Wednesday, 21 December 2016

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 20

  *December, 2016*




                   ★*★*★*★
Few months later...
    Ba laifi yanzu Zeezee ta d’an maida hankali gun karatu tunda batada wani distraction yanzu dan tun ranan da sukayi exchanging words da Ammar word be sake had’a ta da shi ba, ko sun had’u a school sede suyi burning face suyi passing juna dama seda Lubiee ta gaya mata ta guji Ammar d’an iskan guy ne tak’i. Preparation na 3rd term exams nasu suka shiga yi which will take place in a week time! Biology teacher’n su na fita Zeezee ta koma seat nata da Lubiee ta zaro wayan Lubiee suna hira tana kallon pictures. Kawai coming across the most breath takingly gorgeous guy ever tayi, shi gashi nan kaman balarabe dan kyau, komi a fuskansa beauty off neh I don’t have to go in details! sede ba fari bane skin nasa na nan wane na buzaye ya had’e iya had’ewa ga kuma swags uwa uba. Rikicewa Zeezee tayi gun gabad’aya har tana manta yadda ake breathing. “O my GEE! Lubiee don’t tell me wannan guy is for real.”
  “Wai waye kike wannan exageration haka, muga” Tayi maganan tana kar6e wayan “aww wai Adeel?”
  “Don’t tell me thats his name.”
  ”It sure is.” Chinyan Lubiee Zeezee ta buga friendrily “don’t tell me kinsan sa please.”
   “LOL nasan shi mana, brother’n sister in-law na ne (k’anin matar yaya na.)
  “OMG! I’ve fallen wallahi, dan Allah aina yake?”
  “Ke Zeezee me haka? Ki dena ba dani please da kinsan halinsa wallahi bazaki fad’i haka ba.”
  “Inma kankat ace yankan kai yake ina? Toh ni yamun ko a hakan wallahi I love him. Jifa yazo dai-dai da zama gashi dama am single, tell me he is also please.”
   “Ke wallahi inhar baki nitsu ba ban baki kowani info. akanshi.”
  “Toh na nitsu meh IG handle nasa?”
  “Adeel_Hussain amman he is private.”
  “Damn it! I can’t follow an unknown guy” Zeezee ta buga hannun ta kan desk. “Kiban details akansa please.”

      “LOL okay, here we go. His name is Adeel Hussain like I told you, he is a brother to my sister in-law, same Mom and Dad. This year ya gama karatun shi a Florida in accountancy, his dad is filthy rich amman ya jima da rasuwa. Facaka da kud’in gadonsa yake Mom nasu kuwa bata ce masa komi wai shine last born. Duk abinda yake bata ce masa ko uffan hakan yasa ya zama tantirin d’an iska, first class certified one ma. Shiyasa ban shiga harkansa, kullum cikin changing girlfriends yake to cut the crap bayi dating one girl at a time ma, kuma a haka matan suke kai kansu gunsa, mschw! But believe me Adeel ya had’u inde had’uwa ne wallahi.”
  “Innalillahi! Ni wallahi ina sonsa a hakan kimin hanya please Lubiee.”
  “LOL kema kinyi joining queue kenan?”
  “Uwaki keh! Am serious”
  “Yo! Taya zan miki hanyan? Wai bakiji bayanun dana miki bane?”
  “Babe naji wallahi ahakan nake sonsa I can handle him, nayi handling Ammar ma”
   “You sure can’t saboda wannan yafi Ammar trust me d’an banzan zuciya ne dashi.”
   “Aswear I can”
   “Toh naji you can, ya kikeso inyi? Ince mai kina sonsa?”
  “Banza! Taya zakice haka? Ai seya raina ni, nide just hook us up together work your magic Babe I trust you.”
  “LOL toh naji amman nawa zaki biyan?”
  “Yanzu Babe kud’i zaki karb’a waje na? Haba what are BFF’s for? Allah banida kud’i.”
  “Chabdi!” Lubiee ta galla mata harara “22k da kika karb’a gun Sumayya fah?”
  “Toh naji zan baki 3k ciki.”
  “A’a wallahi ya kasa 6k nakeso ko na fasa yin hanyan.”
  “Shegiya mayyar cash wallahi dan shi kawai zan baki amman se kinyi hooking namun tukuna.” Lubiee na dariya tace, “whatever way na yarda.”
   “Its a deal!” Zeezee tayi exclaiming tana k’ok’arin sending picture’n Adeel to her phone via whatsapp.

