Wednesday, 29 March 2017

‘YAR GATA CE!

*BY MIEMIEBEE*
  Page 80
 March 2017





    Back inside mutuwa ne kawai Zeezee batayi ba har airtime na Mama ya k'are ta kasa wani push d'in shima Al'ameen sau biyu katin sa na k'arewa yana sake loda new pin. Da k'yar ya samu Zeezee ta sake wani push d'in anan Dr Sammy Tayi exclaiming "the baby's head is finally showing we need three more push, you are doing good Zeezee."
  "Thats My Princess kinga saura just three pushes one for Mama, one for Khaleefah and one for me ko? Muje na Mama toh."
  "Ya Al'ameen ji nake like zan mutu ku bani fresh air please." Bayan fifitan da akayi mata aka samu ta sake wani push d'in. Sun mugun shan wahala sannan aka samu tayi remaining two pushes d'in. Suul Dr Sammy ta jawo baby "wow its a girl!" Wani ajiyan zuciya Zeezee ta sauk'e wearing the most expensive smile. "You did it Princess!" cewar Al'ameen sounding delighted.
  "I wouldn't have done it without you Sweetheart, I love you so much" sannan ta dawo da kallonta kan Mama "thanks for not giving up on me Mama I love you so much also."
   "We love you more" cewar Mama "so Maj-Gen. Bari a kintsa little Princess taka za ayi maka sending picture'nta."
  "Toh Mama thank you, take care okay Princess I love you." Ji yake ina ma yana tare dasu suma yaga little Princess nasa finally.
  "I love you more" Cewar Zeezee, daga nan Mama ta katse wayan. Baby'n aka wanke aka kawo wa Zeezee ita nannad'e cikin pink showel. Se tace tunda tasan kanta bata ta6a ganin kyakkyawar hallita ba kaman wannan little angel dake hannunta ba, gashin kanta ya sauk'o har kan goshinta seda ya had'e da gashin girarta. K'ara ta saki kad'an se kuma tayi shiru tana nonnok'e kanta cikin showel d'in which is damn cute. Bin every move nata Zeezee ke da kallo, "she is soo cute Mama."
  "Masha Allah, Allah ya raya mana ita."
  "Ameen Mama." D'aukanta Mama tayi a hoto ta wayan Zeezee tayi ma Al'ameen sending ta whatsapp take yayi updating nata ya kira su.
   "Princess little Princess is damn beautiful." Ya fara fad'a. Mama dake jinsu kasancewar a speaker phone suke wayan tace, "saboda wannan karan ta d'auko kamannin both parents nata shiyasa tayi kyau dayawa, tubarkallah." Murmushi Zeezee ta saki "nima tun d'azu kallonta nake na kasa gane dawa take kama nasan wannan hanci na ne a fuskanta."
  "Lips nata kuma da eye brows irin nawa ne." Cewar Al'ameen yana me jin dad'i.
  "Yess shape na face nata kam nawa ne her eyes kuma..." Zeezee bata k'arisa maganan ba baby'n ta bud'e idonta "irin na Maj-Gen!" Shouted Mama.
  "Yeyy!  Ta d'au lips d'ina, eyes amd eyebrows nose na Princess ne kawai."
  "Inji wa? Harda shape na fuska. Ai inade ba kamanninka duka ta d'auko ba kuma ma yawan gashin kan goshintan nan irin nawa ne."
  "Amman kamanni na yafi yawa ai."
  "Naji toh, wani suna kasa wa Lil Princess tamu?"
   "Sunan Mama Babba AMEENAH da al-kunyan AFREEN."
    "Masha Allah, Allah ya raya mana surika ta akan addinin muslinci ya albarkaci rayuwarta."
   "Ameen" su uku suka fad'a in unison.
  "Toh Sweetheart se mun sake waya zan shiga wanka yanzu."
  "Toh Princess take care okay? Mun gode Mama."
  "Ba komai Maj-Gen." Anan Mama ta katse wayan ta amshe Afreen daga hannun Zeezee, Zeezee ta shiga bayi bada jimawa ba Baaba da Khaleefah suka shigo, wajen Mama ya nufa da gudu "Granny where is Mammy?"
  "Mammy ta shiga wanka."
  "Who ish this toy Granny?"
  "She is not a toy Mijina, wannan Little Princess taku ce your baby sister."
  "My sister?"
  "Yes your Sister Mammy ta haihu, wannan ne Princess da tasa cikinta yayi k'ato."
  "Ohhhh! Ches cute."
  "Yes she is."
  "Sunanta Plincess?"
  "Afreen Da da ya nad'a mata sunanta Afreen." Ai kawai yasa musu kuka dalili kuwa wai sunan Afreen yafi nasa dad'i shi baze yarda ba.

