Wednesday, 21 December 2016

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 19

  *December, 2016*


      Washegari bayan Ibraheem ya sauk’e Zeezee a school ta tuna da mantuwan TD assignment nata datayi a gida, ga teacher’n mugu ne baya sauraron excuses. Form teacher’nsu tanema tamai magana ya had’ata da Baba a waya tamai explaining komi. Suna cikin yin second period nasu Ibraheem yashigo class nasu bayan excusing kansa da yayi. Sanye yake da T shirt me long sleeve arms da not too tight pencil trousers, yayi matuk’ar yin kyau ai tuni ‘yan matan class nasu Zeezee sukayi falling masa cikin k’asaita kamar yadda ya saba gudanar da ayyukansa ya k’arisa cikin class d’in suka gaisa da malamin sannan ya bawa Zeezee drawing natan yayi ficewarsa. Ai ana fita break ‘yan matan class nasu Zeezee da wanda suke mata magana da wanda basu matan sukayi layi a seat nata “wai meh haka? Ku matsamin mana ko bakuga an fita break bane?” Zeezee tayi stating angrily.
   “Zeezee don’t tell me that Hottie is your brother?!” Matan class nasun sukayi exclaiming almost at thesame time.
   “Ba brother na bane naku ne ai aikin banza, matsa mun nikam.”
   “Please ki tsaya muyi magana” cewar Lieemarh “wallahi yayi min nikam omg! His skin!”
   “Skin ja kaman tsuliyan birin? Lallai kam matsa min mana ku!”

    “Dan Allah meh IG handle nasa Zeezee?” Mjay ta tambaya.
   “Wai tsaya son Ya Ibraheem dukkanin kun nan kuke wai?” Tayi pointing nasu da yatsa.
  “Eh ni wallahi yamin.” said Hajara. Dariyan rainin hankali Zeezee ta saki “Lubiee kinaji wai Ya Ibraheem suke so, wai lallai kam kun tashi a aiki excuse me now, will you?” Nan suka matsa mata suna fad’in “kije ki dawo ma tona.” Ta kai da bakin k’ofa kenan mortal enemy’nta a class d’in wata Sumayya wanda Babanta ke mugun ji da kud’i har mota ya sai mata. Ko kad’an bata wa mutane magana dan haka basu shiri da Zeezee dan itama ‘yar iskan kanta ce. “Zeezee we need to talk please” tace da Zeezee.
     “Sumayya ko? Aww! Dama kina wa mutane magana? LOL toh I aiint got your time matsa min.”
  “Please Zeezee lets keep our differences aside wallahi ko me kikeso zan miki just listen to me.”
  “You have two minutes to do so.”
   “Its about the guy that came earlier waye shi?”
  “Wanne? Be precise please kina b’ata min time” Zeezee tayi maganan as if bata gane Ibraheem, Sumayya ke nufi ba.
   “The tall, fair and good looking one daya kawo miki TD drawing naki.”
  “Aww you mean my handsome brother, what about him?”
  “Nothing really you mean he is your brother?” Ta tambaya kinda shocked.

   “Ban kai na zama sister’sa bane kome kike wani zaro idanun nan naki waje haka.”
  “No ba haka bane, abin ne yazo min da sauk’i I don’t need to suffer.”
  “Like I don’t get you kuma kina b’ata min lokaci.”
  “My apologies, dama bawani abu bane digits nasa nake buk’ata.” Dariya Zeezee da Lubiee sukasa harda tafewa, “you mean digits na Ya Ibraheem?”
  “Owww what a lovely name eh na Ya Ibraheem d’in.”
  “Lallai ko kinyi kad’an na baki digits nasa, dana baki gomma na bawa su Salmah.”
  “Please Zeezee lets talk business ki fad’an ko meh kikeso zan baki inhar zaki bani digits nasa in return.”
  “Like money?” Tayi maganar tana lasan lips nata.
  “Eh wallahi ko nawa kikeso.”
  “Interesting Lubiee deal ya taso, kibari yanzu zanje shop in na dawo we’ll discuss it.”
  “Okay am grateful Ameenah lets go” tace da k’awarta suka fice.

