Thursday, 5 January 2017

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 30

  *January, 2016*




      Bayan an k’are breakfast Baba ya kira Al’ameen ya sake jaddada masa kan Zainab fa tasa ce sede inshi yace ya fasa and also karya saurari duk wani abinda zata fad’a mai saboda yarinya ce batasan ciwon kanta ba har yanzu. Sosai Al’ameen yaji dad’i ya buk’aci numban Zeezee inda Baba ke fad’a mai batada waya amman ze masa sending na uwar yaso se suna gaisawa tacan. Sosai Al’ameen yaji dad’i yayi godiya and not long enough Baba ya masa sending numban Mama. Mama na kitchen tana d’an aiki wayarta ya shiga ringing ganin new number ta d’aga tare da yin sallama.
   “Wa’alaikumus salam” Al’ameen ya amsa cikin sark’ak’k’iyar muryarsa me tafiyar wa mutum da imani tare da gaisheta, sama-sama suka gaisa Mama tace bari ta kaiwa Zeezee wayar. Kwance a tsakar d’akinta tana takan rusa kuka Mama ta tarar da ita “ke tashi gashi ana neman ki.” Kaman bazata amsa ba tace, “waye?”
  “Ina zan sani ki karb’a mana kina b’atamin lokaci.” Hannu ta miqa ta amsa seda taga Mama ta fita daga d’akin tace, “waye?” Harshly.
  “Uhm-uhm” Al’ameen yayi clearing throat nasa, “a farko de suna na Muhammad Al’ameen-” wata doguwar tsuka cike da rashin kunya Zeezee taja. Dama yasan this was coming, “Zainab is there a problem?” magana ta soma cike da tsiwa.
   “Yes and you are my problem, haba mana bawan Allah mena tare maka da zaka ce seni zaka aura? Wallahi kasani ni bazan aureka ba, bazan auri tsoho kaman ka ba in kuma har kabari akayi wannan aure kaji na rantse wallahi seka gommaci kid’a da karatu. Tun wuri gomma ka koma kaje ka samu Baba kace mai kai ka fasa. ‘yar 17 years dani zakace zaka aura? Kasani inada wanda nakeso kuma shi zan aura.” Kasancewar Al’ameen ba mutum neba me son tashin hankali da hayaniya bece mata komi ba yayi hanging wayar kawai. Ganin fa rashin kunya is not a solution tayi calling nasa back bayan yayi picking tace, “I’m sorry ina kwana Ya Al’ameen? Dan Allah karka gayawa Baba abubuwan dana ce maka kayi hak’uri sharrin shed’an ne” kai kawai ya kad’a.
  “Lafiya Zainab mun tashi lafiya?”
  “Lafiya k’alau.”
“Uhm so I will believe kinsan kowaye ni and kinsan purpose na kiranki danayi koh?”
  “Eh Mama ta fad’amin komai.”
  “Masha Allah, so am I welcomed?”
  “Ya Al’ameen dan Allah nace badon niba, ka dubi girman Allah SWT ka rufa min asiri ka janye maganan auren nan wallahi sam kai ba taste d’ina bane bawai ina nufin kai mumuna neba ko ka gaza ta wani fannin bane kawai inada wanda nakeso ne kaji k’aina please my future lies in your hands karka rabani da masoyi na.”
   D’an dariya ya saki, “Zainab you don’t even know me bale kice bakiya sona try giving me a chance kinji?”
   “Eh nide kayi hak’uri bani buk’atan sanin kanma. In mata kakeso akwai friends d’ina dayawa da suke son fararen maza kaman ka sena had’aku dan wallahi ni bana sonka banason farin na miji kuma farin ma wai soldier, soldier’n ma wai 42 years old, kayi hak’uri dan Allah” tasa mai kuka. Dariya sosai ta basa “to mesa bakiya sona? Give me one reason aside from I being fair and a bit aged, kinga bani na hallici kaina ba ko? Kuma fa kema fara ce naga.”
  “Eh ai ban kaika ba kuma ni fara sena auri fari? Ai sirkawa ake kai baka ga Mama fara Baba bak’i neba? Ka rufa min asiri dan Allah.”
   “Toh tell me the reason why you don’t like me.”
   “Sabida inada wanda nakeso.”
  “Oh is that so? Shikuma ya skin colour nasa yake?”
   “Yana nan da haske kad’an d’an bak’i-bak’i ba fari bane shi.”
  “Now I get where you are coming from, but Baba besan kinada wanda kikeson bane yace yaban ke?”
  “Yasani kawai bayason aura min shine.”
  “Toh mesa?”
  “Nikam sekace d’an jarida meh ruwanka da dalilin, ni kawai kace wa Baba ka fasa aure na banida tarbiyya kaji please Maj-Gen.” Nanma dariya ya saki.
  “Aikuwa ni bazan iya fad’awa Baba haka ba because through out my life ba gurl data ta6a getting attention and mind d’ina kaman ki Zainab.”
  “Ni dan Allah kadena banaso” ta sake sa wani kukan “wallahi inada wanda nakeso inhar kana sona bazaka sani auranka ba tunda bana sonka ni kamin tsoho ma dayawa.” Wani dariyan ya sakeyi sosai this time around gaskiya Zeezee is funny. “Toh naji we’ll do it this way zan fad’awa Baba kince kinada wanda kikeso in yayi agreeing ze aura miki shi saurayin nakin fine ni zan hak’ura if not kuma ni zan aure ki.”
   “Ai kaima kasan ba yarda zeyi ba.”
  “Toh mesa?”
  “Sabida yace saurayin nawa d’an iska ne shikenan kaji reason d’in ka huta yanzu zaka bar neman aure na?”
  “Yes naji amman bawai zan fasa neman aurenki bane because I love you for the sake of Allah Zainab try giving me a chance kinji? ke yanzu a d’an iskan kike sonsa?”
  “Eh wallahi ni ahaka nake sonsa dan Allah karka shiga tsakani na dashi.”
  “Nikuma ya kikeso nayi da son da nake miki Zainab?”
   “Ka yafe shi zanyi ta maka addu’a Allah kawo maka macen da zata soka tsakani da Allah kaima.” Nanma dariya yasa sannan yace;
  “Toh ai kece macen Zainab.”
  “Wallahi kaga ina maka sanyi-sanyi kake taking d’ina for granted ko? kasani fa na iya suburbud’a rashin mutunci, inhar ka kuskura kabari akayi mana aure wallahi you’ll rule the day you were born tunda ina baka girmanka na wanda ya haifeni baka gani. Ko kai ace yanzu kanada ‘ya kaman ni zaka yarda ta auri me kalan shekarunka ne? Kayi adalci mana Daddy.”
   “Uhm-uhm” yayi clearing thraot nasa “beyi zafi haka ba Zainab naji bari zanyi wa Baba magana.”
  “Da yafi kam kace masa ni ban maka ba kawai.”

