Friday, 24 March 2017

‘YAR GATA CE!

      BY MIEMIEBEE
PAGE 70
  March 2017


   _Copying from me won't ever make you be ME, I'm me you are you. So why don't you just improve your skills and stick to being YOU? #WordsOfWisdom_




       Washegari Zeezee ta tashi garau sa6anin yadda ta saba tashi da zazza6i, hannun Al'ameen dake k'asan rigarta  ta zare a hankula sannan ta raba jikinta da nasa ta shiga bayi tayi brushing ta fice kitchen inda ta had'a musu had'ad'd'en breakfast daga nan ta d'ago tsinstiya ta shiga shara wanda in the process Al'ameen ya fito sanye da vest da shorts.

   "Princess?" Yayi maganan unbelievably.  "Me nake shirin gani haka? Me kikeyi?" A hankula ta d'ago kai tana kallonsa sannan tace, "shara nakeyi har ka tashi? Good morning Sauran wanka."
  "Shara? Da izinin waye?"
  "Sweetheart kaman ya da izinin waye kuma? Rabon gidan nan da shara since when? Yau kuma nad'anji sauk'i se bazan yi aiki ba?" K'arisowa gaban ta yayi da niyyan kar6an tsintsiyan wanda tuni ta 6oye a bayanta.
   "Bani." Ya fad'a in a serious tone. Kafad'a ta buga.
  "Princess bani."
 "O'o."
  "Am serious" ya mik'a hannu a bayanta don kar6e tsinstiyan nan ta shiga 6oyewa, da k'yar ya samu ya kar6e. "Ka bani mana Ya Al'ameen."
  "Nak'i."
  "Toh meh dalilin ka haka kakeson abar gidan da dotti? Jibi k'ura fah."
   "Za'a nemo me aiki tanayi ke bakiji abinda Mama tace bane?"
  "Naji amman ai shara bawani aiki neba meh wahala kuma ni wallahi banason me aiki."
  "Why?"
  "Saboda suna snatching wa mutane mazajensu, ni banaso."
  "LOL Princess ni yaushe ma nake zama a gari bale sumuki snatching d'ina?"
  "Oho nide banaso ka bani tsintsiyan nayi shara na kai kuma kaje kayi wanka."
   "Bazakiyi ba Princess am serious, me aiki za'a d'auko miki ke bakisan in the first trimester na pregnancy babu kyau mace tana yin aiki masu k'arfi ba? Saboda placentation be gama taking place ba har yanzu, pregnancy'n baida k'wari little abu yana iya jawo miscarriage, banason mu rasa little Princess namu." Murmushi tasa sosai a yayinda sonsa ke sake beating a heart nata "kai kuma yaushe ka zama Dr Sweetheart?"
   "LOL kina wasa da ni ko Princess? That aside kibar sharan zamu nemo me aiki."
  "Ni wallahi bana so."
  "Toh naji anytime masu aikin naki sukazo zan shiga d'aki se sun tafi in fito, okay?" Shiru tayi tana nazari. "Okay?"
  "Promise ko d'aukan ruwa bazaka  fito yiba."
  "LOL Princess I promise."
  "Toh shikenan."
  "Kinbar sharan?"
  "Sweetheart d'ina bayaso ba dole in bari ba." Ta amsa mai tana murmushi.

