Wednesday, 29 March 2017

‘YAR GATA CE!

*BY MIEMIEBEE*
 Page 79
 March, 2017


****
      Life moved on drawing us closer to our graves, Khaleefah se dad'a girma da wayo yake ga uban k'iriniya be bar komi ba a halin Zeezee, itako sanin ILLAN GATA yasa bata cika biye mai ba, sau dayawa idan yaga abu gun yara ya hau kuka yana shessheqa shima se an siya mishi, atimes tana siya mai wani sa'in kuma tak'i saboda bata son 6ata sa ya zamanto duk wani abinda yake so yana samu hakan ba gata bane, shide Al'ameen ko uffan bayi ce mata when it comes to tarbiyya saboda yasan uwa aka sani da bada tarbiyya baze sa baki ba yayi ruining tarbiyyan yaransa. Duk wani tafiyan Al'ameen kuwa kamin ya dawo se Khaleefah ya manta dashi yayi ta masa k'uiya se a hankali tukuna yake sake sabawa dashi. Cikin ikon Allah har Khaleefah ya cika one year old, nan ma grand birthday Zeezee da Al'ameen suka yi masa organising fiye dana lokacinda ya cika 6 months had'ewa. Yaro kyau wane d'an larabawa. Kayan wasan da Al'ameen yayi gifting masa as present ranan ita kanta Zeezee tasha mamaki mota guda aka sauk'e na kayan wasan Khaleefah. Haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa cikin so da k'auna. Ba kad'an ba Al'ameen ke ji da Khaleefah kayakin wasan yaro ya cika d'akinsa ya cika store room.

      A haka har Zeezee ta soma service nata ta k'are lafiya, koda Al'ameen ya tambayeta a nemo mata aiki kuwa cewa tayi bata so, daya tambayi dalili kuwa tace masa tunda ba lecturing ko wani aikin asibiti zatayi da ze taimaki al'umma ba bata ga amfanin aikin ba, daman inba don taimakon al'umma ba don samun kud'i ake aiki, ita kuwa bata da maraba da masu aikin ma ko tace tama fi wasun su samu cause kud'in da Al'ameen ke bata don yawa save kawai ta bud'e tana ajiye musu for future use. Idan ya tashi na abincin Khaleefa kawai se ya ajiye 20-30k.
     Amsan Zeezee ba k'aramin dad'i yayi wa Al'ameen ba especially the part that tace she'll be his full house wife. A kullum tana tare da Khaleefanta idan Al'ameen bai gari yau su fita nan gobe su fita chan wataran kuma su yini suta wasa kawai a gida. Sosai Khaleefah ke neman tasowa da gagara amman kasancewar Zeezee na taka mishi birki yasa yake rage wasu abun amman fah har yanzu tana fama dashi kunsan shi gado ba gwaninta bane.  Sau dayawa yana lalata mata waya da miyau, idan ta bashi na wasa kuma yak'i amsa se na gaske.