    *~ *~
  Tun ranar da Zeezee sukayi wannan magana da Lubiee take sa rai Lubiee zata kirata tace mata the did is done. Everyday sede basu had’u da Lubiee ba seta ce mata ya how far? Kullum kuwa amsan d’aya banje gidan Ya Salman ba kokuwa Adeel bezo gidanmu ba. Ahaka har su Zeezee suka gama exams nasu ranar karb’an result as usual suka sha kwalya aka ta d’aukan selfies.

_2 weeks later, gidansu Lubiee._
  Sanye take da fitted gown lace kanta bako d’ankwali, bayan ta fito daga d’akinta da baby sister’n ta tayi making way nata to Ummi’s parlour, achan ta tarar da Adeel zaune kan 2 seater as always yadda ya saba ya mik’ar da dogayen k’afafunsa kan centre table yana latsa wayarsa. Sanye yakeda black ¾ trousers da white T-shirt. Ita ta rasa ya akayi jinin sa ya had’u da Ummi wani sa’in har kiransa take wai yazo ya tayata hira sekace batada yara. Ko uffan bata ce mai ta nufi dining space ta d’au ruwa dai-dai nan Ummi ke fitowa daga d’akinta “sannu Ummi” Lubiee tayi greeting nata cike da ladabi, se anan Adeel ya d’ago kai yana kallonta. “Yauwa Lubiee daman kina ciki ne? Seki taya baban nawa fira zan d’an shiga nan gidan Maman Islam will be back soon.”
   Neman excuse Lubiee ta shiga yi dan she can’t take rainin hankali irin na Adeel, “uhm Ummi daman fa yan-” saurin katse ta Adeel yayi, “ohh no prob Ummi sekin dawo.”
  “Yauwa Baba na na tafi toh” tana kaiwa nan ta fice. Tsaye Lubiee tayi gun sannan daga bisani tayi texting Zeezee _emmata you won’t believe this! Adeel na gidanmu right now come ASAP it might be your biggest chance!_
 
***
   Zeezee na zaune gaban dressing mirror’n d’akinta, ta gama cancare kwalya tasa wata light purple english gown se killing selfies take taga saqon Lubiee ai ba tare da b’ata lokaci ba tayi replying _right away Baby!_ d’akin Baba ta nufa tace mai akira Omar ya kaita gidansu Lubiee. In less than 20 minutes ta isa.
***
   “Ke prob d’ina dake k’auyenci Luba” cewar Adeel mockingly.
  “Banaso kadena cemin Luba!” Tayi stating angrily “and bani waya na ma.”
  “I know where this is going Baby sis, you like me don’t you?”
  “Mschww!! I aiint got your time bani waya na.”
  “Gashi dillah! And please da wani kalan friends kike hanging out? Gabad’aya ba Babe data min.”
   “Bayan Babes da kake da you are still searching for more?”
  “Trust me duk na basu red card yanzu” yayi maganan yana takan viewing photos yazo kan wani pic na Zeezee data baza gashinta kan pillow tana a kwance, tayi pouting mitsitsin bakinta, dai-dai nan take shigowa parlour’n k’amshin turarenta ne ya mamaye gun gabad’aya tare su Lubiee suka juya suna kallonta. Ita kanta Lubiee tsayawa tayi tana kallonta, daga bisani ta mik’e taje tayi hugging nata “Babe you didn’t tell me you were coming.” Tayi maganar yadda Adeel zejita.