     Tana katse wayar ta share hawayenta a yayinda Al’ameen ya kira Baba, “hello Brother.”
  “Yes Maj-Gen.”
  “Uhm yanzu muka gaisa da Zainab but it seems theres a problem.”
  “Problem? Wani iri kenan?”
  “Tace tanada wanda takeso I can’t force her into marrying me nakega zan hak’ura kawai.”
  “Tanada wanda takeso haka tace maka? Lallai yarinyan nan she wants to die kabarni da ita.”
  “A’a Brother please calm down, inhar hakan ne why not ka aura mata shi d’in?”
  “D’an iskan yaro ne kaide kanason Zeezee koko a’a?”
  “Ina sonta inde so ne.”
  “Toh kai zaka aure ta kada kaji duk wani shirmen da zata fad’a maka bata da wayo ne kaji please?”
  “Naji Brother am grateful.”
  “Nine da godiya” yana kaiwa nan ya katse wayar se d’akin Zeezee, buga k’ofar yayi seda ta razana. “Me kikace wa Al’ameen?” Ya tambayeta furiously.
  “Bb... Babu” tayi stammering.
  “Ina wasa dake ne? Nace me kikace mai ko sena baki kashi zakiyi magana?” Yayi taking few steps close to Zeezee. B’ari tashiga yi “Baba dan Allah kayi hak’uri ce masa nayi inada wanda nakeso bayan nan wallahi bance komai ba.”
  “Uwarki nan da ke da wanda kikeson, kinji ba uwaku duka nace ‘yar iska kawai ni zaki baiwa kunya? Nace na miki miji kice masa wai ke kinada wanda kikeso, iyyeh?” Yi yayi kaman ze rufe ta da duka nan tashiga k’wala wa Mama kira and ba tare da b’ata lokaci ba Mama ta fito daga kitchen. “Ya haka Alhj?” Tayi maganan tana jan Baba baya.

