- PAGE 21
*December, 2016*
_Assalamu Alaikum readers/fans, I will first of all like to thank you all for your maximum support and love, I love y'all so very much, INA TARE DA KU forever! So idan kun lura zakuga inda nayi mistake which is common to us all human beings cause we aiint perfect. Tun a page 18 nace Yasmeen tayi aure se kuma a page 19 nasa Yasmeen tama Zeezee breakfast, duk wani me tunanin daya zauna yasan slip of mind ne, we are all human beings sabida haka we are prone to make mistakes so nima se ayimin uzuri. Thank you once more, *TEAM ‘YAR GATA CE #YGC*_
★*★*★*
Cikin sa’a su Zeezee suka samu suka k’are first term nasu suka shiga hutu. Yau ranar ta kasance Saturday tana zaune a gida. Wanka tayi ta shirya tsaf tanason zuwa gidansu Lubiee bayan tagama komi ta zarce site nasu Ibraheem knocking tayi sannan yace, “come in.” Da friend nasa Aleeyu ta tarar da shi bako gaisuwa tace, “Ya inason ka kaini gidansu Lubiee.”
“Driver’n kine ni? Kuma baki iya gaisuwa bane?”
“Toh so nawa kakeso na gaishe ka?”
“Bani ba Aleeyu nake nufi.”
“Nikam zaka kaini ne ko a’a?”
“Zainab ki kiyayeni!”
“Haka kawai sekace wacce bata da abinyi kullum inyi ta gaishe maka da friends, karka kan” tana kaiwa nan ta fice ta hau gunguni “to meye amfaninka a gidan tunda ko kai mutum unguwa ma baka iya ba mschww! ni wallahi kayi kayi aure ma kowa ya huta” d’aki ta koma rai a dak’ule. Data takeson ta bud’e amman tsoron kalan bala’in da Adeel ze mata take, hakan yasa ta fasa bud’ewan ma totally. Daga d’akin Ibraheem kuwa Aleeyu ne ya riga bashi hak’uri kan dan Allah ya kaita unguwan kawai, ba dad’i tagama shiri ace ta fasa fitan. Bawan Allah kam ashe da biyu ne shi wai son Zeezee yake dukda uban rashin kunyar tata.
15 minutes later Ibraheem yaje ya bud’e door na Zeezee “tashi in kaiki zanyi dropping Aleeyu.” Dad’i sosai taji, nan da nan ta kintsa suka fito sede se kallonta Aleeyu yake wanda har cikin jikinta takeji, tsabagen tsoron Adeel da take ko kallonta wani d’a na miji yake setana ji kaman Adeel na ma gun ze mata masifa. Koda suka shiga mota Aleeyu se satan kallonta yake ta mirror ahaka har suka sauk’eta on their way to Aleeyu’s residence yace, “maza wannan sister’n taka fa tamin gaskia.” Brake Ibraheem yaja unexpectedly. “Come again ban jika ba.”
“Zeezee, nace tamin ina so.”
“Zeezeen? Wancan fitsararriyar? Yanzu har akwai d’a na mijin da zece yana son Zeezee?”
“Gani nide ina sonta.”
”Lallai kuwa baza ayi wannan abin kunyan dani ba wallahi ahaka ma ya na k’are da ita bale wai taji friend d’ina yana sonta please ka rufa min asiri, ma me abin so a jikinta please? Yarinya cefa.”
“Haba maza! Kai de kawai kace kana min rowa ne shikenan, ba seka tsaya kana raina min hankali ba.”
“Seriously guy bawai batun ina maka rowa bane, had it been Yasmeen ce ko Mariam kace kana so wallahi I’ll gladly give them to you amman banda wannan fand’ararriyar.”
“Ka dena zaginta haka please.”
“Wai kai bakaga yadda tak’i gaishe ka bane?”
“Ni I don’t care Allah ina sonta.”
