Tuesday, 3 January 2017

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 29

  *January, 2016*



       Abokin Baba ne amman ba agemates neba su, sabida Baba na fifty-five (55) years old whereas abokin nasa MUHAMMAD AL’AMEEN SHETTIMA yana da forty-two (42) years old. Soldier (soja) ne babba yana matakin MAJOR GENERAL third to the last rank on list. Fari ne sol dukda kalan wahalan da soldiers ke sha a training besa haskensa ya dishe ba, gashi tsayayyen na miji me jini a jik’a. Yanada tsawo averagely da d’an kauri kad’an. Fuskansa bame fad’i bane yana nan siriri dai-dai, idanunsa suna nan ba manya ba bakuma k’ananu ba da long eyelashes, yanada slim but silky eyebrows wanda suke na wane anyi carving nasu. Yanada dogon hanci ba laifi amman ba irin har bakan nan ba. Koban fad’a ba za’a san yanada pink lips saboda farin fatarsa. A takaice de kallo d’aya za’a mai asan da akwai dangin Shuwa Arab tattare dashi saboda yanayin gashin kansa, saje da kuma na jiki.
   Sanye yake da uniform nasa na soldier dake mugun amsar sa har na k’in k’ari. Tunda Major General Muhammad Al’ameen (Maj-Gen Al’ameen) yake be ta6a yin aure ba, bakuma wai bayida ra’ayin yin bane lokaci ne beyi ba. Kasancewar girman rank nasa yasa duk inda zasa da sojoji suna gadinsa yake zuwa. Da manya-manyan Prado (land cruisers) guda biyu yazo gidansu Zeezee. Driver na parking d’aya daga cikin k’ananun sojojin rik’e da bindiga ya fito daga d’ayan motan tare da bud’e mai motar da yake cikin yana me saluting (sara) masa.

   Cike da k’asaita kamar yadda ya saba gudanar da al’amuransa gentlemanly ya fito, nan soldier’n ya rufe k’ofan sannan about four of them rik’e da bindigoginsu sukayi walking nasa izuwa gidansu Zeezee. Baba na zaune a parlourn sa yana karanta newspaper ya mik’e yayi welcoming aboki kuma k’anin nasa. Wato tun a Saudiya da suka had’u suka k’ulla zumunta bayan gano juna da sukayi kan attending secondary school thesame da suka ta6ayi sede tun kafin Maj- Gen Al’ameen ya iso secondary level Baba har ya gama dan ratan dake tsakaninsu.
   “Soldier ne gabad’aya yau a gidan nawa?” Baba yayi maganan fuskarsa d’auke da murmushi yana me mik’a mai hannu suka gaisa. Dariya kalan ta manya cikin sark’ak’k’iyar sweet manly not too husky voice nasa me sanya sanyi a zuciyar me sauraro ya sakar tare da fad’in “gani nan de, I thought I might suprise my Brother.”
  “You’re welcome, please come in.”
  “Wait for me here” yace da guards nasan nodding kai sukayi tare da saluting nasa sannan yabi Baba suka koma parlour. Nan sukayi former greetings “ban zata ai zaka iya gane kwatancen gidan nawa ba, yau shekara nawa?”
   “Gashi de nagane, you have a very nice house.”
  “Thank you Maj- Gen so ya aiki? Kullum baku zama gu d’aya.”
  “Alhamdulillah da godiya, dawowa na daga Abuja kenan nace barin k’ok’arta naga gidan Brother’n nawa yau.”
  “Aiko ka kyauta wallahi, am very grateful.”
  “Ya Madam da kids?”
  “Alhamdulillah duk k’alau. Yara duk sunyi aure d’aya ce a gabana, Madam ta fita ma bari ko ruwa ne a kawo maka. Zeezee! Zeezee!”
    “Wow, toh masha Allah.”
***
   Zumbur Zeezeen da ta manta when last Baba ya kirata ta miqe zaune kan gado tana raba ido, me kuma tayi yanzu da wannan kira? Bade ya gane tana communicating da Adeel ta wayan Mama ba. “Wayyo Allah na mutu gashi Mama bata gida.” faracunta ta shiga ci unknowingly.
  “Zeezee!” Baba ya sake kiranta. “Na’am” ta amsa tare da janyo bak’in gyale ta yafa akanta daman wata bak’ar doguwar riga ne a jikinta. Har 6ari take ta fito daga d’akin nata “na’am Baba gani” tayi maganan in a cracky voice zaue a k’asa. Tana noticing bak’on Baba tayi saurin gaishesa “ina wuni?” A nitse ya juyo da kyakkywar fuska yana kallonta sannan ya amsa “lafiya ‘yan mata ya karatu?” kai ta d’ago dan kallonsa sabida yadda muryansa ya mugun mata dad’i, fiye dana Adeel nata.
   “Lafiya alhamdulillah.”
  “Masha Allah.”
  “Jeki d’auko wa abokin nawa drink ko ta kawo ma abinci ne tunda daga tafiya kake?”
  “No not at all, don’t bother ruwan is okay.”
  “Toh ki d’auko mai drink d’in.”
  “Toh Baba” a nitse ta mik’e tare da ficewa, kawai ganin sojoji har hud’u rik’e da bindigoginsu tayi tsaye bakin k’ofan. Wannan kuma gunwa sukazo? Bade d’aukana zasuyi su tafi dani bako? Tayi tunanin haka a ranta. Sekuma datayi tunani kode gadin abokin Baban suke? Wow he must be a big soldier ba tare da b’ata lokaci ba ta had’a mai cup, ruwa, da frutta juice akan tray ta kai har gabansa ta ajiye tare da zuba mai kad’an daga cikin juice d’in a cup, “thank you koh?” Kai kawai ta gyad’a sannan kanta ak’asa ta juya ta koma d’aki.

