad shiyasa tak'i kiransa har yanzu thats why yayi calling nata instead. Tana ganin call d'in har ya tsinke bata d'aga ba, video call next ya shiga yi mata nan shima tak'i d'agawa, again ya shiga calling nata wanda in the process ta kashe wayar nata kwata-kwata. Nan fa hankalin Al'ameen ya sake tashi, guards nasa biyu da ya bar mata a gida ya kira ya buk'ace sa daya kai wa Zeezee wayar. Tana zaune kan kujera ta since d'aurin data sha ta ajiye a gefe se kuka take shark'af shark'af ta jiyo knocking. Sanda ta share hawayenta ta tambaya.
  "Waye ne?"
   "Sadiq ne Madam."
  "Lafiya?" Tayi maganan tana clearing voice nata.
  "Uhhm Madam please ki bud'e." A hankali ta mik'e ta bud'e mishi k'ofan. "Lafiya?" Ta sake tambaya. Wayansa yake miqa mata "Boss ne ya kirani yace in had'aku ta nan gashi yana kan wayan." Duk anan Al'ameen na sauraronsu.
   "Princess yi hak'uri ki amshi wayan kinji?" Ya fad'a cikin zazzak'ar muryansa me narkar wa Zeezee da zuciya ta speaker phone. Shiru tayi wane me nazarin abu.
   "Princess? Am sorry yi hak'uri ki kar6a kinji?" Ganin bata ko motsa ba and bata da niyyan hakan Sadiq yace, "please ki kar6a Madam Boss is so worried." Kallonsa tayi sannan ta miyar da k'ofanta ta rufe. Me kuma Al'ameen ze sake ce mata bayan evidence sun nuna he is cheating on her. D'aki ta wuce ta cigaba da kuka abinta hannunta rik'e da cikinta.
   "Am sorry Sir, ta rufe k'ofan she is not ready to talk."
  "Its okay Sadeeq thank you."
  "No please don't thank me again Sir, its my job."
  "Good" ya fad'a tare da katse wayan. Yau ina zesa kansa? Tunda yake Zeezee bata ta6a yimai fushi kaman na yau ba meke faruwa haka? Shi da yasani da tun da a baya ya yi maning up ya sanar da ita actual batun but he was afraid kar gabanta ya fad'i abu ya samu baby'nsu.
    Bacci ne yayi awon gaba da Zeezee se Maghrib ta tashi tayi Sallah har anan tak'i kunna wayar tata shiko Al'ameen yini ranan yayi yana trying numbers nata and duk basu shiga haka ya kasa bacci ranan. Ace for a whole day beji muryan Princess tasa ba be kuma sata a ido ba ai wannan k'anin mutuwa ne. Apology messages yata tura mata wanda se a washegari da ta kunna wayar ne ta gansu still bayan ta karance su bata ji ta sauk'o ba da abinda Al'ameen ya mata. Taya zeta wasa mata da hankali haka? Idan har budurwarsa tacan ne ta ke rik'esa he could have simply told her akan wasa da hankalin daya ta mata. Wayan na a hannunta Al'ameen ya shiga kira nan ma tana gani tak'i d'agawa. Yayi mata missed calls bil adadi da text messages yana pleading nata da tayi hak'uri ta d'aga he is so sorry and damn missing her sweet voice. Seda ta gama basa wuya sannan ta d'aga wayan tare da yin shiru.