“Nide wallahi ba ruwana, kuma inhar kana sona as a friend please back off. In budurwa kakeso zan ma Fateemah na magana tayi hooking naka da ko friend nata ko cousin amman de banda Zeezee kam. I can’t take that raini wai friend d’ina na sonta mschw!”
“Nide tamin wallahi ka bani go ahead kokuwa...”
“Kokuwa meh?”
“Ko kuwa naje na sameta na mata confessing Allah.”
“Dan Allah kaje in ka fasa.” ya fad’a angrily.
“Haka kace?”
“Eh saboda ba bakina aciki.”
“Naji ba bakinka aciki amman bani digits nata toh.”
“Wallahi ban bayarwa kaji na rantse don’t even beg me to.”
“Karka damu zan samu da kaina.” Rai a dak’ule Ibraheem yayi dropping na Aleeyu kan hanya, ya k’arisa dashi ciki ma yak’i. Wajen Fateemansa ya zarce tad’an faranta mai rai sannan ya koma gida waiting for Zeezee’s arrival.
Not long enough ta dawo. Har d’akinta ya bita yayi tsaye a bakin k’ofa yana galla mata harara a yayinda haushinta keta running a veins nasa. Banza dashi tayi tahau rage kayan jikinta, ba ko kunya. “Ke bakida kunya ne? Ina tsaye a kanki zaki hau cire kaya?”
“Aww! Wai dama da mutum tsaye wajen ne? Toh bakayi sallama ba baka kuma yi knocking ba ta ina zan san da mutum akaina? That aside ma naga ai nan d’akina ne ko a d’akinka kakeson inje in cire kayan?” Ganin yayi kamar ze nufi inda take tasa ihu “dan Allah kayi hak’uri kar ka tab’ani na tuba wallahi bazan sake ba.”
“Da yafi miki kam, so nazo nayi making it clear to you saboda bana son raini, duk wanin da kika san na sani yazo yace wai yana sonki ko wani iskancin karki d’au da bakina aciki dan ni ba sa’ar yinki bane count me out.”
“Toh nikuma meya kawo wannan magana yanzu?”
“Am warning you against the future, kar kiga wai dan wani wai shi friend d’ina yace yana sonki kice zaki raina ni.”
“Chab! Allah kiyaye, wasu gajiyayyun friends nakan? Ai kai ma kasan nafi k’arfinsu.” Mac powder’n ta dake kan dressing mirror ya d’aga ya wulla mata se setin goshinta, wajen ta rik’e tana ihu “karki iya bakinki, su waye gajiyayyun?” Shiru ba amsa... “nace su waye?” Ya nufi kanta da sauri tace, “friends d’ina ba naka ba dam Allah kayi hak’uri” da k’afa ya gishimeta “marasa kunya kawai ni na ma rasa abin so ajikin ki wallahi da har Aleeyu ze dage yace se ke. Ma yaushe kika balaga?” Hawaye take tana binsa da harara ita kam. “Mschww!” Dai-dai ya juya ze fita kenan wayarta dake kan gado ya soma ruri ai tana kai dubanta taga ‘My Very Own’ yana flashing kan screen d’in. Kafin Ibraheem yayi glimpsing tayi sauri ta ja ta b’oye. “Wake kiran naki?”
“Toh Ya ina ruwanka da wanda ke kira na? Ba waya na bane.”
“Baki bar kula samarukan nan naki ba ko? Nace wake kiranki?”
“Babu” tayi muting call d’in “ba gashi ba? Text message ne ya shigo, ni dan Allah kayi hak’uri ka fita zan cire kaya na kokuma in cire a idonka wallahi.” Ganin bai motsa ba ta hau cire vest dake jikintan tuni Ibraheem yabar d’akin “ai daka tsayan inban ragar da bra kad’ai a gabanka ba tunda daman muharrami na ne kai.” Sefa a yanzu ta tuna Ammar ne ya kirata bata d’aga ba. Ya kira bata d’aga da wuri bama ya suka k’are bale ace yau bata d’aga ba. “Omg!” tayi stating sannan ta shiga dialing number’n sa, har 3 missed calls beyi picking ba. Bawai kuma bayi kusa bane, actually wayan ma na hannunsa d’agawan ne bazeyi ba shi wai me zuciya. Se a karo na hud’u ya d’aga nan ma yayi shiru “hello My Very Own?” shiru ba response.