   “Kinji ba this should be the first and last time, Al’ameen ya sake kiranki kice masa kinada wanda kikeso kiga abinda zan miki in ban baki wa Ya Wakeel na shago as sadaqa ba ki canza min suna. ‘Yar iska dake ma kisamu gentleman kaman Al’ameen ki tsaya kina mai yanga? Ajinki da yasan halinki ma zece yana sonki ne? Dake nake magana!”
  “A’a kayi hak’uri.”
  “Wawiya kawai” yana kaiwa nan ya fice. Kuka Zeezee tasa tana sauqa har k’asa. “Ke me kikace wa Al’ameen d’in Babanku ke fad’a haka?”
  “Mama daman kinsan shi ya kira kika k’i gayamun?”
  “Ba abinda na tambaya ba kenan, me kikace mai Babanku ke fad’a haka?”
  “Gaskiya na gaya mai mana, banason abokin nasa.”
  “Gomma kin nitsu fa Zainab tam! Ki nitsu dan k’aniyanki meh Al’ameen ya rasa da zakice baki sonsa ko se an aura miki Ya Wakeel asalin tsohon zaki shiga hankalinki?”
  “Ni banason farin na miji-”
  “Ked’in mene? Ba fara ce keba? Ni d’inma ba fara bace? Se a k’imu saboda kalan fata?”
  “Kece de fara nide wallahi ba fara bace sabida ban kaiki fari ba, haske ne kawai dani. Ni wallahi bana sonsa gasa kuma soja, sojan ma tsoho har 42 wayyo Allah Very Own d’ina!!”
  “Zako ki gaji kibari wallahi dan koni nan na goyi bayan auran nan naku d’ari bisa d’ari.” Mama na kaiwa nan ta fice. Wayar Mama Zeezee taja ta kira Lubiee and not long enough ta d’aga “hello Babe, kwana biyu kin b’oye.”
  “Lubiee dan Allah help me out.”
  “Me kuma ya faru yanzu?”
  “Aure Baba zemin wallahi harya min miji wani farin soldier wai shi sunansa Muhammad Al’ameen kuma fa karki manta tsoho ne wallahi he is 42 years old.”
  “Wow! A Soldier?!” Lubiee tayi exclaiming.
  “Me wani wow? Karki ban haushi mana, think of a solution please.”
  “Ke Zeezee bakisan auren kalan masu age na Ya Al’ameen yafi dad’i ba? Come to think of it yanzu kallon yarinya yake miki duk wani abinda zaki masa koda rashin hankali babba kika tafka gani zenayi yarinta ke damunki yana baki excuse and above all sunfi iya soyayya wallahi. Incase of young brats kalan su Adeel naki kuma suma kansu rawa yake, he is just 25 koda ba laifi kika mai ba, baze tab’a iya overlooking slightest mistake naki ba sede ku taru kuyi ta fad’a da yarinta kullum. Ga solution nan Allah ya kawo miki har d’aki Zeezee, ni wallahi tun ban gansa ba nasan ya had’u soldier nefa! Its always my dream to marry a soldier me rank nasa?”
  “Ke gidanku kina jina ko? Zaki bani shawaran ne kokuwa?”
  “Toh gayamun me rank nasa.”
  “Oho wai Major-General ne komeh ni ba abinda ke damu na ba kenan. Help me out please, wallahi bana sonsa Babe, Very Own d’ina nakeso shi kuma zan aura.”
 