   "Thanks Gee! Thank you for picking up Princess." Shiru tayi bata amsa ba, "Princess you there?" ya tambaya jin shiru.
   "Ina kwana?" ta gaishesa briefly.
  "Princess please kiyi hak'uri and let me explain banason inga kina fushi dani haka ko bacci na kasa yi jiya I've been thinking about you the whole night."
  "Me kayimin kake bani hak'uri haka? Ni nace kamin wani abu ne? I didn't."
  "Come on Princess, ni kaina nasan me laifi ne ni shiyasa nake son in baki hak'uri da ki yafe min, I'm sorry."
   "Laifin me kamin Ya Al'ameen?"
  "Yau ko Sweetheart babu, Oh God Princess am sorry please."
   "Ni wai nace kamin laifi ne?"
  "Baki fad'a ba amman ni nasan na miki, Princess bawai ina yaudarar ki bane ko wani abu, I just didn't want to tell you saboda gudun abinda ze haifar. Ba a banza 'yan office d'ina suka k'aramin 2 weeks d'incan ba, seda suka min prolonging zama na har na zuwa 3 months and I accepted it saboda I thought you were sick lokacin, yanzu kuma sun k'ara min 1 week again akai probably in 3 weeks time zan shigo in shaa Allah kiyi hak'uri please."
   "All these and you didn't tell me Ya Al'ameen? Taya kakeso in yarda yanzu? I asked you at first kace min a'a se yanzu kuma kake jeromin wannan bayanan? It would have been better idan fili kafito kace min akwai wacce ke rik'e ka a chan akan wasa da hankalin da kake tayi min, I was sick yestarday, leg cramps ke damuna sosai amman na tashi ba kalan aiki da girkin da ban maka ba duk ya tashi a iska, kasan ba tahowa zakayi ba why messing with my brain and making me look like an idiot, tell me taya bazan ji haushi ba Ya Al'ameen?"
  "Yaaa Salam! Princess wani irin magana kuma kike haka yau? I am sorry please."
   "Thats what your actions are telling me Ya Al'ameen sau nawa kake ce min zak shigo amman har yau shiru, idan ba rik'e ka wata take ba explain the reason for all these lies."
  "Princess I can't stop you from imagining and thinking of whatsoever kikeso saboda you have every single right to but ki sani wallahi I am not cheating on you, I will never cheat on you. Inada perfect wife why will I search for a better one? Its not possible. I love only you Princess and no one else and am sorry for lying to you all these times, banida enough courage da zan sanar dake ne da nayi a long time ago kiyi hak'uri please, I'm sorry and I love you so much." Kasa cewa komi tayi saboda yadda kalamunsa suke melting mata heart. Meyasa tayi judging nasa da sauri haka? Gaskiya ne Al'ameen baze ta6a cheating akanta ba amman kuma meyasa zuciyar ta takasa yarda da hakan har yanzu?
   "I'm sorry also" kad'ai ta iya cewa dashi.
  "You are still mad I can sense that, just know that I'll never give up har se kinyi believing d'ina I love you morethan I do love myself."
  Nan ma "thank you" zallah tace dashi. Ba k'aramin damunsa I don't care short responds nata suke ba.
   "Ya k'arfin jiki?"
  "Alhamdulillah." Ko ya aiki tak'i tambayarsa.
   "How's my Little Princess?"
   "She's fine." So yake ya sata surutu amman se basar dashi take, da a da ne cewa zatayi ba Princess bace Soldier ne, he miss her being herself.
  "school fah?"
  "Muna tests ma."
  "Wow really? Not so fast, Allah ya taimaka ya bada sa'a I love you."
  "Ameen thank you zanyi karatu se anjima."
  "Toh Princess, I love you."
  "Aha bye" tana kaiwa nan ta katse wayar.

   Daren ranan Al'ameen ya kasa bacci se tunanin Zeezee yake besan ya zeyi ba  ya gyara tsakaninsu yasan koda ze had'a sama da k'asa 'yan office nasa baza su barsa ya koma gida ba. Haka nan tun daga ranan idan ba wai Al'ameen neba ya kira Zeezee ita bata d'aukan waya ta kirasa. She is damn missing him har wani rashin lafiya rashin sa ke sata but she can't help it ta kasa gane dalilin da zesa yayi ta mata k'arerayin da ya mata, meya miyar da ita? Doll baby? koda tace zatayi believing abinda ya fad'a mata seta kasa. Sunyi haka na two more weeks Al'ameen da k'yar ya samu ya kar6a break bayan k'aryan daya musu na cewa matarsa batada lafiya nan ma one week break kad'ai ya samu da k'yar. Sam be sanar da Zeezee ba yanason suprising nata. A ranan da ze taho da safe ya kirata dan su gaisa. Seda call d'in ya kusa yankewa ta d'aga "hello Ya Al'ameen?"
  "Na'am My Princess ina kwana?"
  "Ina kwana Ya Al'ameen?"
  "Lafiya ya kike? Ya Little Princess d'ina?"
  "We are all good."
  "Leg cramps sun dena?"
  "Da sauk'i yau."
  "I miss you Princess, I miss your crazy talks, your smile I miss everything, I promise to make it up to you."
   "Uhm ya aiki?"
  "Na gaji da shi I want to come back to my Princesses."
   "Ina d'an aiki kad'an will call you up later." Zaune take a d'aki tana buga candy crush amman take cewa tana aiki.
  "Princess haka kike avoiding d'ina yanzu?"
  "Ba avoiding naka bane inason in k'are aikin da naken ne, ga baby se kicking yake gabad'aya ya dameni."
  "Awcch! Sorry Princess, just some months to go finally zamuyi meeting Little Princess namu."
  "Allah ya kaimu."
  "Ameen Habibtee."
  "So sena kira ka anjiman."
  "I love you so much."
  "I know se anjima" tana kaiwa nan ta katse.