   Duk wannan abu da take idon Maj-Gen Al’ameen bebar kanta ba, tun dayake, tunda ya san kansa be ta6a feeling like this with any other girl ba. Duk matan da Mamansa ke had’ashi dasu duk basu tab’a mai kamar ‘yar Zeezee daya gani ba yanzu. Ga kyau, ga fasali and above all ga tarbiyya (bari de abar kaza a gashinta!)
   “Masha Allah wannan ‘yarka ce Brother?”
  “Sosai itace last born d’inda nake fad’a maka ai.” Baba yayi maganan yana jin dad’i.
  “Wow! Seriously? Ashe kanada manyan yara haka.”
  “Amfanin aure da wuri kenan.”
  “Gaskiya in kace kai ka haifesu ma baza’a yarda ba.”
  “Haha koh?”
  “Sosai, toh Allah ya raya mana su” yayi maganan tare da sipping juice d’in. “So wannan tana nan ATBU ne?”
   “Eh tohh...” Baba ya shiga neman excuse, “sude suka gama makarantar this year amman bata samu admission ba ita.”
  “Ohh ayyah, maybe next time.”
  “In shaa Allah, so Brother do you plan on marrying her to anyone now or karatu zatayi?”
   “Yyess, aure zan yi mata soon in shaa Allah jiran miji kawai nake.”
  “Oh wow! Jifa yazo dai-dai da zama kenan.”
  “Haha, ko kanada wanda zaka had’asu ne?”
  “Will I make a good match?” Ya tambaya tare da d’age gira d’aya. Gyara zama Baba yayi “Maj-Gen kai da kanka?! Kode wasa kake.”
   “No seriously jokes apart yarinyar ka tamin sosai, like ban ta6a feeling this love at first sight da kowa ba seda ‘yarka, tarbiyya da ladabinta ya gama min komi.” Alhamdulillah kawai Baba keta nanatawa a ransa.
   “Toh ai wannan ba wani abu bane Maj-Gen. Zainab taka ce duka.”
 
  Zainab ya nanata sunan Zeezee a ransa. “Amma dagaske kake Brother?” Yayi maganan a bit suprised.
  “Sosai ma, daman neman meh amanan da ze rik’e min ita nake sekuma Allah ya kawo ka gaka kuma na gida ba abinda zance ai sede Alhamdulillah.”
  “Gaskiya yau da sa’a nake, mata a sama toh nagode Brother, so se muji daga bakin ta in nayi mata toh inko a’a we can’t force her koya kace?” Ya sake sipping juice nasa.
   “Wannan ba wani abu bane ai Maj-Gen kasa aranka ma ta riga ta amince.”
  “Toh hakane?” sanadiyar murmushin da yayi dimples nasa suka lotsa making him worth more looking.
  “Sosai mah kuwa.”
  “Toh godiya nake Brother in shaa Allah zaka sameni me rik’e amana.”
  “Nine da godiya nan da gobe zan sanar dakai duk abinda akwai in shaa Allah.”
  “Toh am grateful, thank you.” Be jima ba yace ze tafi, fifty thousand (N50,000) ya bawa Baba kan a baiwa Zeezee sam Baba yace baze kar6a ba amman Al’ameen yayita insisting seda Baba ya karb’a yayi mai godiya. Har waje ya mai rakiya sannan ya dawo shikenan atlast Allah ze rabasa da Zeezee shi bek’i ko a gobe a d’aura auren ba Zeezee ta tare tabar mai gida. Allah-Allah yake kawai Mama ta dawo ya watsa mata labari, Zeezee baiwar Allah dake d’aki batasan meke faruwa ba jira kawai take biyar yayi azo a rufeta as usual setaji shiru yau.