   ****
   Khaleefah nada one year seven months, dare d'aya Zeezee ta soma feeling nauseatic, ga kuma fever da take ji again gabad'aya de ta tashi ba seti ranan. Gashi Khaleefah ya ringa yi mata wasa kaman d'an biri kenan ya hau kanta tanan ya sauk'a ta can. Haka yanzu ma tana kwance akan gado bata jin dad'i shiko yana zaune akan bayanta yana doki, chan yaga haske na flashing akan screen na wayan Zeezee hoton Al'ameen daya bayyana as identity na wanda ke kira yasa Khaleefah riding faster akan Zeezee yana "Da da" Da da! Da da!" Kaman yadda yake kiran Al'ameen.
   "Da da ne yake kira?" Ta tambayeshi idonta a kulle. "Da da!" Ya cigaba da kira har seda Zeezee tayi picking up call d'in nan fa ya nitsu yana kallonta.
   "Mamin Khaleefah My Princess."
  "Na'am Da dan Khaleefah My Last Standing Soldier." Ta fad'a da k'yar don jirin da takeji.
   "Princess is something wrong? Yana ji muryan ki so low? Are you okay?"
  "I am karka damu."
  "Kin manta munyi promising juna baza mu sake yiwa juna k'arya ba ko?"
  "Am sorry."
  "Tell me toh." Ta bud'e baki zatayi mai stating bata jin dad'i kenan taga tabargazan da Khaleefah yayi mata da pillow, wannan hak'waran nasa sunfi razor ci. Pillow ya yaga da teeth nasa ya ciro abin cikin yana watsi dasu one-by-one. Seta tuna ranan da ya gantsara mata cizo a bakin nono, har kwad'e sa seda tayi ranan Al'ameen yayita mata masifa. "Haba! Haba! Haba! Baby mesa kake min destroying komi na ne? Haka jiya ka yage bedsheet d'in nan I had to change it yau kuma pillow na ka tsaga haka?" Dariya Al'ameen dake jinta ya saki a yayinda Khaleefah ya tsaya yana yi mata murmushi har yau dan tsiya bayi kiranta da komi amman tuni yabawa Al'ameen suna, ko pic nasa ya gani ya hau kiran 'Da da! Da da!' Kenan to her ultimate suprise taji yau yace, "Mammy."
  Ido ta zaro in disbelief "say it again Darling, say Mammy again" gabad'aya ta nemi rashin lafiyar nata ta rasa ma tsabagen farin ciki. For how long have she been waiting for this day? "Say it again kaji Cuddle Bear? Say Mammy" duk ana sauraronsu Al'ameen ke dake Zeezee tasa a speaker phone. Shiru Khaleefah yayi ya had'e rai kaman ba shi ne yayi magana just a while ago.
  "Come on say it! Zan baka mama" ta yaye sa amman take son ta zolayesa. Ba surutun da batayi ba ya sake cewa 'Mammy' yak'i.
   "Yak'i fad'a Sweetheart" ta sanar da Al'ameen sounding disappointed.
   "Se hak'uri Princess" ya fad'a mockingly yana yi mata dariya.
  "Ka cigaba idan na haifo little Princess d'ina seta soma kirana kamin kai."
  "Time shall tell."
  "Mammy!" Cewar Khaleefah da k'arfi again.
   "Ya sake kirana ya sake!" D'agasa sama tayi tana juyi dashi "say it again kaji Sweetheart?"
  "Mammy." Dad'i kashe Zeezee yau finally Khaleefah ya bata name itama ko Al'ameen ze rage mata wani abin yanzu ada cewa yake wai sam Khaleefah baya sonta se shi don kawai yaga yaro ya basa suna gaba da ita.

   Seda ta gama wasa wa Khaleefah gabad'aya ya gajar da ita lik'is gashi daman ba dad'i take jiba ta dawo kan Al'ameen. "Ina Khaleefah?" Ya tambayeta.
    "Yayi pupu Baaba zata wanke mishi."
  "Oh!"
  "Yes seka nemi wani abin teasing d'ina yanzu tunda de Khaleefah ya bani suna, sunan da yafi naka ma dad'i."
   "See this Princess of mine, meye a cikin Mammy? What a common name amman Da da fa ina kika ta6ajin yara na kiran Daddy'nsu da Da da? Se Khaleefah kad'ai."
  "Oho de Mamy yafi dad'i meh Da da sekace Dada na fulani."
  "LOL ai ba hausa pronounciation bane Da Da not Dada."
  "Whatever, Khaleefah ya gajar dani yau d'innan gashi dama bada seti na tashi ba ya office?"
  "Office alhamdulillah meke damunki?"
  "Wallahi zazza6i-zazza6i nakeji."
  "Subhanallah kije asibiti mana gobe ba kyau zama da rashin lafiya."
  "Eh zanje in shaa Allah don tun shekaran jiya yake damuna se worsening kuma yake."
  "Sannu kinji? Get some rest I love you."
  "I love you more, send my kisses to Khaleefah tell him Da da loves him so much."
  "I'll sleep like a baby and dreams about me."
  "Definately and you too good night."
  "Aha night" nan ta katse. Bada jimawa ba Baaba ta kawo Khaleefah da diaper nasa a hannunta tun d'azu ya bari ta sa mishi yak'i seta kwantar da shi zata sa mai seya miqe ya sa gudu. "Mamin Khaleefah ga Khaleefah nan tun d'azu yak'i a sai mai pampers."
  "Ke kuma meye a fuskanki haka Baaba?" Shafe fuskar nata tayi taga farin powder kota ina. "Na shiga uku Khaleefah ne ya fesa min." D'an murmushi Zeezee ta saki "Sweetheart kana son kasha bulala ko?"
  "Mammy" ya fad'a sounding delighted yana miqa mata hannu ta kar6esa. Miqewa tayi da k'yar ta amshe sa, "ki had'a min frisco na shi please yasha yanzun nan yayi bacci ko zan huta nima."