     "Thats My Baby Machine." Ya sanar da ita murmushi kwance fal a fuskarta.
  "Muje kayi wanka toh breakfast is ready."
   "Har yaushe kikayi setting dining table Princess? Banason kina wahalar da kanki da kuma little Princess d'ina."
   "Wahala kuma? You are My Only Soldier in banyi ma bauta ba mawa kake so inyi wa?"
   "Ni banason abinda ze gajiyar min dake ne all I need you to do is to rest."
   "Don't worry chips ne kawai kuma you keep on saying little Princess ni Little Soldier nakeson in haifa, exactly as you saboda koda kayi tafiya se yana keeping d'ina company."
  "Ni kuma little Princess nakeso ranan da kikayimin wannan zuciyan naki setana keeping d'ina company."
   "LOL ba kaine kake tafiya ka barni ba kaga dole in haifi little Soldier."
    "Nop Princess little Princess zaki haifa kuma zaki gani."
  "Nop" tayi sauri ta kad'a kai "I told you little Soldier zan haifa."
  "Hakane? toh lets bet."
  "lol Sweetheart kai zakayi loosing wallahi lets not even start."
  "See this Princess o telling me ni zanyi losing" yayi maganan yana janta jikinsa and finally wrapping his arms around her tiny waist a yayinda ta zagaye nata a wuyansa. "Ko kin manta ni nayi ajiyan achan? Nasan meh na ajiye kuma Princess na ajiye." Da murmushi d'auke a fuskarta tace, "no amman d-" her last word was crashed on his lips. A hankali yayi owning lips nata ya shiga kissing nata, sun d'au tsawon lokaci a haka sannan yayi breaking kiss d'in in a teasing manner. "Its a little Princess." Ya fad'a with no room left for arguement.
  "No problem ai munyi betting, idan har na haifi Little Soldier zaka bani izini inyi naming d'inshi after duk name daya min no questions, idan kuma vice-versa na mace na haifa kai zakayi naming nata after who ever you want I won't ask questions." Yana wasa da jelan gashinta da suka faffad'i bisa shoulders nata yace, "are you ready to lose?"
    "I am ready to win over My Soldier."
  "Good! Zamu ga toh."
  "Zamuga Little Soldier'n mu ba." Ta fad'a mockingly.
  "Princess zan..." sekuma yayi shiru.
   "Zakayi meh? You want me on bed with you?" Ta fad'a tana dariya sosai. Tsayuwa yayi yana adoring nata cause she have the most perfect smile, "you know I can do that anytime I wish to right?"
  "Ka manta meh Mama ta fad'a maka ne? Cewa tayi ka barni in huta."
  "Aww ma haka zaki ce koh?" Gira ta d'aga mai tana mai gwalo.
 
   "Bari in kira Saje yazo ya shirya min akwati na now now now ko da mota ne in wuce Abuja." Hannunsa ta cafke da wuri kafin ya juya "you are not doing that."
   "Zaki gani ai."
  "O'o" ta maraice fuska. "Wallahi wasa nake maka kasan I need you badly than how you need me ko a yanzu kakeso muje na yarda banda zancen tafiya please." Ganin yadda ta rud'e yasa shi dariya sosai har da rik'e ciki. "Eh ka samu mahaukaciya ba dole ai kayita mata dariya, bari little Soldier na ya iso kaga ko zan na damuwa da stay naka ma."
  "Haba! Princess" yayi cupping face nata, "you know right how much I love you, ba inda zani ina nan to watch over my little princess growing up in my Princess, I can't wait to see that baby bomb."
   "Ni kuma banaso" tayi maganan tare da had'e rai.
  "But why Princess?"
  "Saboda ka samu abin teasing d'ina ba kana neman tsokana na."
  "LOL Princess inji waye?"
 "Eh mana gashi tun yanzu ka soma yi, in ba haka ba mey abin kallo a baby bomb? Ni banaso."
  "Princess it'll suit you, ai kinada tsawo infact bomb d'in ma zebi tsawonki your tummy won't grow big."
  "Are you sure Sweetheart?"
  "Yes Darling Baby Machine."
 "Kasan mazajen yanzun nan da zaran sunga cikin matayensu yayi k'ato se su dena sonsu har kunya suke su ce wannan matarsu ce kum-" da sauri ya aza yatsansa bisa lips nata yace, "shhh!" tare da kad'a kai. "Don't ever say such a thing Princess, I am not that kind of men, I am Al'ameen Zainab's lucky husband, bazan ta6a tsanan kiba, I love you and its true." Yayi maganan tare da d'ago hannayenta yayi pecking kansu.
   "Awwwn! Sweetheart you are so sweet, I can't ask for a better husband when I've got the best. Allah ya bar mu tare ya k'ara mana dank'on soyayya, I know our love will never die."
  "Ameen Princess, it'll never because its true love."
  "Kaga se surutu muke zubawa bakayi wanka ba har yanzu muje muje kayi." Hannunsa ta kama har bayin ta rakasa sannan ta basa privacy. Kafin ya fito ta cire masa kayan da zesa ita ma ta sake gyara makeup nata. Cike da so da k'auna suka k'arisa dining suka karya, yau se surutu Zeezee ke tayi wa Al'ameen su ba sabon ba yau jiki da sauk'i.