 ***
   Kusan da Maghrib aka sallami su Zeezee. Son Afreen Zeezee ke sosai, yarinyar abar so ce kodan kyanta gata bata kuka like Khaleefah tun da aka haifeta har izuwa yanzu bata sha nono ba ruwa kawai tasha se bayan isha Zeezee ta sa mata mama a hankali ta kama, kad'an tasha ta sake. In three days time Al'ameen ya iso dad'i kashe Zeezee yau mafarkinta ya zamo gaskiya. Gashi ta haifi yara har biyu mace da miji sauran su koma Washington kawai yanzu dream nata yayi coming true.
  Suna wane sunan d'an fari haka wannan ma mutane suka cika, abubuwan da Al'ameen yayi a bikin sunan Khaleefah haka sak yayi ana Afreen Zeezee da 'yarta sun sha kyautuka sosai abin ba'a cewa komi. Zeezee na nan fit sekace ba wacce ta dire yara biyu ba. Ko da aka yi suna Al'ameen be koma Abuja ba hakan yasa Mama ta k'ara mata kwanaki hud'u kawai ta koma gida, Al'ameen keyi wa Afreen wanka da kansa atimes kuma Zeezee shide Khaleefah ya kasa gane feeling da yake yi wa Afreen atimes ya ji yana sonta atimes kuma yaji ya tsaneta yata kuka wai se an mayar da ita asibiti inda suka d'aukota sam wai Zeezee bata sonshi se Afreen, d'an banzan kishi ne dashi. Idan iskancin sa ya tashi kuwa yace shima seya sha nono musamman idan yaga Zeezee na breastfeeding Afreen, ba k'aramin drama suke sha ba. Akwai rananda Al'ameen ya kama Khaleefah na toshewa Afreen hanci don mugunta kawai, kad'an ya rage Zeezee bata mai duka ba ranan.
 
   Haka kuma rayuwarsu ta cigaba da kasancewa, what a family they are now kullum Zeezee na cikin kamawa Afreen gashinta into different and stunning styles saboda aljanun gashi ne da Afreen sekace ba yarinya ba. Cikin runfan Allah yara suke ta girma a yayinda soyayya tsakanin iyayensu ke sake dad'uwa a kullum.