“Very Own please kayi hak’uri and let me explain.” Wayar ma ya katse gabad’aya haka kamar jaka ta sake kira nanma se a karo na uku ya d’aga “Very Own please let me explain kaima kasan dagangan bazan k’i picking up call naka ba, I was with Ya Ibraheem shiyasa.”
“You are lying to me again.”
“No I’m not.”
“Yes you are, I don’t mean anything to you thats why har zan kiraki bazaki damu ki d’aga ba, ba laifinki bane ai, ni na kiraki.”
“Wallahi ba haka bane Very Own dan Allah kayi hak’uri I can’t take it, you being mad at me.”
“And am very mad at you right now am hanging up dan ko muryanki banason ji.”
“Please don’t meh zan maka ka hak’ura?”
“Nothing!” yayi snarling at her.
“Please mana I’m on my knees begging dan Alkah kayi hak’uri.”
“Kinsan this is the second time hakan ke faruwa ko? Na uku I think we’ll just have to break up tunda I don’t mean anything to you.”
“Very Own wallahi thats not true you mean everything to me, kuma ka dena fad’in wai zamu rabu, I belong to only you. I love you morethan words can ever tell.” Dad’i sosai yaji amman ya dake “shine sena kiraki bazaki d’auka ba?”
“Na fa gaya maka yau Ya Ibraheem na tsaye kaina, the other day kuma wayar na cikin jakana ne I didn’t hear it ring.”
“Daman I you wouldn’t hear it tunda you don’t care, I can’t talk right now am hanging up.”
“Very Own wai baka hak’ura ba har yanzu? Gobe kazo ka d’aukeni and lets go somewhere, I have a suprise for you.”
“I’m mad I can’t go out with you.”
“And I’m sorry my Handsome Bobo, it’ll never happen again ever!” haka da k’yar ta samu ta shawo kan Adeel ya yarda a goben ze zo.
***
Washegari around 10:00AM Zeezee ta shirya tsaf cikin electric blue lace tasha had’ad’d’en makeup sannan ta fito Mama na ganinta tace, “ina kuma zaki yau da safen nan?”
“Gidansu Lubiee mana.”
“Kullum gidansu Lubiee? Jiya bakije bane? Anya kuwa chan kike zuwa bawani yawon banza ba Zeezee?”
“Yawon banza? Toh me zan zauna inyi a gida ba Adda Mariam ba Yasmeen?”
“Wallahi inma yawon iskanci kike kina bin samari gwara tun wuri kin dena.”
“Baba! Baba!” Nan da nan ya fito daga d’aki “na’am K’anwata ina zuwa da safe haka?”
“Gidansu Lubiee zanje shine Mama wai sam yawon banza da iskanci zani.”
“Kamar ya yawon iskanci? Hafsah baki yarda da tarbiyyan da kika bawa ‘yarki bane da zakice zata yawon banza?”
“Ina kuwa na yarda dashi? Kullum ace wai se ‘ya ta fita kuma gidan su Lubiee wallahi k’arya ne inma saurayi kike bi ranan da kika d’auko abinda yafi k’arfinmu nan gabad’aya ke kika sani.”
“Kai! Meh haka?! Ya isa da Allah, kidena yima K’anwata baki in shaa Allah ba abinda ze sameta” hannu yasa a aljihu ya zaro 1k ya mik’a mata “gashi ko Allah ya kare.”
“Ameen Baba na tafi.”
Dai-dai ta fito bakin k’ofa kenan sukayi bumping into each other da Aleeyu. “Awch!” Tayi exclaiming in pain.