   “I thought I might suprise you, so how are you?” Cewar Zeezee cikin wani muryan da ban ta6a saninta dashi ba.
  “Mu k’arisa ciki toh.”
  “Nahh muje room naki it’ll be more comfortable there.”
  “Okay toh Adeel hand me over my phone my BFF is here” tayi maganan tana dosan inda yake. Sanda ya k’are wa pic d’in kallo sannan back to Zeezee again ya tabbata itan ne ya mik’a ma Lubiee wayar. D’akin Lubiee suka zarce “ke Babe you killed it! Kinganki kuwa? Duk kwalyan nan masa ne?”
  “Believe me da nasan tuni yana nan senayi makeup dayafi wannan kyau.”
  “Ke guy d’innan is fire kiganshi! Omg! Allah sa he’ve noticed me.”
  “Ai da kin bari mun zauna a parlour’n so that ya k’are ma beauty’nki kallo da kyau.”
   “Ina Ummi? Ko zamu koma ne?” Cewar Zeezee all confused.
  “Na yaushe kuma? Kin kopsa a-” bata k’are maganan ba idonta yakai ga kan screen nata “omg! Wallahi picture’n kima yake kalla a wayana, Babe you nailed it!”
  “Kamar ya what do you mean?”
  “Gashi pic naki yake viewing a phone d’ina kin mai wallahi!”
  “Don’t tell me please, wani pic? Allah yasa toh” ko good 20 minutes Zeezee batayi ba tace zata tafi nan ma seda suka sake komawa parlour’n seyi suke kaman sunje shan ruwa ne daga nan ta tsari napep ta dawo gida. Adeel na ganin Lubiee ta dawo daga rakiya ya fita tare da shan gabanta. Ita kuwa knowing this was coming seta wani burning face “ya da haka Mr. Player?”

   “Oh common Baby sis don’t call me with this name a presence na Babe d’incan.”
  “Wace kenan?”
  “Your BFF, the one that left just now.”
  “Aww you mean Zeezee? Toh kona kiraka da Mr. Player a gabantan ma so what? Its not as if she’s your girlfriend.” Smirking yayi ta one side of his face sannan yace, “she’s not but will soon be.”
  “How?”
  “Through my Mr. Handsome magic” yayi maganan yana shafa sajensa “kema kinsan all girls I mean all fall for me at once and I’m very sure your friend did also ko ba haka ba? Tace miki kiyi hooking namu up didn’t she?”
  “You are crazy Adeel, to ba haka bane, Zeezee don pass your class excuse me.”
  “Inhar haka ne dare me and give me her phone number.”
  “A dalilin me zan baka number’n BFF d’ina? Saboda kayi toying da precious heart nata and leave her heartbroken kamar yadda ka saba?”
 “Common Baby sis, lets not make this hard on ourselves. Ke kin samu ma ina tambayan digits na friend naki, you know it happens just once in a lifetime ban tab’a tambayan digits na wata Babe ba se ita.”
  “Dole ai ka tambaya saboda ita ta kai ne, not like your other hoes”
  “Then give me.”
  “I shan’t, shegen feeling d’in tsiya wai yazo tambayan abu amman yana gasa wa mutum magana.”
  “LOL you are afraid I will win over her heart in just 24 hours kenan.”
  “No ba haka ba- ”
  “Then give me her digits” ya katse ta. Haushi ne ya cikata, batasan a lokacinda tayi mai dictating number’n ba offhand.
  “Good girl wait for tomorrow kiga I’ll be going in Ummi tazo kice mata na tafi.”
  “Mschw! Nak’i bazan fad’a ba.”
  “LOL don’t be jealous Baby sis” ya kama d’aya daga jelan gashinta yana wasa dashi, “zan had’aki da cousin d’ina Fahad.” Fisge kanta tayi “ce ma akayi nayi kwante ne? Argghh!” Ta watsa mai harara sannan tabar gun. Shegen murmushinsa ya saki sannan ya nufa E-class nasa ya fice.

***
  Zeezee de tun isarta gida take jiran call from Lubiee. Not long enough ta kirata ta irga mata yadda sukayi da Adeel sannan taja mata kunne kan no matter what she should not say yes to him today tabari seta ja mai class if possible fiye da yadda ta jawa Ammar ma amman inaa abin ba haka take ba ta side na Zeezee jinta kawai, ita batak’i ma itace tacewa Adeel tana sonsa ba inhar he’ll say yes right away.