   “Ke Zeezee wallahi baki san ciwon kanki ba har yanzu, me zakiyi da Adeel bayan Allah ya kawo miki Soldier me future? Adeel fa malalaci ne ko aiki yak’i ya fara da anmai magana yace kud’in gadonsa ya ishesa. Ahakan kikeson ki zauna dashi? Rananda kud’in ya k’are fah?”
  “Seya nemi aiki a lokackin” ta amsa a takaice.
  “Akwai guarantee na samun aiki ne a wannan country namu?”
  “Ke ni ko a talauci zan zauna da Adeel bale ma he’ll never go bankrupt ki taimaken please Lubiee banason wannan Al’ameen.”
  “Aiko banida shawaran dayafi nace ki bud’e zuciyarki wa Ya Al’ameen dukda bansan sa ba nasan gentleman ne shi, eventually zaki fara sonsa just give it a try.”
  “I can’t, my heart is with Adeel and him alone I thought a friend indeed is a friend in need amman you aiint ready to help me thanks.”
  “Ze-” katse wayar Zeezee tayi koda Lubiee ta kirata kuma k’in d’agawa tayi haka ta rufe kanta a d’akin ta cigaba da kuka ita shikenan tana ji tana gani za’a raba ta da Adeel nata and theres nothing she can do about it? There has to be a way!

*~ *~ *~
  Washegari Al’ameen ya kira Zeezee still ta wayan Mama alokacin ma wayan na gefenta tana ganin numban jikinta ya bata shine tak’i d’agawa ya kusa yankewa Mama tashigo d’akin “wayana ne ke ringing?” Kafin Zeezee tace zata d’aga ya yanke. “Waya kira?”
   “Uhm... Uhm nima ban sani ba.” Amsan wayan Mama tayi ta duba nan ta gano Al’ameen ne.
  “Numban Maj-Gen d’inne zakice wai baki sani ba?”
  “Aw shine?”
  “Ohh k’arya zakimin? Inje in gayawa Babanki Al’ameen ya kira kika k’i d’agawa?”
 “A’a, a’a dan Allah kiyi hak’uri ya sake kira zan d’aga.”
  “Seya sake kira? Babban mutum dashi? D’aga ki kirasa maras kunya kawai!”
  “Mama sena ce mai meh? Kibari mana ya sake kira.”
  “Alhj!” Mama ta shiga kiran Baba.
  “A’a dan Allah ki bari zan kira san, zan kira.”
  “Oya amshi ki kira san!” Amsan wayan Zeezee tayi tana galla mai harara “ya what are you waiting for?”
  “Toh kifita mana kina tsaye akaina ne zan yi waya dashi?”
  “Alhj!”
  “A’a zan kira zan kira Allah” nan tayi calling nasa bada jimawa ba yayi picking.
  “Hello...?” Shiru Zeezee tayi not ready to talk, mari Mama ta kai mata a baya fas! “Baza kiyi magana bane?” Tana susa wajen tace, “ina kwana?”
   “Lafiya Zainab, how are you?”
  “Lafiya” ta amsa k’asa-k’asa se anan Mama ta fice nan Zeezee ta samu kanta “ka kyauta ai daka kama kaje ka had’amin gu wajen Baba.” Dariya sosai ya tsaya yi Zeezee bata gajiya da sasa dariya, “menayi kuma Zainab?”
  “Bansani ba, nace kace masa baka sona ka kama kace mai wai nace maka inada wanda nakeso saura k’iris yamin duka wallahi jiya.”
  “Duka?!” Yayi exclaiming yana sake mik’ewa kan red california bed nasa, haka kawai maganan Zeezee kesa sa dariya.
  “Eh mana, ai dagangan kayi.”