***
  Haka kuma rayuwarsu ta cigaba da kasancewa, cikin tsan-tsan so da k'auna da kuma biyayya wa juna. Sanin kowa ne yadda Soldiers suke respecting matayensu. Gatan da Zeezee ke sha gun Al'ameen kam sede muce Allah kawo mana mazajen da zasu kula damu muma haka, ma'aurata kuma ya k'ara dank'on soyayya a tsakaninsu, AMEEN.

     Kusan 2 months Al'ameen yayi ma Zeezee, kula da Zeezee yake sosai, basu wasa da pre natal appointments nata, Zeezee can't ask for more!
    'Yan gun aikinsa kuwa sunka ishesa da lalle fa ya dawo aiki ya musu yawa they need him, gashi ma Zeezee needs him. Gashi nan cikin nata d'an kad'an ya 6ullo kai. Kullum Zeezee na gaban mirror tana dubawa she can't get enough of herself, she is now 3 months pregnant, ji take kaman ta jawo watan haihuwarta don tabawa Al'ameen family'n da he has always longed for.

 ******
   Zeezee na kwance rabi akan gado rabi jikin Al'ameen ta jiyo wayansa na ruri kasancewar baccin nata beyi nisa ba yasa takejin dukkanin abinda ake fad'a mai da kuma abinda shima yake fad'a a wayan. Hak'uri yake ta bawa manyan da suke kansan da su d'an k'ara mai hutun koda na 2 weeks ne amman sunk'i saboda they need him badly, Al'ameen is such a great warrior, soja ne me aiki da kuma k'uzari, bayi tsoro saboda haka they can't do without him. Ba kalan pleading nasu da beyi ba amman se hak'uri suke basa suna cewa ba yadda suka iya ne suma yayi hak'uri haka shima he is left with no option dole yabar Zainab tasa. Yana katse wayar ya miyar da hannunsa kan k'aramin cikin Zeezee yana tunanin ya zeyi ya tafi ya barta. Ba Zeezee kad'ai ba yanzu, shi kansa Al'ameen he is addicted to her saboda a kullum suna tare befi a sati su fita sau biyu ko uku ba nan ma sede gida gun Mama ko asibiti sam baya son tafiya shima yanzu yafi son yayita ganin Little Princess tasa tana girma a idonsa, he can't tell just how much he loves Zeezee.