   _3 years later..._
   Da gudu Afreen dake 3years old yanzu ta fito daga d'akin Khaleefah tana sanye ne da penal 4 uniform nata na school da alama yanzu suka taso daga. Kanta an kama mata into two ponytails, shima Khaleefah da gudun ya fito yana paparota. He is now 5 years 4 months old yaro ya zama saurayi sanye yake da wandon uniform na school nasu shima da singlet hannunsa d'aure dawani blue agogon ben 10 na roba. Kitchen Afreen ta fad'a tana kiran "Mammy Mammy!" Da gudu ta k'arisa tana 6uya Bayan Zeezee. Khaleefah na k'arisowa ya wuce direct zeje ya fincikota wai, da sauri Zeezee taja sa baya "what is wrong with you Khaleefah? Get your senses together, ban hanaka biyo Afreen kitchen ba?"
   "Kullum ni kita scolding d'ina Mammy, kinsan me tamin ne?"
  "Zan saka kneeling k'ark'ashin rana fah! Manners!"
   "I'm sorry, book d'ina fa ta d'auka tana drawing ABCD wai nata ne."
  "Afreen Princess give him back his book."
  "No! Ba naci bane its mine!"
  "Its mine keda kike Nursery 1, ita da zaran taga 1 akai kawai setace nata ne, nima ba primary 1 nake ba, give it back."
   "No I won't its mine."
  "Princess let me have a look at the book." Cewar Zeezee calmly.
  "O'o nawa ne."
   "I know lemmi have a look."
  "O'o zaki bashi."
  "Bazan bashi ba in gani." Da k'yar Zeezee ta iya ta amshe book d'in "Princess wannan ai na Khaleefah ne."
  Zaune tayi akan tiles tana shure k'afafunta tana kuka "nawa ne ga one akai."
   "Tsaya kiga, kinga ke sunan ki daga letter 'A' ya fara nashi kuma daga 'I' now tell me the Princess with brains what letter is here?"
  "Number I." Ta fad'a confidently. Dariya Khaleefah yasa "jita wai number I dolo kawai, letter 'I'"
  "Mammy kinji yana shemin dolo ba." Hannu ta d'aga ta zage shi. "Laaa a kunnen Da da Afreen na zagi."
  "Zagi" Exclaimed Zeezee "ban hana zagi ba Princess?"
  "I didn't insult him."
  "Yes you did, she did Mammy."
  "Toh kaima meya kaika ce mata dolo? Ban hanaka ba?"
  "Kin hana" ya fad'a yana kallon k'asa "ni bani book d'ina in koma d'aki na." Miqa mai littafin Zeezee tayi "oya hold your sister's hand kuje ka cire mata kayanta kasa mata leggings da crossed neck vest nata all in blue, na aiki nanny'n ku kasuwa. Kai kuma kasa shorts naka da shirt."
  Ni bazan cire mata ba rashin kunya ne da ita. Kuma ni banason shorts full length trouser zan sa."
  "Khaleefah! Manners!"
  "Am sorry amman kice karta min rashin kunya."
  "Princess banda rashin kunya kinji? Khaleefah is your big bro."
  "He ish not." Tayi maganan tana zuba mai harara.
  "Kingani ba Mammy?"
  "He is Sweetheart bisa ya cire miki uniform naki se kuzo muci abinci zamu fita shopping kunsan next week zamu je Washington ko?"
  "Yeyy! We are going to fly!!!" Afreen tasa ihu.
  'Yar k'auye kawai me acikin flying d'in?" Cewar Khaleefah yana wani basarwa.
  "Ba laifinka bane ai saboda bana maka malu kake wannan iyayin gobe zan kaika barbing salon a kwashe wannan gashin duka."
  "No please Mama I'm sorry bana son malu."
  "Then behave yourself."
  "I will Afreen lets go."
  "Mammy kishe mishi yashe min Plincess."
  "Call her a Princess Khaleefah."
  "Why shall I Mammy? Neither you nor Da da is a King or a Queen taya ta zama Princess?"
  "Mammy tell him to call me a Plincess."
  "Call her a Princess Khaleefah!"
  "No Mammy."
  "Aje ayi maka malu?"
  "Alright, alright Afreen Princess muje in cire miki uniform naki, shikenan?"
  "Yeyy! I am a Plincess."
  "Yes you are Sweetheart" pecking nata tayi a forehead sannan wa Khaleefah ai kuwa shi babban yaro yasa hannu ya share "ni banason kiss d'innan kinayi wa Afreen zallah."
  "Ai sena aske gashin nan zaka shiga hankalinka." Be sake cewa komi ba ya shiga jan hannun Afreen "banda duka ko fad'a Khaleefah duk wanda yayi fad'a baza a je Washington da shi ba." Seda suka 6ace daga kallonta ta hanzarta ta k'arisa lunch ta yi setting table, gashi Al'ameen ze shigo gobe she is damn busy.
   Bayan sun ci abinci sun kuma wani wankan suka fice Jifatu shopping mall. 100k each Al'ameen yama Zeezee sending akan tayi musu siyayyan kaya, duk abinda yaran suka ce suna so shi take siya musu tunda Baban su ya bada kud'in. Sunyi shopping kaman ba gobe sunzo fita kenan se k'iriniya Khaleefah da Afreen suke kaman yadda suka saba, basu mintuna biyu gu d'aya basu yi fad'a ba.