  Cikin d'an k'ank'anin lokaci hadari ya had'e a garin Abuja gashi dai-dai time na flight na Al'ameen kenan noway jirgi ze iya tashi. Driver'nsa dake Abuja yayi wa magana akan ya taho zasu tafi by land. Driver ya rasa why Al'ameen is so desperate haka, mostly rananda wheather bashida kyau yana fasa tafiyan amman wannan karan ba yadda beyi da Al'ameen ba yak'i jinsa. Haka suka d'au hanya wajajen k'arfe hud'u su Al'ameen suka shigo su garin Bauchi.

*****4:30pm Zeezee na zaune a parlour ta baza agwalu6a a gabanta se sha take da book akan cinyarta tana karatu ta jiyo rurin wayarta. Ganin Al'ameen taji kaman ma kar ta d'aga har yanzu bata hushe ba ita, sanda ya kusan tsinkewa tayi picking up "hello Ya Al'ameen?" Jin different voice from na Al'ameen ya sata cikin duhu.
    "Please ina magana da matar me wayan nan ne?" Ba k'aramin rud'ani ba question na mutumin ya jefata.
  "E... eh itace matarsa ce."
   "Toh Madam please ki kwantar da hankalinki ki taho Teaching Hospital yanzu."
       "Teaching hospital?" Ta zabura tana zaro ido a yayinda cikinta yake mugun d'aukan ruwa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Teaching hospital? Meya same sa please? Teaching hospital na wani gari?" Take ta shiga zubda hawaye.
   "Na nan garin Bauchi."
  "Bauchi? Ba a Abuja yake ba? Bawan Allah anya kuwa ka gane da wayan wa kake magana? Ya Al'ameen miji na fa a Abuja yake ba a Bauchi ba."
    "A hanyarsu na tahowa Bauchi yau ko ince bayan shigowansu Bauchi a bayan gari armed robbers suka yi attacking nasa da driver'nsa. Shi mijin naki sun har6esa-"
   "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fad'a tare da katse sa, "Ya Al'ameen!" Tasa wani irin d'ankaren ihu na bakin gate na iya jiyota. Kawai ji tayi jini na bin k'afafunta tsabagen kalan tashin hankali da tsan-tsan masifan data tsinci kanta a ciki. Se k'aran fad'uwan abu kukeji a k'asa rigijib! "Hello? Hello?" Mutumin ketayi amman ba response kasancewar sumewan da Zeezee tayi. Sakamakon ihun da tayi yasa Sadeeq shigowa don tabbatar da ko lafiya knocking ya tayi bisa k'ofan jin ba response kawai ya fad'a ciki nan ya samu Zeezee cikin pool of blood a sume. Da gudu yayi kanta tsoron ta6ata ma yake ganin he is running out of time yasa kawai ya cinci6eta se Teaching Hospital achan aka shiga bata taimakon gaggawa don stopping bleeding d'in before yayi affecting baby'n nata. Kafin nan kuma Sadeeq ya kira layin Al'ameen inda yata ringing ba a d'aga ba. Mota ya shiga ya wuce gidansu Zeezee inda yake sanar da Mama halin da ake ciki. Nan da nan tasa hijabinta suka fice kwata-kwata basuda labarin halin da Al'ameen yake ciki.

   _30 more minutes..._
   K'ofan d'akin da Zeezee ke ciki ne ya bud'u revealing a Dr da sauri Mama tayo kansa. "Dr how is she?"
   "Calm down Ma'am she is fine ki kwantar da hankalinki."
  "Alhamdulillah! Baby'n nata fah?"
  "Both the Mother and child are fine, mun samu munyi stopping bleeding d'in before it went any far yanzu ma zaki iya shiga ganinta."
  "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Thank you Dr Allah ya biyaku."
 "Ameen excuse me please." Bata kai da shiga cikin d'akin ba Sadiq ya iso gun yana gudu yana hak'i. "Hajiya! Hajiya" Chak ta tsaya tare da kewayowa.
  "Sadeeq lafiya?" Kai zallah yake kad'a mata "Hajiya I just received a call."
 




*MIEMIEBEE.       Team #YGC!🎀*
   *ZAIMEEN flames🔥🔥🔥*
Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄

1 comment:

Unknown said...

Wayyo ya Al-ameen Allah ya baka lfy.