  _9:20PM_
   Tana miqe bisa gado taga incoming call from new number tsalle ta daka gun tsabagen murna har ta mance ya ake answering phone call. Seda ya kusa ending ta samu ta d’aga tare da yin shiru shima Adeel d’in shiru yayi se chan yace, “halo Zeezee on the line please?” cikin sark’ak’k’iyar muryarsa.
  “Yy... Yes.” tayi stammering.
  “Cool pretty girls digits are really hard to miss.”
  “Uhmm.. Who’s it?”
  “Don’t worry Pretty you’ll get to know me soon, so remember the handsome guy you saw earlier today at your friend’s residence?” Shiru Zeezee tayi tana nazarin tace eh ne ko a’a finally tace “no.” Deep breath sarcastically Adeel yaja ya saki yace, “woah! I never knew handsome faces can be ignored, Pretty you musn’t lie I know you saw me.”
  “You’ve got some nerve you know.”
  “LOL so kin yarda kin gannin? Ko sena miki describing kaina zaki tuna? Well, I’m the gold skinned, handsome, tall looking dude at your friend’s house earlier today.”
  “LOL you keep on saying you’re handsome bayan ni banga handsomeness d’inba.”
  “Gosh! Don’t make a sin both you and I know am handsome and ahh! Kin ganni kenan tunda kince bakiga handsomeness d’inba.”
  “If I must admit, yeah I saw you.”
  “Hah! I know right. So that aside, I’m Adeel Hussain” nan ya bata details about him bayan daya gama ya buk’ace ta da tayi itama. Sun gama introducing juna yayi clearing throat nasa, “so Pretty I won’t lie, actually your personality and cuteness got my attention today in bazaki damu ba I will like us to be...” Se kuma yayi shiru Zeezee ta k’osa taji me zece.
   “I will like us to be friends if possible” Ihu ne kawai Zeezee bata saki ba just friends? Ita girlfriend nata takeson zama ba friend ba, ina ma zata iya fad’a mai.
   “Halo Pretty you there?”
  “Uhm yeah.”
  “So what do you say?”
  “Sure why not? Request accepted.”
    “As expected thanks tho.”
  “you’re welcome.”
  “I’m single and you?”
  “I am too” ta amsa batare da tasan taya ba.
  “Cool so after graduating where do you wanna proceed your studies to?”
  “ATBU in shaa Allah.”
   “Oh wow, we’ll get to be in touch kenan.” Hira sama-sama suka tab’a. Itade Zeezee duk ranta a b’ace yake suna gama wayan ya jira tayi hanging sannan ya saki wata mak’irar murmushi “you’ll have to beg for my love Zeezee.” pencil nose nasa yaja sannan ya koma kan gado ya miqe.

  *~ *~ *~
   Haka nan tun daga ranan suka soma waya jifa jifa, Adeel seya jera kwana hud’u be kirata ba, ita kuwa batak’i ace 24/7 suna waya ba. Gashi kota ce zata kirasa se taji baza ta iya ba gudun karya bonsa ta. Bayan nan ga kuma yadda Lubiee ke mata warning kullum kan she should play hard to get to him. Chatting ma sama-sama sukeyi nan ma se a snapchat akwai sanda tamai magana a whatsapp yana gani yak’i replying back koda yazo ya kirata daga baya kuma take cemai why did he ignored her message. Arrogantly yace mata he wasn’t in the mood of replying messages at that instant. Haka fa har watanni biyu suka shud’e ba improvement a relationship nata da Adeel. Ko wuqa za’a sa mata a wuya bazata iya fad’in kalan relationship dake existing between them ba, saboda they are morethan friends from the way yake calling nata da pet names da kuma yadda yake acting amman kuma they are not in a relationship saboda har sau biyu yana kawo mata case da girlfriends nasa kuma haka zata danne zuciyarta ta basa shawarwari. Sede batasan meh ba ita duk kalan mazan da suke cewa suna sonta ta kasa accepting nasu duk in sunzo korasu take tace tanada saurayi, ta rasa dalilin hakan bayan gashi de bawai they are in a relationship bane da Adeel toh why? She can’t answer.