   Yana dariya yace, “ina ni Zainab! am sorry toh it’ll never happen again.”
  “Wai mahaukaciya ce ni da duk maganan da nayi kayita min dariya? Kuma ina bazaka ja baya da zancen auren nawa bako?”
  “Mesa zan ja baya da maganan auren ki Zainab? Just give me a chance.”
  “Aww ma tambaya kake? Wai kai rashin kunyan da nake maka bai damunka ne? Wallahi ko Adeel bana gaya mai magana kaman yadda nake gaya maka.”
   “I’m not Adeel I’m Al’ameen.”
  “Oho maka ni inada abinyi Daddy se anjima kuma wallahi Daddy har ka bari aka mana aure se kayi nadama.” Bata jira jin me zece ba ta katse. “Ai wallahi seka gommaci kid’a da karatu muddin ka bari akayi mana aure dan ni ai belong to Adeel and no one else.” Ganin Mama tayi bak’uwa tasa lock d’akinta tayi skyping Adeel “Hi Very Own.”
  “Sweetest Love I thought ko nayi laifi ne yadda kikayi dumping d’ina a trash can two days. I wanted calling you amman ina tsoro kar Mama ta d’aga, I really miss you.”
  “Wallahi I miss you more Very Own banji dad’i bane two days shiyasa.” ta gyara kwanciyanta kan gado tare dayin ruf da ciki, shima copying style nata yayi.
  “I should have guess, so how are you feeling now?”
  “Much better don’t worry.”
  “I miss you, I miss your arms around me.”
  “I miss yours too, I miss your fragrance Very Own its hard living without you” tayi stating as if though crying.
  “Shhh! Babe we will be together soon enough. I believe in us, so ya kike da Baba har yanzu, any progress?”
  “Not at all har yanzu wai aurar dani zeyi to whomsoever.”
  “Toh why not naje nace mai nazo neman aurenki?”
  “He isn’t dumb Adeel kallo d’aya ze maka yasan you must be my boyfriend, though har yau ban fad’a masa actual name naka ba duk da Sadeeq suka sanka.”
  “I love you Babe.”
  “I love you too...” Daga nan suka zarce hiran Lovey-Dovey dan kansu sukayi sallama not long enough Lubiee ta kirata da kaman bazata d’aga ba sannan tayi picking “meh na kira nan kuma?”
  “Haba Babe menayi kuma? Gimmie a break mana!”
  “Bansani ba ina ni zaki watsa ma k’asa a ido?”
  “Bawai batun watsa miki k’asa a ido bane Babe understand mana, kinfa san koda had’a sama da k’asa zakiyi Baba baze ta6a aura miki Adeel ba toh why not ki hak’ura da Ya Al’ameen d’in. Kuma fa he is just 42 bawani tsoho bane ko kin manta Annabi Muh’d SAW ma seda yakai 40 years aka basa annabci? Na miji at 42 wallahi ba tsoho bane.”
  “Oho damuwanki ni in sonsa kike wallahi ina iya had’aku.”
  “Banza! taya zan sosa? Nima my own Soldier is there somewhere waiting for me. Kinsan meh?”
  “Sekin fad’a.”
  “Why not to just go with the flaw?”
  “Kamar ya to go with the flaw ban gane ba.”
  “I mean koda bakison Ya Al’ameen pretend you do-”
  “Chabd’i! Akan meh?” Ta katse Lubiee take.
  “Ohhh! Ke ki tsaya mana kijini, will you?”
  “Toh inaji” tayi maganan in an I don’t care tone.
  “Ehem kina jina? Ko baki sonsa ki nuna a gida kin amince da auran saboda ladabi, kinga you’ll then kill two birds with one stone infact naki ma three birds ne. Na farko kinga ahaka ne zaki gyara relationship naki da Baba, na biyu Ya Al’ameen nasan me kud’i ne saboda Maj-Gen ne arzikinsa zaki tatsa kaman nono wallahi. Bakida waya yanzu kikace ya sai miki take zeyi saboda he wants to make you happy kema eventually you will not know when you’ll fall for him.”
 