  *~ *~
   Zeezee na dawowa daga shop ta tara ‘yan class nasu da sukayi falling wa Ibraheem gu d’aya sannan tayi clearing throat nata ta soma da cewa, “so all of you here have fallen for my handsome brother kuma kunason digits nasa ko? Cikin ku takwas (8) d’innan mutum d’aya zan baiwa.”
  “Zeezee ni please” cewar, Ashnur da Xarah.
  “Ai ba daganan take ba girls, sayar maku da digits nasan zanyi.”
  “Ki fad’i ko nawa ne am ready to pay” Sumayya tayi stating arrogantly.
  “Good I like that, so out of the eleven digits each number contains, kowani digit d’aya N500 altogether making five thousand five hundred (N5,500) kenan who will pay?” Ai kap suka d’aga hannu dake duk ‘ya‘yan masu kud’i ne ‘yan k’arya kuma. Ganin haka Zeezee ta k’ara deal d’in zuwa one thousand (1,000)  nan ma kusan duka sun d’aga hannu haka tayita raina musu wayo har suka iso two thousand inda Sumayya kad’ai ta d’aga hannu.

    “Tam Sumayya kece winner ke zan bawa number’n Ya Ibraheem that is after I get to see my tewnty-two (22) thousand.”
  “Toh ai kinsan bada kud’i dayawa nake zuwa school ba but trust me gobe zan kawo miki kiban contact d’in.”
  “Uh-uh Babe, I don’t play that game, pay before service kina bani kud’i na ina baki digits nasa” haka Sumayya ta hak’ura a washegari ta taho da 22k pil cikin envelope ta danka wa Zeezee ita gata shegiya ‘yar gidan minister nan Zeezee ta bata number’n Ibraheem not minding the consequences.

   _Da La’asr._
   Baba na zaune a parlour da friends nasa suna hira, Zeezee ta shigo bako sallama bale gaisuwa ko sannu, wajen Baba ta nufa direct ta tsaya akansa “ya akayi K’anwata, lafiya?” Kai ta kad’a nufin a’a.
   “Toh baki gaishe da friends d’ina ba.”
  “Ina wuninku Uncles?”
  “Lafiya Zeezeen Baba” suka amsa in unison almost about 5 of them.
  “Yauwa to meneh neh?”
  “Baba pad d’ina ya k’are kabani kud’i na sai sabo.” Kunya sosai Baba yaji tamkar ya nitse k’asa, dama seda Mama ta gaya masa yayi a hankali wataran se Zeezee tamai abin kunya amman yak’i jinta ya mata kunnen shegu. Ga irinta ai yau!
  Bending nata yayi dab da kunnenta yace, “haba K’anwata bazaki jira se friends nawan sun tafi ba tukun?”
  “Toh ai zanyi staining kaya na.” wani abin kunyan again! Cike da mamaki friends nasan suke kallon Zeezee “excuse me please” cewar Baba tare da jan hannun Zeezee izuwa d’akin Mama.

    Koda Mama tagansu bata ce komi ba se kallonsu kawai take, “haba Zeezee! Meh amfanin hakan? Bakiga inada bak’i bane?”
   “Ya meya faru haka?” Mama tayi speaking up finally.
  “Muna zaune da friends d’ina taje wai na bata kud’i ta sai pad.”
  “Ahap! Ban fad’a maka ba dama ka guji rana kamar ta yau? Tunda Allah yayi ina raye duk lokacin da take buk’atan abubuwa haka tazo ta sameni tamin magana sam kace kai ba haka ba, duk abinda take buk’ata ta sameka ta maka magana, kad’an ka gani ai wataran cewa zatayi kasa mata inde Zeezee ne expect more wallahi.”
  “Toh ya isa haka! Ni nake gama wallahi bakinki yake kama mu, kullum sede bakiyi magana ba se abin ta faru, dan Allah daga yau inkin san bazaki fad’i alkhairi ba kija bakinki kiyi shiru.”
  “Kanku akeji kai da ‘yar naka da bata da kunya.” Kuka Zeezee tasa wai Mama tace mata batada kunya da k’yar Baba ya samu tayi shiru “amman kema karki sake tambaya na stuffs haka in public kinji?”
  “Koda zanyi staining kaya na?”
  “A’a ni bance haka ba what I mean is nan gaba in na cikin mutane ki kirani gefe kinji?”
  “Toh naji.”
   “Yauwa K’anwata Allah miki albarka” yayi maganan tare da zaro 5k daga wallet nasa, “ungo toh in cenji ya rage ki d’auka na baki.”
  “Toh nagode” tana kaiwa nan ta fice.
  “Hmm kaide inba kuka Zeezee ta saka da hawaye ba bazaka tab’a yin hankali ka soma ganin laifinta ba.”
  “Kanka akeji” yana kaiwa nan ya bar mata d’akin.