^^^^^
    Washegari da safe Zeezee ta shirya ta shirya Khaleefah suka wuce asibiti. Da mamaki ta tsaya tana kallon likitar data ce mata zatayi mata pregnancy test like how can she get pregnant when Khaleefah is not even upto two years? Fargaba tashiga sosai, yanzu inhar cikin ne da ita meye Al'ameen zece mata akuya kome? Koda Dr ta miqo mata result d'in kasa bud'ewa tayi seda Dr'n da kanta ta d'aga ta bud'e "kamar yadda na fad'a" tayi maganan tana murmushi. "Mr Handsome ya zama big bro your little sister or brother is on board, congratulations Ma'am."
   "Dr taya hakan ze faru? Ina kan planning fah Khaleefah is just 1 year 7 months old kuma kice ina da wani cikin yanzu?"
  "Ai faruwan hakan shi yafi yawa, arziki Allah ya kawo miki Hajiya kinga be kamata kice tayaya ba."
  "Hakane kam nagode."
  "Yauwa saura scanning ko?" Ma wata nurse Zeezee ta miqa Khaleefah da k'yar suka samu ya yarda ta kar6e shi sannan aka yo mata scanning aka gano cikin d'an d'aya ne nanma d'auke da ita which is just 3 weeks old. Maguna d'aya zuwa biyu aka rubuta mata sannan aka bata next appointment nata. Ita gabad'aya Zeezee hankalinta ya tashi inta itane she is fine with it amman tunanin ya zata soma 6ullowa Al'ameen da wannan zance take ya ze d'au maganar? Sun isa gida bada jimawa ba ya kirata don jin ya jikin nata.
  "Alhamdulillah da sauk'i."
  "Kin samu kin je asibitin?"
  "Eh yanzu dawowa na."
  "I hope ba wani abu serious bane?"
  "Yaushe zaka shigo?"
  "Princess!"
  "Na'am."
 "Meke damunki?"
  "Babu in ka dawo zan sanar da kai ba maganan waya bane."
  "Ya Salam mesa kikeson tsinka min zuciya ne Princess? Meke damunki please?"
  "Seriously idan ka shigo zan sanar da kai, se yaushe kenan?"
  "This week zan shigo."
  "Toh seka shigo."
  "Princess please promise me ba abinda ya sameki."
  "Wallahi babu am perfectly fine kaide seka shigo kawai, I love you okay?"
  "I love you more ki shafa min kan Khaleefah zuwa anjima zan miki facetime video call ki had'ani dashi."
  "Toh Da dan Khaleefah bye."

   Zeezee ta kasa sanar da kowa labarin wannan k'aruwa da ta samu don tunanin k'aramar k'wak'walwa irin tata wai gani take za'ayi mata dariya idan tace tanada wani cikin yanzu bayan gashi ko shekara biyu Khaleefah be cika ba. Wannan cikin natan be kai na farkon bata wahala ba, sam be kwantar da ita ba befi kawai atimes tana jin amai da jiri ba thats all. Ranan da Al'ameen ze dawo ita da Baaba sukayi major cleaning sannan ta girka fried rice had'ad'd'e da kayan marmari akai.
  3pm Al'ameen ya dawo as always ta tare sa cike da so da k'auna. Al'ameen na dawowa Khaleefah ya k'auracewa Zeezee shi a dole d'an GATAN Da Da.
   Da misalin k'arfe biyar da mintuna aka na yamma Zeezee da Al'ameen suna manne a jikin juna as always, Khaleefah ko yayi bacci an kaisa d'akin shi. "Yauwa Princess am home tell me meh Dr ta gaya miki da kikaje asibiti?"
  "Promise me first no matter what you won't freak out and zaka min kyakkyawan fahimta baza ka zageni ba."
  "Princess meyasa zan zageki? I promise."
  "Okay ina zuwa." A nitse ta miqe ta shiga bayi ta b'allo test strip tayi carrying out test d'in ta jira yayi reading positive sannan ta fito ta buk'acesa daya k'ariso. A tsakar d'akin ya iso ya sameta. "Your hand" ta buk'ata, nuna mata yayi ta placing mai strip d'in akai. With bewildered eyes ya tsaya yana kallonta "me wannan kuma Princess?"
  "Strip ka duba kaga." Ido yasa ya ga ya nuna layi biyu nufin positive kenan sede har yanzu be gane waye keda cikin ba.
  "It says positive who is pregnant?"
 Kar ki kariya cewar zuciyarta. Da k'yar ta furta "I, I am pregnant again Sweetheart." A rud'e ta shiga jero jawabi "please don't be mad wallahi nima bansan ya hakan ya faru ba, ina kan plan-" crashing lips nasa yayi akan nata giving her the kiss of her life, mamaki sosai hakan ya bata meaning he is not mad that she is pregnant again kenan? Kissing nasa back ta shigayi itama with same intensity se chan yayi pulling out tare da d'ago fuskarta setin nasa suna kallon idon juna.
  "You are not mad Sweetheart?" ta tambayesa chan k'asa k'asa.
   "Why shall I get mad or furious saboda Allah ya sake azurtamu da wani arzikin Princess? Sekace wanda be san addini ba. I am so happy for the both of us, I can't wait to be a daddy again, thank you Princess I love you so much Allah ya inganta ya sauk'e ki lafiya."
  "Ameen My Soldier ban san da wani bakin zan yi maka godiya ba, you are so so sweet I am head over hills in love with you."
   "I love you more, yanzu kam Princess zaki haifo mana me kama dani ko?"
 "Princess me kama dani deh."
 "LOL zamu gani, yaushe zamu je muyi scanning Princess namu?"
  "Nayi ai."
  "Really? how many weeks."
  "Just 3."
  "Wow! We have a long way to go, I'll be by your side through every hardship because I've got you."
  "Thank you Sweetheart."
 "Gobe zamu fita first shopping." Da mamaki take kallonsa how he is getting excited and happy as if wannan ne first karonsa na jin tana da ciki. "Right?"
  "Sweetheart baka ta6a gajiya dani ne wai kam? Wannan fa ba shine karo na farko ba."
  "Princess if you'll get pregnant for the 10th time it will always be like the first time to me cause I love you."
  "I love you more." Turesa baya-baya ta shigayi seda ya fad'a kan gado ta fad'a akansa suna masu ragewa juna kayan jikinsu. Ganin abin na son fin k'arfin idona nima na buga legediz benz d'ina na ja musu k'ofa.