  ”LOL dama-dama first and second points nakin ma amman dekam banda na ukun dan ni banga abinda ze sani son wannan Al’ameen ba.”
   “Why not?”
  “I have an alternative.”
“Which is?!” Lubiee ta tambaya a takaice.
  “Kinga daman a gida kowa ya riga yayi believing ina son shi Ya al’ameen d’in ba? Bayan biki sena gasa mai aya a hannu I won’t rest until ya sake ni kinga koda na dawo gida kowa ze yarda shine ya cuceni yaganni ‘yar yarinya yayi taking advantage d’ina only then I can marry my Adeel.”
  “Uhm har haka Babe? Nifa da zaki bi nawa wallahi ki mance da Adeel trust me and give Ya Al’ameen a chance he’ll definately win over your heart than Adeel did.”
  “Ba ruwanki, nide kinban clue shikenan thanks.”
  “Toh hope we good now? Tunda na share miki hawayenki yanzu?”
  “Ofcourse Babe I love you, kud’in Al’ameen se yayi kuka wallahi shi ba wai yaganni yana sona ba, ze sani!”
  “Kide bisa a hankali.”
  “LOL nagode semun sake waya probably a new line d’ina.”
  “Haha shegge Babe kina wuta ina binki da nuclear bomb Allah yasa toh.”
  “Ameen duk abinda akwai I’ll let you know.” Tana katse wayar ta ajiye tana tunanin ya zata fara gudanar da wannan plan nata into action. Sanin 5pm Baba zezo ya rufe mata d’aki, bayan sallan La’asr ta tabbata Baba na gida ta nufi d’akin Mama tayi sallama.

  “Wa’alaikumus-salam” shida Mama suka amsa.
  “Sannu Baba, sannu Mama.”
  “Yauwa sannu Zeezee” cewar Mama a yayinda Baba yayi banza da ita.
  “Uhm Baba nazo ne na baku hak’uri akan abubuwan dana muku a baya, kuyi hak’uri ku yafe min. Duk abubuwan da kuka min bangani ba dana tashi na sak’a muku da butulci  na 6ata muku suna a gari. Am truely sorry ina fatan zaku yafemin. Na tuba bazan sake ba, maganan auren Ya Al’ameen kuma da nace da abaya banaso shima kuyi hak’uri, wace ni da zaku yanke hukunci akaina nak’i bi? Ba Ya Al’ameen ba kowa kakeso na aura zan aureshi Baba inhar yin hakan ze farinta maku rai da Mama. Bazan gaji da baku hak’uri ba dan Allah kuyi hak’uri wallahi na tuba na kuma amince zan auri Ya Al’ameen ko a gobe kukeson in tare zan tare. Farin cikinku ya fiye min komai a duniyan nan sabida banida kamanku my dear parents am so sorry please find it somehwere in your precious hearts to forgive your dear daughter.” Ta k’are maganan cikin sautin kukan munafirci.


  *Team #ADEEL🎀 OR Team #MAJ-GEN.AL’AMEEN❣??? nide nace...!!!*




   *© MIEMIEBEE*

  www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄

8 comments:

Unknown said...

Yaro man kaza, zeezee kinshigo hannu, sannu da kokari sis.

Unknown said...

TEAM🎌👮#Good work miemiebee

Unknown said...

Nice one dear thanks for the update TEAM AL AMEEN OF COURSE

Unknown said...

#Maj-gen

Anonymous said...

Nafi so ta auri adeel just to learn her lesson. ta gane illar gata da yawa.

Anonymous said...

Up gen 100%
thanks alot dear

Unknown said...

General ne daidai da zeezee

Unknown said...

Kai! Allah ya shirya yarinyannan da iya magana. Kawai ta aureshi anyi me wuyan. 😃