_8:45PM_
   Ibraheem na mik’e kan gadon d’akinsa yasa earpiece a kunne yana d’anjin beats, kira daga new number ya katse mai waqansa bayan daya duba yaga fa besan lamban ba seya k’i d’agawa se a karo na biyu “Halo” Sumayya tace cikin wata karuwar murya sekace ba ‘yar 16 years ba.
  “Yes Hello” yayi speaking finally.
  “Uhm Ibraheem ne please?”
  “Yes shine.”
  “Ohh thanks Gee! Am Sumayya by the way, I know baka gane wacece ba ko nace bakasan wacece bama thats why I need to introduce myself.” Har anan sauraronta kawai Ibraheem yake totally specheelss, bayan data gama bayanin kantan yaji ma ashe yarinya ce sa’ar k’anwarsa na chan baya-baya.
  “So little baby dake a ina kika samu digits d’ina?” ya tambayeta finally.
  “It doesn’t matter ni kawai kabani dama na fad’a maka meke tattarre dani.” Murmusawa yayi ya sake mik’ewa kan gadon “meke tattare da ke ‘yar yarinya?”
  “Right from the moment my eyes decended akan breathtaking face and body naka heart d’ina yayi skyrocketing, I don’t know how to explain it to you but the truth is I’ve fallen for you and I love you.”

   “Woah! You’ve got such confidence, kafin nan answer me aina kika samu digits d’ina Zeezee ce ta baki?”
  “A’a ba ita bace.”
  “Don’t lie to me kikayi hakan you’ll just ruin yourself and make me hate you.”
   “Yes itace, but it does-” bata kaida idda maganan ba yayi hanging wayan tare da mik’ewa a fusace yaja belt nasa dake rataye jikin wardrobe yabar d’akin sena Zeezee gbam! gbam! gbam! Yayi knocking tana cikin irgen kud’ad’d’enta tace, “ina zuwa” da sauri ta miyar tasa cikin pillow case nata sannan ta mik’e ta bud’e k’ofan. “Ya lafiya?” Idanunta na kaiga belt dake nannad’e a hannunsa ta shiga b’ari kafin tayi wani k’wararren motsi ya bankad’eta tare da sa kai cikin d’akin “wayyo Allah Baba na wallahi ze kasheni!” tasa ihu, kota kanta beyi ba yayi locking k’ofan d’akin.
  “What did you do at school today?”
  “Bbb.. Babu.”
  “I said what did you do today?”
  “Ya dan Allah kayi hak’uri” d’aga belt d’in yayi ya shod’eta dashi nace, “what did you do at school today?” Cikin sautin kuka tace, “nn... na bawa Sumayya number’nka amman dan Allah kayi hak’uri wallahi sharrin shed’an ne it’ll never happen again.”
   “Meya kaiki bata number na? Sa’an kine ni? Ko bakida hankali ne?”
  “Wallahi ina dashi Ya dan Allah kayi hak’uri na tuba” sake kai mata wani dukan yayi “wayyo Allah Baba na!” sede duk ihun da take Baba bai gida bale ya ceto ta. “Zan zane ki yadda duk ‘yan class naku suka ganki gobe se sun tambayi meya faru. bayan nan kuma ko aljannah akace za’a baki kibada number na bazaki bayar ba.”
  “Wayyo Allah Baba na Ya dan darajan Allah kay- wayyo Allah na!” Duka yayi mata na k’in k’ari, Mama najin sautin kukanta tun daga d’akinta amman kota damu ta duba ta saboda tasan dole laifi tayi ma Ibraheem.