   Khaleefah na rik'e da stickers daya sa Zeezee ta siya masa zeje ya manna a d'akinsa Afreen ta sa hannu ta wabce tasa wani d'ankaren gudu tsantsi ne ya kwashe ta gab da ta kusa fita daga exit d'in, ta kusa fad'i kenan wani mutum ya tare ta daba don haka ba data sha k'asa. Gaban Zeezee ya mununar fad'i a rayuwa batason abinda ze ta6a mata lafiyan Afreen ko Khaleefah. Khaleefah ko dariya yake haushi ma yaji da aka tarota yaso ta fad'i ta buga bakinta nan gaba bazata sake guduwa da abinda ba nata ba.
  "Afreen!!!" Zeezee Tasa ihu. "Alhamdulillah!" Ta fad'a sounding relieved, da sauri ta k'arisa wajen tare da jan hannunta "bawan Allah thank y-" bata kai ga k'arisa maganan ba mutumin ya d'ago kansa, fuskan data gani ne ya mugun jijjigata.
   "Adeel?!" Ta furta with ultimate suprise and disbelief. Shima kallonta yake ya ma kasa cewa koda uffan. Da ba don ya ma Zeezee sani na sosai ba da seyace wata ce me kama da ita saboda wani haske na musamman data k'ara da kuma k'iba, a takaice tafi da yin kyau. "Zeezee, kece?" Ya fad'a shima disbelievingly.
  "Laaaa!" Afreen tayi covering bakinta da hannu "Khaleefah a stranger just called Mammy Zeezee, ba Da da ya hana ba?"
  "Ke da Allah kima mutane shiru and give me back my stickers"
  "Its mine."
  "Give it back." Ganin suna neman fara wani sabon fad'a Zeezee tayi seizing stickers d'in "oya kubi driver ku wuce mota."
  "But Mammy its mine."
  "Do as I ask Khaleefah to the car."
  "Mammy my stickers." Cewar Afreen.
  "Se munje gida, to the car now."
  Mammy why are you talking tona stranger? Da da ya hana."
  "He is not a stranger Honey sunan shi Uncle Adeel."
    "Da da ya san shi?"
  "Kibi Khaleefah ku wuce mota we'll discuss it later okay? I love you both." Hannun Afreen Khaleefah ya rik'e suka fice. "I should get going also Adeel, thanks for saving my daughter from tripping." Har yanzu Zeezee bata ishe sa da kallo ba a gaskia yayi babban rashi a rayuwan shi na rasa Zeezee gadhi nan ita har yara biyu. allah ya azurta ta dashi, kyawawa sasu wane yaran larabawa. Gaskiya ne Allah ba azzalumin bwansa bane, duk yadda yaso destroying wa Zeezee mahaifatrta Allah be yarda da hakan ba tunda she was innocent gashi nan shi yanzu yana neman shekara tara (9) da aure ko rabin yaro baida, a rayuwa koda wasa kar mutum ya yarda ya d'au alhak'in wani. Seda tazo gab da fita bakinsa ya iya bud'uwa.
   "Zeezee ko gaisawa ai sai muyi... please." Kaman bazata tsaya ba se kuma ta tsaya, "ina yini?" ta gaishesa briefly.
   "Thousands of days, how have you been great I guess."
  "Alhamdulillah ya kake da kuma Ruky?"
  "Lafiya, were those two your-" katse sa tayi with a "yes. Yarana ne babban Khaleefah, k'aramar Afreen."
  "Masha Allah time heals, Allah ya raya mana su."
  "Amin, nagode ya naka yaran?" Kai ya kad'a mata "sorry?" Ta tambayesa bewildering.
   "Allah be kawo rayayye ba har yanzu Zeezee, sau uku kenan tana haifa ba rai miscarriages kuwa ba iya ka yanzu haka she is 8 months pregnant duk tsoro saboda idan ta haifa ba rai suke fitowa kokuwa su koma kafin suna."
   "Subhanallah am sorry, Allah sa masu cetoh ne ya kuma kawo maku rayayyu."
  "Ameen Zeezee thank you, Zeezee nasan hak'k'inki ne yake binmu har yanzu Ruky have been searching for you Allah be ta6a had'aku ba. Naji har kinyi obtaining degree naki na miki murna sosai."
   "Ayyah thank you nikam na jima da yafe muku Adeel, dukan mu masu laifi ne kuma innallaha gafur rahim ku cigaba da addu'a Allah shall see you through in shaa Allah."
   "Zeezee am so happy for you, indeed rabuwa da ni da kikayi shine alkhairi a gareki ko ban tambaya ba nasan Maj-Gen na kula dake sosai and for that Allah ya biyashi da gidan Al~jannah."
  "Uhm, Ameen nagode nima, I should get going yara na suna jira na I don't wanna keep them waiting."
   "Achan ko?" Ya nuna motan da Khaleefah da Afreen suke ta fad'a a ciki.
  "Yes."
  "Nice ride also."
  "Thank you se wataran Adeel ka gaishe da Ruky kace ina mata fatan Allah ya sauk'eta lafiya ya kawo rayayyu."
  "Ameen Dear Friend In shaa Allah, ko zaki bani number'nki ta kiraki she've been wanting to do so."
  "Sure" wayansa ya miqa mata ta zuba mai sannan sukayi sallama ta fice yana me binta da kallo seda motansu yabar haraban mall d'in.