   Zeezee data jiyo komi a waya tace a ranta wallahi baza ku tafi min da Sweetheart ba. Plan ta had'a abinta, seda ta bari Maghrib yayi Al'ameen yazo tashinta Sallah sannan ta langwa6e tana wani abu sime-sime tana ishh! ashhh! washhh! ita bata jin dad'i bata da lafiya.
   "Princess are you okay?"
   "Ya Al'ameen am not" tayi maganan tamkar zatayi kuka.
   "Oh God! Meya sameki? Meke damunki? Ina ke miki ciwo?" Cikinta tayi pointing "nan."
   "Little Princess d'ina ne take damunki?" Kai ta gyad'a cike da shagwa6a "harda baya na ma" tayi adding.
  "Sorry Baby Machine, me kikeso toh yanzu? Muje asibiti?"
   "Arrghhh! Cikina Ya Al'ameen do something please." Gabad'aya ya kid'ime yama manta da sallan dake kansa. "Ina... inaaa waya na?" Ya shiga i'ina.
  "Dr zaka kira?"
  "Eh ta duba min ke sannu."
  "Ni o'o banason Dr ni kai nakeso."
  "Toh Princess ya kikeson inyi? Am not a Dr."
  "Arrggh! Baya na!" ta sake sa wani ihun. "Omi'god am so sorry kinji? Yi hak'uri ki bari in kira Dr."
  "Ni kar ka kira Dr."
  "But why Princess?"
  "Ni banaso kawai stay with me in muna tare ina jin rashin lafiyana na d'aukewa. You are the remedy to all of my sicknesses." Murmushi ya sakar mata me sake kwantar da hankali.
  "I love you Princess and am here for you, Sallah fa? Zaki iya tashi?"
  "Eh tayani in tashi."
  "Zaki iya? Are you sure?" Kai zallah ta gyad'a mishi sannan ya kaita har bayin tace mishi she can manage from here. Gabad'aya hankalin bawan Allah ya tashi besan duk set up na Zeezee bane. Tana ganin ficewansa daga bayin ta sharo k'wallanta tana murmusawa sosai "ai wallahi ko sunfi mamannin su k'ok'ari se sun bar min kai ka k'ara koda sati biyu ne ko d'aya, iskanci kawai." Nan da nan ta d'auro alwala ta fito daga bayin ma tak'i kira ta sa mishi chak yazo ya d'auketa ya direta kan sallayan daya shimfid'a mata tare da sanya mata hijabin.
  "Zaki iya yin Sallan a tsaye ko zakiyi a zaune?"
  "Zan iya kar ka damu, Matar Soldier cefa ni."
    "Thats my superwoman I love you."
  "I love you more and more, muyi sauri ciki na." Nan da nan ya jasu sallah cikin nitsuwa, tattalin Zeezee yatayi yinin ranan ya ma kasa sanar da ita ya kusa komawa Abj ganin condition da ta shiga gashi da zaran yace ze kira Dr Sammy seta ce ita bataso. Tabi ta tada mishi hankali har ya rasa nayi, ya had'a mata tea tace bata so, custards, oaths duka tak'i sha idan yana kallonta tayita matso k'wallan tsiya da zaran ya juya tasa dariya ciki-ciki. Kiran 'Yan office nasu back Al'ameen yayi inda ya musu stating critical condition da Zeezee ke ciki, ya kuma rok'esu da don Allah su d'an k'ara masa hutun koda sati biyu ne. Sun ka ko amince amman da sharad'in idan ya dawo aiki se ya musu 2-3 months tukuna ya koma, ba yadda ya iya hakan ya yarda. Suna gama wayan ya dawo d'akin nasu, nan fa pretender ta soma awwch da washhh. K'arisosa gabanta yayi ya zauna fuskarsa d'auke da damuwa, a rayuwa baya son abinda ze ta6a masa Princess nasa. "How are you feeling Princess? Har yanzu little Princess na damunki?"

   Ita kanta ya bata tausayi ganin yadda hankalinsa ya tashi matuk'a amman ya ta iya? She have to keep on the pretense idan ba haka ba seyace ze koma Abj dan ita bata ma san yayi waya da 'yan office nasan ba yanzu.
   "Har yanzu Sweetheart."
  "Sannu kinji? Kiyi hak'uri gobe muje asibiti ni bansan me zan sake miki ba, an not good in this only if I can take away your pain." Hannunta ta zaro daga bargon da take lullu6e dashi tare da rik'e hannun Al'ameen cikin nata tana murzawa soothingly.
   "I love you this way Sweetheart, I love you for who you are, thanks for staying with me."
   "I owe the pleasure Princess, zaki sha koda black tea? Karki ce no kinji yi hak'uri kar Little Princess namu tayi starving."
  "Toh ka had'a min zan sha." Ta sanar dashi face nata d'auke da smile. Dad'i sosai yaji wanda ya kasa 6oyewa don kuwa tun safe suke abu d'aya. "Ina zuwa kinji?" Ya fad'a tare da pecking forehead nata. "Wait Sweetheart yanzu this week d'in zaka koma aiki ka barni ni kad'ai?" ta k'are maganan wane zatayi kuka wearing a most sad face