  2 weeks back da taje wani biki suka had’u da Adeel. To her suprise yak’i kulata, infact yi yayi tamkar besan taba ma. Abun ba k’aramin ci ma Zeezee rai yayi ba dan har kuka seda tayi. Ita kanta tasan mahaukacin so take mai amman until when zece mata yana sonta? Bayan faruwan incidence d’in bata sake yi ta kansa ba 2 days later ya kirata sede daga yadda take mai magana yagane bata tare da walwala, daya tambaya kuwa bata b’oye mai ba ta fayyace mai komi to her suprise taji ya k’yal-k’yale da dariya yake ce mata is she jealous? Ai ba saurayinta neba shi bale don ya shareta yaje ya kula wata taji haushi shi gaskiya baya son haka they are just friends ba ruwanta da dating life nasa. Kuka Zeezee tai tayi har seda garin Allah ya waye ta kira Lubiee take irga mata yadda Adeel ke affecting nata like an infection or rather disease.
  Adeel d’an iska kuwa duk da gan-gan yakeyin wad’an nan abubuwa. So yake ya gama toying da heart nata, ya zama he is the only one she wants kafin nan yace mata yana sonta.

  ** **
   Su Zeezee sun shiga Ss3 bada jimawa ba Adeel yayi asking nata out kan will she be his girl? Ita kanta batasan a lokacinda ta amsa mai da ‘yes’ right away ba. Tun daga wannan rana rayuwar Zeezee ta canza komi Adeel, kullum tana cikin snapchat tana mai sending videos da pictures. Books nata na school gabad’aya sunan shine kota ina. To cut the story short ko zaune take ita kad’ai muddin da biro a hannunta toh believe me sunan Adeel zata hau zanawa a hannunta. Password nata na laptop, waya, ipad komi Adeel, snapchat handle nata da whatsapp name ma ‘Adeel’s Very Own’ ta miyar. Haka wallpapers nata ma duk killer pictures nasa ne. Zeezee can die for Adeel hakan yasa yake mugun bata wahala, abu kad’an ya hau mata zuciya kokuwa masifa, ko kiranta yayi bata d’aga da wuri ba seya hau k’orafi. Shi ya iya sa pictures na friends nasa mata a dp aman ita koda dan wishing na male friends nata happy birthday ne ya hanata. Sam se yace wai she is cheating on him.
  A haka fa suka samu sukayi one month in a relationship. Cikin wata d’ayan nan akwai sanda Adeel yayi sati be kiran Zeezee simply because yaje school nasu ya tarar da ita tana hira da friends nata maza. Cikin satin nan har ramewa sanda Zezee tayi kullum cikin sending mai apology and ‘I love you’ messages take amman hakan besa ya ragar mata ba. Dan haka yanzu tama bar kula mazan class nasu se in ta kama. Ko liking pictures na instgran boys followers nata ya hanata amman yana chan shi har commenting yanayi a nasa na female friends d’in. Zeezee de bata tab’a shiga tashin hankali irin wannan ba a rayuwarta, Lubiee kullum cikin nadaman had’asu da tayi take. Duk kalan masifa da tsiwa kalan na Zeezee when it comes to Adeel bata iya gaya mai koda maganan banza ne, koda ita ce da laifi ita ke basa hak’uri.

   _Nide Miemie nace Allah ne ya soma kamata tunda ta iya raina mahaifiyarta da yayyunta._

             



*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com

6 comments:

Anonymous said...

Ai tukunna ma

Unknown said...

Wasa farin girki

Unknown said...
This comment has been removed by the author.
Unknown said...

salaam Sis, Hope you are OK cos kwana biyu ba post? Allah Ya Kara afuwan jiki ameen

Unknown said...

Allah dai ya shirya mana da zeexee n baba

Unknown said...

God don catch her. Sauran babanta