  To Maghrib Mama ta dawo gida, bayan dawowan Baba daga masallaci yashigo d’aki tare da rage kayan jikinsa ya zauna bakin gado.
  “Sannu da zuwa Alhj, naga yau baka kulle Zeezee ba ko punishment d’in ya k’are ne?”
   “Ya k’are mana tunda ta kusa aure.”
  “Ko kayi mata miji ban sani ba.” tai maganan tana ninke kayanta.
  “Ina abokin nan nawa yaron nan, Maj-Gen Muhammad Al’ameen wanda muka had’u dashi a Saudiya lokacin da mukaje?”
  “Eh wani farin sojan nan ko?”
  “Shi!”
  “Ayya na ganesa inade ba mutuwa yayi bako?”
  “LOL ko kad’an d’azu ai yazo yace na gaisheki ma.”
  “Ayyah ina amsawa.”
“Toh shi yaga wancan ‘yar iskan yace yana so.”
  “Shi Maj-Gen d’in yaga Zeezee yace yana so?”
  “Ni kaina abin yaban mamaki dan ban zata ma yanada ra’ayin aure ba saboda he is almost 42 ashede lokaci ne beyi ba.”
  “Alhj anya kuwa? Ba kai kamai tallan Zeezee ba?”
  “Kamar ya ni namasa tallan ta? Inma tallan ta zanyi ai bazan yi a gun masu mutunci kaman Maj-Gen ba sede a kasuwa.”
  “‘Yarka cefa Zeezeen kake aibanta ta haka.”
  “Aww dan bance zanyi sadak’anta masa ba kike neman gayamin magana, ina wayana baki sanni bane.”
  Da sauri ta d’ale gadon ta ja wayan nasa “wallahi baza ayi haka a gida na ba.”
  “Bani wayan nace!”
  “Ban badawa, kamar ya zakayi auren sadaqa da Zeezee? Astaghfirullah ko handicapped (masu nak’asa) ma anbar yin sadaqa dasu se Zeezee yarinya da kyanta da ilimi da budurcinta kace zakayi sadaqa da ita, wallahi a’a.”
   “Kyan banza kyan wofi! Me kyan ya amfana mata? Su Yasmeen da Mariam sun fita mutunci a idona, auren sadaqan zanyi da ita ta shiga hankalinta.”
  “Haba Alhj! Wallahi koshi Maj-Gen d’in yaji sadaqar da ‘yarka zakayi zesan da akwai wani b’oyayyen al’amari bayan nan ma koda bayan auren ne baze rik’eta da mutunci ba as zena mata kallon ‘yar iska.”
  “Toh mene ba ‘yar iskan bace? Sadaqan zanyi da ita ko sadakinta banason gani yasan batada value a ido na.”
  “Alhj inhar kana tsoron Allah kana k’aunan manzon sa baza kayi haka ba, kai yanzu baka tunanin ya zamu b’ullo wa Zeezee da wannan al’amari kasani ko zata yarda koko a’a?”
 