    *^ADEEL^*
  Home shopping na provisions Adeel yayi bayan daya gama instead ya koma gida se ya wuce gidan wani friend nasa saboda har yanzu shi da Ruky Mama kawai tura tafiyan suke for all these years al'amura basu dai-daita ba a tsakaninsu.

     _9pm_
 Miqewan Ruky Mama kenan daga kan gado da  k'yar saboda yadda tayi nauyi da alama cikin nata na 'yan biyu ne cause of irregular girman shi. Bayi ta k'arisa a dafe ta d'auro alwala tayi Sallah. Wayanta dake kan gado ta miqa hannu ta d'aga tare da duban lokaci ganin after 9 kuma Adeel be dawo gida ba kawai tasa kuka.
  Verily, tayi regreting dukan abubuwan da tayi wa Adeel and above all Zeezee.  Neman lamban Zeezee take ido a rufe, Adeel kuwa bata san me zata sake yi mai ba a rayuwa ya koma sonta kaman da, ba kalan neman tubansa da batayi amma har yau al'amura sun kasa daidaita a tsakaninsu da bak'in pentin data shafawa kanta da a baya har yanzu yake kallonta da shi, be sani ba ta shiryu yanzu she is really a changed woman. Sau dayawa yakan ce mata shifa ya yafe mata past is past amman tasani koda ya yafe mata be mance da misdoings natan ba. Idan ba wai ita ta nemi Adeel ba bayi ta6a nemanta idan kuma har ya zama affectionate and caring towards her to fa a lokacin tayi miscarriage ne kokuwa ta haifa d'an ya koma koya fito ba rai bayan nan Adeel bayi ma sanin wani yanayi take ciki, bazata iya tuna when last Adeel ya leqo d'akinta ba. Ci da sha kam bata rasa ba, bayan nan kuma ko wani k'arshen wata yana bata dubu goma, ba k'aramin kunyan abubuwan da tayi masa take ji ba.
    Ita yanzu ta hak'ura ya auro duk macen da tayi masa muddin itan zata faran ta masa rai amman yayi hak'uri ya bata chance su gyara tsakaninsu. For how many years now suke cikin abu d'aya? Shi be k'ara aure ba bai kuma bata chance da take nema ba a kullum, she misses her fulani guy, her Adeel. Bata da burin daya fi taga ita da Adeel are back as the lovebirds they were before. Layin Adeel da tayi saving as. _Baby_ tayi dialing sanda ya kusan tsinkewa ya d'aga.
  "Halo Baby?"
  "Yes Ruky."
  "Ina yini?"
  "Lafiya ya jiki?"
  "Da sauk'i, Baby ina ka shige? Yau ma bazaka kwana a gida ba? Please kayi hak'uri ka dawo I'm sorry." Ta k'are maganan cikin tsan-tsan kuka.
  "God! Kukan me kuma kike? Yaushe mukayi dake bazan dawo ba? I'll come home soon."
  "Dagaske Baby?"
  "Yes so stop crying its not good for your health."
  "Toh seka shigo, I love you."
  "Aha, bye." Sanyi sosai taji a ranta yau wata rana Adeel ya damu da condition nata. Duk da kasalan da takeji hakan be sata ta fasa garnishing wa Adeel nata had'ad'd'en jollof na spaghetti ba tayi setting table.

   10:23pm ta jiyo k'aran bud'uwan gate, makeup nata ta gyara. Sanye take da wani electric blue maternity gown, fitowa parlourn tayi sai dai kafin ta isa da bud'e k'ofan ya bud'e. "Sannu da zuwa Baby" tayi mishi tana neman amsan ledojin dake hannunsa.



*MIEMIEBEE.   Team #YGC!🎀*
*ZAIMEEN flames🔥🔥🔥*
Beeenovels.blogspot.com 👄

No comments:

Post a Comment