   "Shhh! Don't cry Princess taya zan tafi in barki a wannan condition? Kema kinsan its not possible. Na rok'esu da k'yar suka k'ara min sati biyu."
  "Sati biyu!" Tayi exclaiming cike da murna harda mik'ewa zaune tayi watsi da bargon da take lullu6e dashin, tama manta tana faking rashin lafiya tsan-tsan farin ciki. Ido da baki wangalau Al'ameen ya bud'e ya tsaya kallonta da mamaki itan da tace ko k'arfin d'aga jikinta batada saboda yadda take jin zazza6i amman kuma shine ta daka wannan tsalle? Ganin fa yana iya gano faking rashin lafiyar take daga yadda yake ta kallonta yasa ta d'an rigingina da gadon tana ta6a kan cikinta "d'an ihun danayin nan yasa bayana ciwo Sweetheart kawai naji dad'i ne bazaka tafi ba se in 2 weeks time. I love you."
   "I love you more My Baby Machine." Ya fad'a still checking her, anya kuwa? Ya tambayi kansa "bari in had'o miki tea'n ina zuwa." Yana mik'ewa Zeezee  tasa murmushi k'us-k'us tana me jin dad'in Al'ameen baze tafi ba ya barta ba har da wani YES! nata irin mission accomplished d'innan. Shiko har ya juya se kuma ya sake turning back to her ba shiri don tambayarta koya sa mata madara ne a tea'n ko bak'i takeso.
    Nan fa ya kama Hajiyar red handed tana dariya bama murmushi ba wanda tuni ta tsuke fuska ganinsa amman inaaa ya riga ya gan ta.