    Life continued, cikin k'oshin lafiya cikin Zeezee yake girma sosai take samun kulawa daga gun Al'ameen nata har izuwa lokacinda ya koma Abj.
  Alokacin da cikin Zeezee yake 8 months yayi k'ato ya fito sosai, rana d'aya Khaleefah dake 2 years 4 months kenan yanzu ya soma magana kad'an kad'an ba laifi dukda ba sosai kalamun nasa suke fitowa ba amman don son surutunsa baze barsa yayi shiru ba. Seda ya bari yana a tsakiyan Mammy'n shi da Da da ya kira Al'ameen.
  "Da da."
  "Yes Little Man ya akayi?"
  "Mammy" ya dawo da kallon sa kan Zeezee. "Yes Sweetheart."
  "Da da why is Mammy's tommy vely biggg?" shi a kullum abin mamaki yake basa don ba haka yasan Mammy'nsa ba. Shiru Zeezee tayi tana jiran Al'ameen ya amsa sa. "Uhn-uhm" yayi clearing voice nasa. "Mammy will bring our little Princess into life Little Man, ba kaga d'akin da aka gyara shi a gefen nakan nan ba? Toh na little Princess ne, Mammy is carrying her here." Yayi pointing cikin Zeezee.
  "Ahhhhh!" Ya bud'e baki wide open tare da dafe hannayensa kan chubby cheeks nasa. "Da da akwai baby in Mammy's tommy kenan?"
 "Exactly smart guy, akwai baby." Ai se ya sa kuka both Zeezee and Al'ameen sun rasa dalilin hakan. "Sweetheart why are you crying?" Cewar Zeezee tana neman jawo sa jikinta aiko ya sake sa wani kukan "don't touch me" da sauri ya fad'a jikin Al'ameen yana me cigaba da kuka. Da k'yar Al'ameen ya samu yayi shiru bayan promising nasa da yayi gobe tare zasuyi training men nasa da shi. Khaleefah nason ana training dashi wai yana son ya zama soldier shima harta uniform sanda aka d'inka mishi. "So tell me what made you cry Lil man."
  "Mammy is wicked che... che swallowed a baby." Haba dariya sosai Zeezee da Al'ameen suka kwasa. Da k'yar Al'ameen ya tsagaita dariyan nasa yace, "that's not true Honey, Mammy bata had'e baby ba."
  "Toh how?" Yana son yayi dogon zance amman maganan be zauna ba.
  "A market muka siyo se aka sa mata." Wayaga a market, dariya Zeezee keson yi amman ta maqe.
  "How?" Ya sake tambaya.
  "Through her stomach she didn't eat up a baby okay?"
  "Ejit tlue Mammy?"
  "Yes Sweetheart why will I eat up a baby? Mammy is not a bad guy."
  "Yeyy!" Jikinta ya koma tayi hugging nasa. "That's My Little Soldier."