   Seda Zeezee ta shiga yin amai ya k’yaleta yana huci, “kad’an kika gani ke bawai rashin kunya da fitsara ba? Sekece a kanki akayi wahayinsa ba? I’ll correct your sitting settings, nan gaba zaki sake bada number na wa ‘yan iskan yaran class nakun stupid kawai” yana kaiwa nan yabar mata d’akin. Kuka sosai Zeezee keyi abin tausayi jikinta du yayi shati yayi ja yau ko Allah ya isan ma babu, anan bacci b’arowo ya saceta. Se Asubah da Mama tazo tashinta shirin school ta tashi jikin nata du yayi tsami. Bin jikin nata tayi da kallo sannan taja doguwar tsuka, “mugu kawai Allah ze sak’a min ni makarantar ma na fasa zuwa, haka kawai bazan jeba su Sumayya su san duka Ya yamin ba” tana kaiwa nan ta ja comforter ta cigaba da bacci.

   6:50AM Ibraheem ya gama shiri yau, 5 minutes to 7pm ya lek’a ko Zeezee tagama shirin itama, gani yayi ba kowa a parlour don haka ya tambayi Mama kota ga Zeezee. “Ni ban ganta ba, ga can breakfast nata Yasmeen ta had’a mata bata fito taci ba. Ma meya had’aku jiya naji kake dukanta?”
   “Zagin Fateemah tayi.” yayi mata k’arya dan ma kunya yakeji ace mates na Zeezee suna son sa.
  “Zagi! Toh Allah shirya Zeezee kaje ka dubata a d’aki karta saka latti.”
  “Toh Baba fah?”
  “Yayi tafiya sammako yayi tun 6.”
  “Ohh Allah dawo dashi lafiya toh” da ‘ameen’ da Mama tace ya fice zuwa d’akin Zeezee. Knocking yayi sau biyu “wayene?” ta tambaya sleepishly.
  “K’aniyanki ne bazaki fito bane? Ko sena tafi na barki?”
  “Eh ka tafi ni bazan je school d’inba” k’ofan ya bud’e ya sameta nannad’e cikin bargo tana bacci. “Meh haka?”
  “Nace bazan jeba ka tafi” tayi maganan tana juya mai baya.
  “Dalili?”
  “Ka kama ka faffasa min jikin ne zanje makaranta wallahi Allah ze sak’a min.”
  “Oya maza tashi ki shirya ina jiranki, ji maganan banza sabida jikin ki ya tashi shine bazaki school ba?”
  “Toh so kake naje su Lubiee sumin dariya.”
  “Eh susan akwai me discipline naki a gida tashi nace! don’t let me repeat myself.” K’afafunta tashiga shurewa kan gadon, “ai ba kai kake biya min school fees ba yanzu ni wallahi bazan jeba” ganin ya soma dosan inda taken ta mik’e a guje “oya wuce kiyi brushing ki shirya wankan me sekin dawo kiyi dan kuwa bazaki sani latti ba.”
    “Toh an tab’a zuwa school ba wanka ne?”
  “I don’t care kinsan da hakan kika k’i yi tun d’azu? Oya you have 10 minutes ki gama shiri, wallahi na dawo baki gama ba banga me hanani dukan ki ba.” Yana kaiwa nan ya fice “mugu kawai da wani jan fuska sekace k’osai wallahi akan yaranka da wannan Fateeman zan rama wannan mugunta duka.” Cikin 7 minutes ta gama kwaskware jikinta tasa uniform, kasancewar skirt natan d’an guntu iya saman gwiwarta ne yasa shatin belt na Ibraheem duk ya fiffito yadda da angani ansan dukanta akayi. “Oh! Damn it!” tayi maganan tana bin legs natan da kallo, “yanzu haka zanje su Lubiee su gani su san duka na akayi? What if Ammar ya tambayeni ina nasamu wannan marks da bruises fa? Definately zesan duka na akayi.” Drawer’n socks nata tayi pulling ta shiga neman white leggings nata don rufe k’afafun nata dashi.