    "Princess?" Da wuri ta sauk'e idanunta a k'asa. Komawa yayi ya zauna gefenta "Princess?"
  "Na'am" ta amsa not looking at him.
  "Look at me." Da wuri ta kad'a kanta.
   "Kuma murmushin me kike? Princess anya kuwa?"
  "Anya meh?" Finally ta d'ago kanta tana kallonsa.
  "Anya ba faking rashin lafiyar nan kike ba Princess?"
  "Kaman ya Sweetheart? Dan ba kai keda cikin ba ai dole kace faking nakeyi, ni kad'ai nasan abinda baby'n ka kemin." Ta qare maganan tana zum6uro baki.
  "In haka ne toh dariyan me kikeyi? Wanda bashida lafiya yana dariya ne? Kuma ina juyawa kika sake fuskar."
   "Haaa'a! Ni murmushi nayi ba dariya ba. Yanzu ma murmushi ban isa inyi ba Sweetheart shikenan ya zama abin magana akai?"
  "Yanzu Princess kina kallon cikin idona kina min k'arya koh?" Sekuma taji ta kariya. "Nifa ba k'arya nake ba."
  "Ga jikinki ma ba zafi."
  "Alright alright naji ka kamani ina maka k'arya I'm sorry, I just can't help it and wannan plan d'inne kawai solution gashi yanzu sun k'ara maka hutun sati biyu ai, it worked!" Da mamaki ya tsaya kallonta har tayi fooling nashi haka be gane ba? Lallai kuwa ta fisa wayo, "so duk kuka-kuka da su awch da wash na d'azunnan duk k'arya ne?" Kai ta gyad'a mar a hankali "am sorry."
   "Haba! Princess kinsan yadda hankalina ya tashi kuwa?"
   "I'm sorry Sweetheart but kaima inda kaine a shoes d'ina you'll do exactly the same thing bana son ka tafi, I want you by my side."
   "Yanzu kenan duk sharri kikayi ta wa Little Princess d'ina?"
   "Ba Princess bace, Soldier ne kuma nasan ze yafe min kaman yadda Daddy'nsa ya riga ya yafemin ko?" Tayi maganan cike da shagwa6a.
    "Am very mad Princess." Hannunsa ta kama ta had'a da nata tana murzawa soothingly, "Sweetheart please don't be I'm sorry."
   "Kinsan yadda hankalina ya tashi kuwa? Ban nuna miki bane fa kawai, har kai na sanda yamin ciwo bana son ganinki ba lafiya."
  "I'm sorry Sweetheart please forgive me, I couldn't think of a better plan shiyasa, ka gane mana bana son ka tafi ka barni ne."
  "Uhmm" zalla yace.
   "Baka hak'ura ba har yanzu?" Hannun nasa ta sake ta kama kunnuwanta both "I'm sorry My Soldier I won't do it again, please." Kallonta yayi na 'yan seconds sannan ya miqa hannunsa ya sauk'e hannayen nata. "Promise?"
  "I cross my heart."
   "Toh na hak'ura."
  "Thats My King!" Ta fad'a tare da shigewa jikinsa tana hugging nasa, shima hugging nata yayi back yana shafa bayanta a hankali, "but my plan worked atleast you are staying with me for the next two weeks, it isn't bad or is it?"
   It is yake son ce mata dan kuwa idan ya tafi yanzu bai sake zagayowa se nanda 3 months, tafiyan da be ta6a yi ba zeyi wannan karan. Yasan idan har ya sanar da ita akwai tashin hankali.
    "Is it?" Ta sake tambayarsa jin shiru. Breaking hug d'in yayi tare da cupping face nata "it is not Princess actually nima ba son tafiyan nake ba, we get to spend two more weeks together." Hannunta ta aza akan nasa dake rik'e da fuskarta tana shafawa a hankali.
 
   "I love you My Soldier, gani nake like bazan iya rayuwa ba idan ba kai, na gommaci in rasa komi a duniyan nan harta rai na da akan in rasa ka, banida burin da yafi inga muna tare kuma ina sanya ka farin ciki. I love you eternally." Kissing lips nata yayi lightly but with so much emotions, assuring  her he is with her forever. A hankali yayi pulling out, "I love you more Zainab, for all my life ke kad'ai ce macen dana ta6a so. Despite all the different types women I met during my time in school, despite all those Mama introduced to me, duk cikinsu ba wacce ta ta6a yimin, but ke? For the first time that I set my eyes on you Zainab, my heart skyrocketed, alokaci guda naji ina sonki even though I've never experienced love I know it was love, alokacin banida burin da yafi in mallekeki and make you happy-"
   Katsesa da wuri tayi sounding disappointed "and a lokacin I failed to see you for who you are, I was dense and stupid and blinded by Adeel's playful love na kasa baka chance."
   "Don't talk like that Princess, here we are together today ready to die for each other, it is all that matters right?" A hankali ta gyad'a mishi kai, "I love you Habeebi kasan haka Fannah ke kiran Anas wani love story dana karanta and sunan yamin dad'i sosai."
   "I love you more Habibtee, bari in had'o miki tean."
   "Muje mu had'a lunch tunda ba rashin lafiya again."
   "LOL pretender kawai, You sure about this?"
  "Yes Sweetheart." Hannunsa ya miqa mata tasa nata ciki sannan ya mik'ar da ita a hankali suka fice kitchen. Macaroni me rai da lafiya suka girka da minced meat all over se k'amshin girki ke tashi a gidan. Atare suka ci abincin sannan suka fito waje gun garden suka zauna suna shan iska kamin Maghrib ya shiga.






*MIEMIEBEE.        Team #YGC🎀*
   Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄

1 comment:

Unknown said...

Tnx MIEMIEBEE, Allah ya kara basira.