   In two weeks time Al'ameen ya koma Abuja Zeezee taso ace yana nan zata haihu. Two more weeks ahead due date nata ya shiga tun asuba ta fara labour tun anan ta kira Al'ameen ta sanar dashi. Har Azahar Zeezee ta kasa haihuwa, da laborn Khaleefah da na wannan bata san na wanne yafi bata wahala ba sema gani take like na wannan, ko pushing ta kasa ganin abin nason fin k'arfinta tace ita a kira mata Al'ameen yazo. Nurse d'aya aka turo waje da tace Al'ameen ya shigo. Nurse na zuwa ta samu Mama dake d'auke da Khaleefah a cinya, "Sannu Mama please Al'ameen na nan?"
  "A'a yana Abuja ko ya 'yar tawa ta samu ta sauk'a?"
  "A'a Mama abin ya gagara har yanzu ko pushing ta kasa yi wai se Al'ameen na nan zata yi."
  "Na shiga uku ni Hafsah! Ya Al'ameen dake Abuja ya take son ayi? Don Allah ku bata hak'uri tayi pushing a wuce wajen."
   "Tak'i Mama maybe ki shigo kiyi mata magana halan taji ki ke." Wa Baaba Mama ta ajiye Khaleefah ta bi bayan nurse. Zeezee na ganin Mama ta sake sa wani kukan, gabad'aya ta fita daga kamanninta da hayyacinta Mama na iya rantsewa bata ta6a Ganin Zeezee cikin bad condition irin na yau ba ko rasuwan Baba albarka. Take wani irin wawan tausayinta ya mamaye zuciyarta da gudu ta nufi kan 'yarta tana share mata hawayen nata dakuma gumi duka da bakin mayafin ta. "Sannu Mama na, sannu kinji?"
  "Mama zan mutu please forgive me."
   "Shhh! Bazaki mutu ba Zainab, just push kinji?"
  "Mama I can't."
  "Yes you can Zainab am here for you."
  "Mama please don Allah ku kira min Ya Al'ameen."
  "Zeezee Ya Alameen na Abuja ya kikeson yazo nan?"
  "Mama I don't care ni don Allah ku kira min shi I need him please." Ganin yadda Zeezee ke kuka yasa Mama fitowa daga d'akin ta shiga neman Al'ameen daman wayan na gefensa shima tun sanar dashi da Zeezee tayi ta shiga labor yau ko office ya kasa shiga se tunanin wani halin take ciki yanzu yake. "Halo Mama ina yini?"
  "Lafiya Al'ameen ya kake?"
 "Lafiya Mama ya Zainab ta sauqa?"
  "Har yanzu fa Maj-Gen ba yadda ba'ayi da ita ba tayi pushing tak'i wai se kana wajen zata yi ni bansan ya zamuyi ba, ba kalan rok'an ta da banyi ba tayi hak'uri tak'i wai akira ka kazo."
   "Oh God! Ya zamuyi yanzu? Ga pilot na Private jet d'inmu yayi tafiya, Mama please ki rok'eta nasan zata ji maganan ki she is in so much pain."
  "Maj-Gen. ba yadda banyi da ita ba tak'i jina bari na had'aku a wayan muga." Nan da nan takaiwa Zeezee wayan tasa a speaker. "Princess?" Ya kirata cike da tashin hankali.
   "Ya Al'ameen" ta fad'a cike da azaba da wahala.
  "Princess calm down and breathe kinji calm down am here."
  "Ya Al'ameen I need you I can't do this without you please come."
   "Am here Princess am here for you, Khaleefah is also here fo you ke kad'ai zaki iya kawo mana Princess namu into live and I trust you. I love you so much."
  "I love you also."
  "Good breathe along with me, in... out. In... out" sunyi hakan kusan sau biyar sannan yace, "thats My Princess now is time to push."
  "No Ya Al'ameen bazan iya ba."
  "Zaki iya Princess I trust you remember kin cemin you'll never break down my trust, haka ne?"
  "Haka ne."
  "Good so I trust you I know you can do this. In the count of three se kiyi pushing kinji? Kinji?"
  "Uhum."
  "One... two... three push." Pushing d'in tayi da iya k'arfin ta amman ko 6ullo kai baby beyi ba. Jin ihun Maminsa tun daga waje yasa Khaleefah 6arkewa da kuka daman tun d'azu se turancin where is my Mammy and Granny yake yiwa Baaba kasancewar ba jin turancin take ba se ce mai take eh takalmin ka yayi kyau d'an kyakkyawa. Kansa ya rik'e yana toshe kunnuwansa "Mammy!" Ya kira ya na kuka nan ta fito dashi harabar asibitin tana jijik'a shi.






*MIEMIEBEE.   Team YGC!🎀 ZAIMEEN flames🔥🔥🔥*
  Beeenovels.blogspot.com 👄

No comments:

Post a Comment