  “Da Zainab tana so da bata so Maj-Gen. zata aura se in shine yace ya fasa kinji na rantse.”
  “Toh naji amman de ba bata shi sadaqa zakayi ba dan Allah nace” da k’yar Mama ta samu Baba ya yarda ya fasa bada Zeezee as sad’aqa wa Al’ameen.
  “Toh barinje in fad’a mata.”
  “Wannan ke kika sa kanki don da kin sanar da ita da bakiyi ba auren ta da Al’ameen ba fashi.” Ba tare da tace komi ta kama hanyan d’akin Zeezee.
  As usual miqe kan gadonta ta tarar da ita “sannu Mama” tayi maganan tana k’ok’arin zama.
  “Yauwa sannu” Mama ta zauna a gefenta.
  “Yau Baban naki be rufe ki bako?”
  “Eh nima na rasa dalili.”
  “Uhm d’azu ashe wani abokin Babanku yazo.”
  “Eh wani farin soldier ko? Yazo har Baba ya kirani nayi serving nasa drink.”
  “Ayyah, Zeezee ki bud’e kunnwanki da kyau ki saurareni toh. Kinsani har yau Babanki yak’i hak’ura ko? Yana kan bakansa na yin sadak’ar ki with whomsoever right?” A hankali Zeezee ta gyad’a kai “eh Mama amman ai zaki cigaba da basa hak’uri ko? Kar yayi min auren sadaqa.”
  “Sosai se a inda k’arfi na ya k’are.”
  “Nagode Mama.”
  “So kinga abokin Babanku da yazo d’azun ai? Sunansa Maj-Gen. Muhammad Al’ameen Shettima ya ganki yace yana sonki da aure-”
  “Aure?!” Zeezee tayi maganan unbelievably tare da miqewa.
  “Aure kuma Babanku ya riga ya basa ke, ko ince ya mishi sadaqar ki.”
  “Innalillahi wa inna ilaihi raji‘un My Very Own!” se kan gado tayi ta fad’i a sume. “Zeezee! Zeezee!” Mama ta shiga tapping nata ganin ba response ta nufi d’akin Baba aguje tana k’wala mai kira “Alhj! dan Allah kazo Zeezee ta sume min!”
  “Ba inda zanje, ta mutu taga dama auran Al’ameen ne se tayi dan haka kibar cika min kunne.”
  “Alhj! Abinda zaka ce kenan?”
  “Tabbas” batayi ta kansa ba ta koma d’akin Zeezee har yanzu she is unconcious. Bayi ta nufa ta d’ibo ruwa ta yayyafa mata a fuska a hankali ta soma kefta ido, wani hamdala Mama ta saki “Zeezee! Tashi kinji?” Kuka Zeezee ta shiga yi “Mama dan Allah ku rufa min asiri, wallahi na tuba bazan sake ba dan Allah karkuyi sadaqa na, na rok’e ku.”
  “Zeezee calm down nayiwa Baban naku magana an fasa yin sadaqan dake amman hakan bawai na nufin bazaki auri Maj-Gen. bane aure ba fashi, Muhammad Al’ameen shine mijinki Zeezee.”

  “Noo, noo Mama dan Allah karku min haka, what of My Very Own? Wallahi bazan iya auran YaAl’ameen ba, bana sonsa yamin tsoho dayawa Mama karku lalata mi future dan Allah in aurar dani Baba yakeson yi dan ya huta a gobe wallahi zan kawo mai miji ku rufa min asiri dan Allah.”
   “Dolenki ki auri Al’ameen da kink’i da kinso ‘yar iska kawai.” Fad’in Baba dake tsaye bakin k’ofa “aure ba fashi, nan gaba ko kasheki za’ayi akace ki kwana a waje baza kiyi ba. Kinma ci sa’a shi Al’ameen ne yace yana sonki wallahi da Ya Wakeel na shago ne ya soma zuwa kokuwa me dry clean d’innan Uthman kinji rantsuwa ba kaffara zan basu ke a sadaqa ma in huta dake. Tun wuri gomma kinsan ina ke maki ciwo, da d’an iskan saurayin naki zaki kawo min kuma kike tsammanin zan aura miki shi? Lallai bakida hankali.”
   “Baba dan Allah kayi min rai, karka min auren dole na tuba, ka yanke min kowani hukunci amman banda wannan Mama dan Allah kibasa hak’uri banason Maj-Gen. bazan iya auransa ba.”
  “Se muga meze hanaki auran nasa, muddin ba mutuwa kikayi ba wallahi Al’ameen shine mijinki, Hafsah tashi kibar d’akin nata zan rufe.”
  “Baba dan Allah kayi hak’uri wallahi bazan sake ba na tuba, Mama dan Allah ki basa hak’uri, ku rufa min asiri dan Allah.”
  “Alhj dan Allah ko na yau ne kabarni in kwana anan kaga condition nata.”
  “Ki tashi nace karki b’ata min rai... Bazaki tashin bane?” Zanin Mama Zeezee ta tattara ta rik’e tana kukan cire rai “Mama dan Allah kuyi hak’uri karku aura min Maj-Gen wallahi na tuba”
   “Bazaki saketa bane?” Kai kawai take jijjigawa tana me cigaba da kuka, “dan Allah kuyi hak’uri wallahi bazan sake ba.” K’arisawa cikin d’akin Baba yayi yaja Mama kamar baby’n roba sukayi waje sannan ya datsa kwad’o a k’ofan. Bin k’ofan Zeezee tayi tana bubbugawa tana kuka sosai “Baba dan Allah kayi hak’uri, kamin duk wani abinda kaga ya dace dani amman banda wannan dan Allah, karka aura min wanda bana so, na rok’eka dan Allah fa nace” ta k’are maganan tana kuka tana jijjiga k’ofar. Mama kanta batasan a sanda ta soma hawaye ba.
  “Alhj dan Allah ka tausayawa yarinyan nan kabarni in kwana da ita yau” ko sauraronta beyi ba yaja hannunta zuwa d’akinsu. “In har kika koma d’akin ‘yar iskan can kuma ban yafe ba.”

****
    Kuka Zeezee ketayi a tsakar d’akin nata a yayinda kan ta keyi mata wani irin sara. How? Taya Adeel na raye zata auri wani na miji daban, mijin ma wai abokin Babanta wanda she is sure da yayi aure da wuri da ya haifi kamanta. Taya zata fara sanar da Adeel wannan sad news? If only tasan ya zatayi ta gudu data gudu tabar wa Baba gidan gabad’aya. She can’t imagine life without Adeel, her Very Own. Kukan ta cigaba dayi har seda bacci 6arawo yayi gaba da ita a wajen.

    Da Asubah Mama ta taho da key ta bud’e mata k’ofar. A hankali ta tayar da ita “tashi Zeezee kiyi Sallah Asubah tayi, kinyi Isha ma kuwa?” Kai ta kad’a da k’yar “Mama kaina ciwo”
“Tashi kiyi alwala toh bari na kawo miki magani.”
   “Banaso bana buk’ata na gwammaci ciwon kan ya kasheni na huta tun wani zamani aka dena auran dole wa mutum da Baba ze aura min tsoho kaman abokinsa.”
   “Ya isa haka toh. Aww baki godewa Allah bama da ba sadaqar ki zeyi ba wato?”
  “Ai duk d’aya ne me maraban dambe da fad’a? Taya zan auri sa’an Baba na Mama? How?”
  “Ke wayace miki Maj-Gen. sa’an Babanki ne? Shekara goma sha uku (13) nefa tsakaninsu koni nan na girmeshi tunda he is 42 nikuma am 45, tashi kiyi Sallah.”
  “Mama yanzu kema kin goyi bayan a aura min tsoho? Am just 17 fa sena kama auran me 42 years old? Kun min adalci kenan? Dan Allah ki bawa Baba hak’uri inada wanda nakeso in aurar dani yake sonyi a yau d’innan zezo su tauna ko sadaqa na ne seya basa na yarda amman banda Ma-Gen please.”
   “Wa? Kina nufin d’an iskan saurayin ki dake saki kwana a waje? Wallahi koni ne bazan aura miki shiba. Inba ke da sokanci ba ajinki Sadeeq ne ko waye ze yi zaman mutunci dake ne? Ya riga da yasan ‘yar iska ce ke koda kin auresa baze na ganinki da mutunci ba.”
  “Inde Ad- aww Sadeeq, inde Sadeeq ne wallahi I trust him he’ll never betray my trust.”
  “Kefa wawiya ce jekiyi Sallah da Allah!” Nan da nan ta biya Isha tayi Asubah Mama ta b’allo mata panadol tasha. “Ke inbanda abinki mutum kaman Maj-Gen. yace yana sonki kik’i? Mene ya rasa? Ga kyau, ga future gakuma hankali da sanin ya kamata, nitsatstsen namiji kaman shi. Ko bakiga sojojin da suke guarding nasa bane? Babban soja nefa.”
  “To hell with all of that, ni bana sonsa, banason farin na miji banason auren soldier and most of all banason auran abokin Baba na ni Very Own d’ina nakeso” tasa kuka.
  “Zakiyi ki gaji ki bari kuwa, ai dama bari nayi uban naki yayi sadaqan ki tunda ke bakida mutunci. Gomma tun wuri kin tattara hankalinki gu d’aya ki nitsu ki bud’e zuciyarki wa Al’ameen dan wallahi kece zaki wahala kizo ki tashi a tutan babu keba Sadeeq ba keba Al’ameen ba.” Mama na kaiwa nan ta fice. Ihu Zeezee tasa kanta kaman ze fashe dan ciwo amman hakan besa tabar kukan da take ba, ko breakfast tak’i ci ranan.





*© MIEMIEBEE   Team #YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄

8 comments:

Anonymous said...

thanks alot
May god bless you

Unknown said...

Thank you

Unknown said...
This comment has been removed by the author.
Unknown said...

Thanks dear I can't to read d next page 😘💋❤

Unknown said...

Sorry I can't wait to read the next page 😍

Unknown said...

Kai wallahi ansami perfect match wa zee zee, more grease to ur elbow sister

Unknown said...

Kai wallahi ansami perfect match wa zee zee, more grease to ur elbow sister

Unknown said...

Gara dai is better al ameen din cause adeel besan mutuncinta ba