   Ba inda bata duba ba amman bata samu ba. Ana cikin haka Ibraheem ya shigo “ina kike?” A zatonsa ma bata shirya ba ganin ta da uniform yace, “Allah ya soki oya mutafi.”
  “Toh ka tsaya mana na nemi leggings d’ina.”
   “Dama kina zuwa da leggings ne, ba anklet socks kike sawa ba? Kina fa b’atamin lokaci.”
  “Ai dama bance ka jirani ba” tayi maganan k’asa-k’asa. Atlast ta samu leggings d’in tasa sannan ta d’an kimtsa face nata suka fito. Dining ta nufa yayi saurin tambayarta “ya haka? Wai karyawa zakiyi ina jiranki?”
  “Eh mana ba kai kace sena jeba.”
  “Bakida hankali, will you get up my friend!”
  “Baba! Baba! Kaga Ya wai bazan karya ba zan tafi school” tayi maganan at the peak of her voice.
  “Thanks goodness Baba bai gida oya mik’e nace kinsan kina jin yuwa kika k’i fitowa ina? Haka da yunwan zaki school” kaman zatayi kuka tabi bayanshi suka shiga mota har suka isa school Zeezee na gun-guni. D’ari biyu ya wulla mata as break money ai atapir tace bazata karb’a ba, ya hanata breakfast ya had’ata da d’ari biyu?! Impossible tense. Ganin zata tara mai jama’a ya bata N500 sannan ta fice bako godiya. Tana isa class aka soma mata kallon bakwai saura kwata, “ya da leggings yau?”Asma’u ta tambaya.
  “Meya miki zafi? Mind your damn business” waje ta nema ta zauna har anan kallonta Lubiee ke, “seriously Babe mesa kika sa leggings yau?”
  “Sanyi nakeji” tayi mata k’arya.

   Not long enough Sumayya da clique nata suka shigo, bayan tayi dropping jakarta ta nufi seat na Zeezee dake ta watsa mata harara tun shigowarta. Kafin tayi magana Zeezee tace, “meh? Meh kuma yau? Leave me alone please.”
  “Oh common Darling don’t talk like that, actually we’ve got a major problem tun jiya nake ta trying line na Ibraheem but yak’i picking atlast ma switching off phone nasan yayi.”
  “And? Seki d’au na Annabawa kiyi hak’uri or what do you expect me to do?”
   “To make me way ofcourse!”
  “LOL make you way?” Tayi maganan tana dariya “just listen to yourself, you know right I can’t force him into loving you right? Win his heart is all you’ve got to do. Now excuse me.” with a nod Sumayya tabar gun. Koda aka fita break kuwa k’in fita Zeezee tayi, da Ammar ya tura a kirata nanma k’in zuwa tayi hakan ba k’aramin b’ata mai rai yayi ba. The whole him?! Dama already yana da side chicks nasa. Kawai Zeezee ji tayi ai Ammar yakai Fiddy school kiosk ya sai mata almost half of the shop, Zeezee deh was left dumbfounded a wajen, Allah Allah kawai take taje gida suyita ta k’ar.

   Koda aka tashi seda ta bari aka d’an wawwatse sannan ta fito Allah ya sota tana fita Ibraheem na zuwa. Suna isa gida ta d’au wayarta ta kira Ammar telling him what he did earlier sucks how could he? Ai kuwa yaro ya haura mata sama a dalilin me zece tazo tace bazata zoba? Itama dama gwana ce ta fannin tashin hankali haka suka k’are da zage-zage. Kaca-kaca sukayi, sukayi breaking up a wajen tace masa they are done sannan tayi hanging akansa exasperating him the more.

 
 

*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com

No comments: