Friday, 6 January 2017

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 31

  *January, 2016*




       
   Wani irin dad’i maras misaltuwa Mama taji a ranta a yayinda hawayen jin dad’i suka soma gangarowa daga idanunta. Finally Allah ya amsa mata addu’arta ya shiryar mata da Zeezee a lokaci guda. Ba ita kad’ai ba harta Baba yaji dad’i matuk’a, saboda yadda Zeezee ta tsara maganan bame sanin wai duk plan ta had’a ga yadda take kuka me tsuma zuciya full of regret. “Come here Sweetheart” Mama tayi beckoning nata over. A nitse ta miqe, hugging nata Mama tayi suna kuka tare duk anan kallonsu Baba yake seda Mama tayi releasing Zeezee yaja hannun Zeezee tare da hugging nata shima. “Alhamdulillah! My old Zainab is back na yafe miki K’anwata, Allah ya cigaba da shiryar mana dake.”
   “Ameen” shida Mama suka fad’a.
  “Baba ina me sake baka hak’uri.”
  “Kema kiyi hak’uri K’anwata for what happened am sorry kinji?”
  “Ni baka min komi ba Baba, I love you so much.”
  “Allah cigaba da raya mana ke.”
  “Ameen” nasiha sosai Mama da Baba suka ta mata a yayinda take ta sheqe kuka, sun gama mata ta musu godiya ta fice a d’akin tana mejin dad’in completing first mission of her plan. Sosai Mama da Baba sukaji dad’i se sawa Zeezee albarka suke duk sun d’au dagaske ne Zeezee ta shiryu musamman ma Baba da abin yafi damunsa nunawa ne kawai bayayi.

   Washegari Zeezee na tashi da safe bayan tayi wanka ta nufi d’akinsu Mama ta gaishesu cike da ladabi sannan d’akin Omar bayan nan ita da Mama suka shiga kitchen for the first time. Dukda kwa6a take amman yau ta shiga kitchen d’in da sunan yin aiki. Sun gama breakfast Zeezee ta ari wayan Mama da sunan zata gaishe da Al’ameen. Ba tare da Mama ta kawo wani tunani a ranta ba ta bata wayan, seda ta rufe k’ofan d’akin nata ta zauna kan kujera sannan tayi dialing number’n Al’ameen. Bejima ba ya d’aga.
  “Hello Ya Alameen ina kwana?”
  “Wow! Zainab kece?”
  “Nice mana, ina kwana?”
  “Lafiya hope you slept well?”
  “Yes I did I hope you too.”
  “Alhamdulillah so you called? Am startled anya kuwa kece?”
  “Nice mana, na kira ne dama na baka hak’uri game da rashin kunyan dana maka a baya, am so sorry hakan ya faru ne bisa rashin tunanin da banyi ba amman I promise it’ll never happen again. Kayi hak’uri please na amince zan aure ka, I welcome you to my life wholeheartedly.” Al’ameen was left dumbfounded, anya kuwa Zeezeen daya sani ce? Kode she is possessed by some kind of evil spirit ne? Kokuwa shiryuwa tayi, but anya?
  “Hello Ya Alameen? I know its hard for you to believe me but believe it or not na tuba kuma ina neman gafararka.”
  “Masha Allah Zainab, I think am the most happiest man on earth right now.”
  “Am glad I made you feel that, so ka yafemin?”
  “Ni bakiyi offending d’ina bama ai Zainab bale ki nemi yafiya na.”
  “Hakane?”
  “Sosai ma Zainab.”
  “Toh nagode mesa kake cemin Zainab?”
  “Isn’t it your name?”
  “It is amman Zeezee ake cemin ai.”
  “I prefer your actual real name, yana min dad’i sosai.”
  “Thank you kaima sunanka na min dad’i.”
  “LOL hakane?”
  “Yes, so ya aiki?”
  “Nad’an kar6i leave but alhamdulillah.”
  “Toh masha Allah, ya kowa da kowa a gida? Kanada sisters? If yes meh sunansu?” Haka Zeezee tayita jan Al’ameen da surutu ranan gabad’aya mamaki ya rufesa he can’t believe actually its Zeezee. Shiko biye mata yayi ko breakfast ma beyi ba ranan seda airtime na Mama ya k’are. Take ya kirata back tayita mai hiran shirmeh bayan sunyi sallama yayi wa Mama VTU transfer’n 10k.

  Wani maqirin murmushi Zeezee ta saki “ai wallahi Soldier seka gommaci kid’a da karatu bakai wai Zeezee kakeso ba? Ha!” Ta cize lips nata. Haka nan tun daga ranan Zeezee bayan 2-2 days take kiran Al’ameen. Atimes in bata kira ba shi yake kira suyita hira kaman dagaske, Al’ameen could’nt ask for more, Zeezee is the most happiest and sweetest thing that has ever happened to him. Tunda yake be ta6a son ‘ya mace kaman Zeezee ba kullum cikin zancenta yake wa elder Sis nasa Sadeeyah da younger sisters nasa Salmah and Ayshah duk they are so eager suga Zeezee. Mamanshi Hajiya Ameenah kam couldn’t ask for more finally Allah ya amsa mata addu’arta her son is in love. Kullum Al’ameen cikin zancen Zeezee yake duk friends nasa sunsan da zaman Zeezee, sonta yake tsakani da Allah, fiye da tsammanin d’an Adam, wannan kenan!

  ****
   Har a yanzu Zeezee bata sanar da Adeel halin da ake ciki ba kamar yadda tayi hani wa Lubiee da komin rintsi karta fad’a mai itama when the right time comes she’ll let him know. Everybody a gida believed Zeezee da Al’ameen soyayya suke saboda har sau biyu yake zuwa mata Baba da kansa ya basu parlour’n shi suyita hira, aduk zuwansa kuwa seyayi wa Zeezee kyautan kud’i wanda kaman dagake ta d’auka duk ta baiwa Mama. Al’amura sun daidaita ras tsakanin Zeezee da Baba sun dawo kaman yadda suke da sede har yanzu Baba bece ze sai wa Zeezee waya ba kamar kuma yadda kuma be miyar mata da motarta ba.
 
  *~ * ~*~
   Yau ranar ta kasance Wednesday, 11:27AM Zeezee ta ari wayan Mama as always ta kira Al’ameen bayan sun gaisa take cemai, “Ya Al’ameen tun d’azu naso kiranka Mama bata tashi da wuri ba.”
  “Ayyah ba komai My Princess, how are you?”
  “As you are, did you sleep well?”
  “I did I also dreamt of you.”
  “Oh really?”
  “Yeah” hira suka tayi chan yake fad’a mata ze koma aiki Abj anjima.
  “Ayyah I will miss you.”
  “Zanzo muyi sallama karki damu we’ll keep in touch.”
  “Da wayan Mama da kullum ke hannuntan? Ina ma ace inada waya na sabida muna waya kullum”
  “Kuma haka fa yakamata ace kema kinada wayarki.”
  “I use to have one.”
  “Ya 6aci ne?”
  “A’a Baba ne yayi seizing ya fasa lokacinda na ta6a yin wani laifi.”
  “Will he agree if I buy you a new one?” Dad’i sosai taji finally her plan is working.
  “Ban sani ba seka tambayesa.”
  “Toh karki damu My Princess zan taho miki da sabon wayanki yau in shaa Allah.”
  “Really Ya Al’ameen?”
  “Don’t you trust me?”
  “Yes I do Ya Al’ameen thank you so much.”
  “Shh! Lemmi take my shower my flight is by 1:30pm.”
“Tam sekazo see you” nan ta katse. “Mschww gaskiya na miji anyi soko wallahi yanzu koshi Ya Al’ameen ne kome sunansa hankali baze basa duk faking nake ba? Ni ina zan kai tsoho kaman sa? Anyways his own wahala my new phone is coming soon can’t wait to skype my very own!”

12:19PM Al’ameen ya iso gidansu Zeezee da sabuwar wayarta cikin leather suna zaune a parlour da Baba bayan sun gaisa yayi clearing throat nasa “Brother ina fatan banyi gwaninta bako?”
  “Name fah Maj-Gen?”
  “Waya na siyo wa Zainab namu tace she is not confortable amfani da wayan Madam.”
  “Oh hakane? Ba matsala toh.”
  “Toh nagode Brother yauma zan koma Abj nazo muyi sallama da ita ne.”
  “Toh bari nayi mata magana” Baba da kansa yaje ya kirawo Zeezee “K’anwata Maj-Gen yazo wajenki.”
  “Toh Baba ina zuwa” ta amsa tana murmushi, gyalenta taja sannan ta fice a k’asa kamar yadda ta saba kullum ta zauna tare da mai sannu da zuwa. Duk da haushinsa da takeji takasa ignoring kyan da Al’ameen ya mata, bata ta6a ganin hot man in uniform kaman shi ba, farin fatarsa dake bata haushi ma yamata kyau yau amman ba hakan yasa taji tana sonsa ba ita Adeel nata kawai takeso.
  “My Princess bazaki zauna kan kujeran ba yanzu?”
  “A’a Ya Al’ameen nanma yayi.”
  “A’a ni ki hau ki zauna please.”
  “Seriously nanma yayi karka damu.”
“Ni sekin hau toh.” Seda yayi dagaske sannan kaman dagaske Zeezee tahau kujera ta zauna se wani kakkare fuskarta take. Hira kad’an suka ta6a yace ze tafi leather’n wayan ya ajiye mata kan cinyarta. “As promised My Princess in colour’n be miki ba let me know zan turo wani yaro na ya sai miki sabo.”
  “Toh meh aciki Ya Al’ameen?” Tayi maganan tana bud’e leather’n black jet iphone 7s taga ciki “wow! Ya Al’ameen thank you!”
  “Nifa na gaya miki banason godiyan nan, do you like it?”
  “Yes I do thank you.”
  “Am glad toh ni zan wuce.”
  “Toh bari nafad’awa Baba” sede data duba alokacin Baba yashiga wanka dan haka ta rakasa har waje tana ganin guards nasan ta wani had’a rai seda Al’ameen ya gano hakan.
  “Bakison ganinsu ne?”
  “A’a” ta k’irk’iro murmushin k’arya “kawai tsoro suke ban da wannan guns d’in.”
  “Next tim zanzo barasu zoba tunda baki son ganinsu.”
  “Oh common karka damu Allah ya kare toh.”
  “Ameen My Princess” Seda taga ficewarsu ta koma ciki wayar ta bud’e a garin haka airtime na 10k da new sim card ya fad’o. Murmushi ta saki “wai! Zanyi skype da Very Own har sena gaji!” Had’a wayar a charging tayi. Baba na fitowa daga bayi taje ta fad’a mai. Nasiha sosai yayi mata and like a good girl tayi godiya ta fice.

****
   Life couldn’t be better tun daga ranan da Al’ameen ya sai wa Zeezee waya ta rage kiransa as 24/7 tana kan video or voice call da Adeel nata. Shima Al’ameen dake ya koma aiki yanzu seya jera kwana uku be kirata ba in se in yasamu free time yake kirantan, ita kuwa seta mai k’arya wai gari ba wuta shiyasa bata samun kiransa itama wayarta ba chargi. Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa, wani new chapter’n love Zeezee da Adeel suka bud’e. Da k’yar ranan Baba yabar Zeezee tajeta gidansu Lubiee nan ma Omar yasa yayi dropping nata. Achan suka had’e da Adeel nata, wani k’war jini taga ya sake mata cause she can’t remember when last ta sasa a ido tun birthday’nsa se inde a video call. Hira da shafe-shafensu suka ta sha like never se 5:30pm da Omar yazo d’aukanta sukayi sallama nanma da Adeel yayi hugging nata ji take kamar ta bisa su gudu karta koma gida remembering she has a better plan in mind sukayi ba-bye ta fice.

    Da daddare tana ta chatting abinta da Adeel da Lubiee. Lubiee tayi messaging nata _Babe nifa har yau kink’i nuna min hoton Ya Al’ameen na k’osa naga angon namu._
  _Gaja ai Ya Al’ameen kome yake ba shine real ango naba ko kin manta Adeel ne? Ya Al’ameen is the ladder that will take me to my dreams._
  _Hmm nide ba ruwana kimin sending pic nasa kawai abinda na tambaya kenan._
  _Yo ai banida pic nasa nikam Adeel ya hanani barin hotunan maza a waya._
   _Babanki dake da Adeel d’in Babe please show me his pic or kishinsa kike ne?_
  _Over my dead body wallahi banida pic nasa amman bari na duba dp’nsa ko yasa na hankad’o miki._
  _Yauwa do please._ Zeezee na dubawa aiko Al’ameen ya cire daman wani hotonsa ne da uniform ya bala’in yin kyau.
  _Ke Babe seki d’au na annabawa yacire pic nasan._
  _Dang it! toh ask him mana ai he is your boyfriend._
  _Fake boyfriend FYI plus a dalilin meh zan tambayesa pic nasa? Ba seya d’au sonsa nake ba._
   _Oh! Toh Allah shiryaki nide na gane rowansa kawai kike min._
  _LOL Allah ya mayar zan miki sending._ chan dare kafin ta kwanta taga yayi changing dp nasa ya miyar dana d’azun take tayi saving ta turawa Lubiee nanfa Lubiee tayita hauka ita sam Al’ameen yafi Adeel kyau kuma ai in bawai an fad’a bane baza’a d’au ma yayi 42 ba sede 38 haka. Zeezee mafa tasan da zaman haka amman dan iskanci da neman take gaskia sam tace ita ba haka ba Al’ameen is too old.

   _Several months later..._
    Al’ameen har ya dawo daga Abuja angama magana ansa date na bikin aurensa da Zeezee in 3 months time. Jin haka kuma Zeezee ta kariya ta soma kuka sosai ita bata son auren. Karap Mama ta bud’e k’ofar d’akinta da wuri ta share hawayen nata. “Kuma kukan me kike?”
  “Niba kuka nake ba.”
  “Banida ido ai nace kukan me kike?”
  “Mama ni banason auren wallahi.”
  “Baki so?! Dama bason Ya Al’ameen d’in kike ba?”
  “Ina sonsa auren ne banaso.”
  “Kinga banason shashanci kina jina ko? Auren ki nanda 3 months ba abinda muka fara gobe zamu wuce Kano chan za’ayi maki siyayyan, kinji koh? Seki fara shiri.” Shiru Zeezee bata amsa ba. “Bada ke bane?”
  “Dani ne.” tayi murmuring. Washegari suka biya ta air to Kano achan suka gama wa Zeezee siyayya, kud’i in abundant Baba ya bawa Mama ba abinda basu sai mata ba. A guest house na Baba aka sauk’e kayakin kasancewar har yanzu Zeezee bata yanke hukuncin wani gari take so ta zauna ba.

  _Morning hours..._
  Tana zaune a d’akinta damuwa sun mata yawa wayarta ya shiga ringing acewarta ma Lubiee ce tana kai dubanta taga Al’ameen wani dogon tsuka taja haka tana gani har ya yanke bata d’aga ba se a karo na biyu. “Hello My Princess” kamar wacce baza tayi magana ba tace, “na’am ina kwana?” sede daga yadda tayi maganan yagano da akwai matsala “any problem Zainab?”
  “Babu” tayi stating sama-sama.
  “Are you sure ko auren ne bakiya so a fasa?”
  “Eh” ta fashe mai da kuka.
  “A fasa?” yasa dariya.
  “Am serious Allah dan Allah karka rabani da Mama da Baba kuma ka bar min dariya.”
  “Toh nadena theres nothing to worry kinji? I’ve got you Zainab, I love you so much.” Wani haushinsa ta sakeji sannan dan dole tace, “thank you.”
  “So kinyi making up mind naki? Zaki zauna a Kaduna a family house kokuma anan Bauchi alone ke kad’ai? Kinsan a Abj nake aiki Kaduna is more closer and zanfi samun visiting naki frequently.”
  “Chabd’i! A family house? Nice zan zauna da in-laws? Lallai kuwa! Ka sake tunani”
  “Excuse me?” Yayi maganan suprised. Ita kanta Zezee batasan lokacinda tayi maganan ba. “Uhm Ya Al’ameen I mean zama da in-laws d’innan gaskiya bana so problems yake haddisawa.”
  “Trust me, my family don’t have that problem.”
  “I know kawai nice banaso gomma nan Bauchin ina kusa da Mama kai kuma koda jifa jifan ne kana visiting d’ina its okay by me.”
  “Are you sure?”
  “I am ”
  “Toh shikenan hakan za’ayi, I love you.”
  “I know, thanks.” Tunda Al’ameen yake be ta6a jin Zeezee tace mai I love you ba amman dake shiyasan yana sonta ne don Allah badan wani abu ba be ta6a damuwa ba.
  “Toh semun sake waya, take care.”
  “Bye” tayi hanging take ta kira Lubiee.

  “Hello Matar Soja” cewar Lubiee.
  “Babe ya zanyi dan Allah? Taya zan fara sanar da Adeel aure na is in three (3) months time? I really dunno how please help me out.”
  “Kefa Zeezee banza ce wallahi, forget Adeel wallahi Ya Al’ameen loves you.”
  “That will be the last thing I’ll ever do kefa bakisan yadda nakeji da Adeel bane.”
  “Toh ya zakiyi yanzu? Kinason na fad’a mishi ne?”
  “A’a please don’t zan fad’a mai da bakina.”
  “Toh suit you well ni ya batun ashobe ne? Wanda muka fitar d’in sunyi?”
  “Yeah leave that to me wallahi kap ashoben Ya Al’ameen ne ze biya tunda shi yace yana sona.”
  “Haba! Zeezee set ukun duka zakice shi? Pity him mana.”
  “Shi yayi pitying d’ina ne daya kama yace yana sona seya auren? Ki ajiye kalman pity agefe friends d’in duka ku nawa ne?”
“Mu 18 ne.”
  “Tam karku damu kede kawai ki sanar musu a group namu na LYS STARS kan in three weeks time suzo su karb’i ashobensu gidanmu.”
  “Toh Matar Soja! Angama.”
  “Mschwww! Banza kawai” tayi hanging. Al’ameen ta kira and har ya tsinke be d’aga ba kasancewar bai kusa, itama missed call d’aya tamai dan iskanci.

****
  Da daddare ta sake trying nasa be jima ba ya d’aga “hello My Princess you called earlier bana kusa sorry.”
  “Its okay dama batun ashoben friends d’ina ne a kace na tuna maka.”
  “Okay, nawa kike buk’ata all in all?”
  “Kaga friends d’ina are 18 in number each person kuma ten thousand five hundred (N10,500) ne making one hundred and eighty-nine thousand (189,00) altogether.”
  “Okay zan baki 200k incase kinsamu additional friends.”
  “Tam sekuma na makeup artist, nida Lubiee kad’ai za’a mana.”
  “Shikuma nawa?”
“Nawa 60k na Lubiee 25k through out the 5 events all together is 425k plus na ashoben making 610k.”
  “Wow! My Zainab is such a great mathemathecian zan miki transferring 650k hope thats all koh?”
  “Eh shikenan and karka min ta acct na Mama kayi ta nawa.”
  “Toh My Princess anything for you shikenan?”
  “Eh shikenan for now.”
  “Okay feel free to call me up whenever your need arises.”
  “I’ll thanks” tayi hanging. “Baho ai seka tsiyaye wallahi mschw ni yanzu ta ina zan fara sanar da Adeel for God’s sake?” Tana cikin wannan tunani alert na 650k ya shigo wayanta maqirin murmushi ta saki.

    3 WEEKS LATER (2 months one week to Zeezee’s wedding) LYS GROUP CHAT.
Lubiee; _Announcment! Babes y’all invited zuwa gidansu Zeezee yau kuje ku amshi ashobenku kala uku which is worth N10,500. Ba a buk’atan kud’inku saboda Soldier’n mu which is our ango to be yariga ya saya muku._

  Sumayya; _what?! You mean to say Zeezee zatayi aure? Tsaya wata Zeezee tukuna?_

  Miss Aysha; _help me ask o bangane wata Zeezee ba nima._

  Lubiee; _Zeezee nawa kuka sani a garin Bauchi? Zeezee Isma’il Yosouf FYI in ashoben ne bakuso a baiwa wasu, mschww!_
 
   Miss Xoxo; _weehoo!! Kuce angon namu DON ne ashoben N10,500 ya siyewa kowa?_

   Lubiee; _abinku da Maj-Gen! So sekunzo wacce batazo a yau ba za’a baiwa nata ma wata._

  Sumayya; _LOL sekun ganmu toh su Zeezee amarya muna jiran pre wed._

  Ilhamerh; _kefa gulmanki ya miki yawa Sumayya angon kike son gani kome?_
 
  Mjay; _barta deh shegen gulma ne da ita._

  Sumayya; _no bayan cika bakin da tayita yi kan seta gama degree tayi aure ne ai nakeson ganin wazata auran wait guys ina Adeel nata fah?_

  Rumaysa; _kema kinsan Zeezee bazata auri gaja anyhow ba ko bakiji Soldier bane?_
 
  Lubiee; _ke wallahi Sumayya gulma ya miki yawa mschw! Ba wanda yasan destiny’n sa kuma thank god ma had’ad’d’en miji zata aura wanda yafi Adeel_ pic na Al’ameen ta musu sending ai sam Sumayya da k’awarta Ameena suka k’i amincewa da wannan kyakkyawan soldier’n ne mijin Zeezee don black belle.

   Miss Aysha; _can’t wait!!!_

   *~ *~ *~
  Da yamma friends na Zeezee suka hallaro amsan ashobe, bikin Zeezee de yazama talk of the town sabida basu ta6a jin bikin da ango yayi ashoben 10,500 wa each friend ba. Har rana me kaman na yau Adeel besan me ake ciki ba as Zeezee bata sanar dashi ba bekuma ji rumor a gari ba.

 


*© MIEMIEBEE   Team #YGC!*
👄👄👄👄
   wwww.beeenovels.blogspot.com

4 comments:

Unknown said...

Hmmmmmm

Unknown said...

This novel is killing Me thank you mariam😍😍

Unknown said...

Wooooh! Can't wait for dis aure to happen. 😃😃😃😃 coz i dey pity zeezee

Unknown said...

Wow Enx sis surely #team Maj-Gen