“Sorry Zeezee didn’t mean to bump into you.”
“Is okay sannu da zuwa” tayi maganan tana wuce sa.
“Ermm... Zeezee can I have a word with you?”
“Ya Aleeyu right now am heading somewhere kabari in na dawo.”
“Just a minute will be okay.” Waje ta lek’a taga ba motan Adeel sannan tace, “toh ina jinka kayi sauri please” nan fa gaye ya hau suburbud’o mata love words shi yana sonta, kuma so na aure ba da wata manufa ba. Dai-dai ta bud’e baki tace mai ita batayi kenan ta hango furious Adeel tsaye gefen motansa. B’ari ta shiga yi tama rasa nayi.
“Wayyo Allah! na shiga uku!” ta aza hannayenta saman kai. “Ya Aleeyu dan Allah ka shiga ciki, ka gama dani yau.” Sam be gane me take nufi ba se daya leqa wajen yaga inda take kalla ya fahimci komi. Kafin tace zata k’arisa inda Adeel yake tuni ya shige motansa ya fice not minding calls da take mai sending. Kuka ta shiga yi wajen tasan koda zata had’a sama da k’asa Adeel will never listen to her, ai dan dolenta ta fice zuwa gidansu Lubiee ba shiri, thank God Ummi bata gida.
“Ya haka Babe? Meya faru kike wannan kuka?” Lubiee tayi maganan tana caressing bayan crying Zeezee ita a zatonta ma ko rasuwa akayi ma Zeezee.
“Lubiee am in trouble, nasan Adeel baze sake min magana ba.”
“Mschww! Yanzu akan Adeel kike wannan kuka? Oh ni Lubabatu! Wallahi da nasan da haka da tun farko banyi hooking naku up ba.” Shiru Zeezee tayi se kuka take chan Lubiee tace, “meya had’aku?” In a crying tone tayi ma Lubiee narrating komi. Bayan data gama sauraronta tace, “yo ai wannan ba abin damuwa bane, call him up and explain everything to him is all you’ve got to do.”
“Ke kina ganin ze saurareni neh? Fa bakisan Adeel bane, mugun kishi ne dashi ko magana da mazan class namu ya hana ni, bale ace ya ganni da wani bakin k’ofan gidanmu yau, kema kinsan da akwai babban tashin hankali, please help me out.”
“Dan Allah kibarsa da kansa ze sauk’o ni wallahi haushi kike ban idan kina ma Adeel haka, sekace shine autan maza mschw!”
“Ni a wajena shine auta, wallahi I can sacrifice everything for him dan Allah help me out.” Kallo Lubiee ta galla mata sannan ta d’au wayarta ta shiga kiransa. Seda call d’in ya kusa tsinkewa ya d’aga nan ta hau mai tsiwa, “kai kuma sarkin zuciya haka akace maka akeyi ne? How can you just jump into conclussion saboda kaga Zeezee da wani bakin k’ofan gidansu? Baka tunanin ko friend na yayanta ne yake bata saqo?”
“Ko d’aya, ni zakuyi playing? Inhar what you are saying is true why didn’t she call me up herself and explain to me? Daman tace min she have a suprise for me and I guess that incident was the suprise anyways tell her I enjoyed every part of it. Am hanging.”
“Adeel don’t! Ade”- karap ya katse abinsa. Jin haka Zeezee ta sake rushewa da sabon kuka haka ta tayi Lubiee na bata hak’uri har ta samu tayi shiru.
“Babe wallahi it hurts me seeing the way you can die for wannan useless Adeel d’in, Allah yaga kina sonsa ne yake miki wannan iskanci. Forget him karki sakeyi ta kansa believe me da k’afafunsa ze dawo.”
“Babe only if I could, wallahi bakisan yadda nake feeling Adeel ajikina bane, I’ve never felt like this with anyone. Sonsa a jinina yake.”
“Naji amman please kidena tayar da hankalinki haka, ke bakisan hawan jini yana iya kama ki a haka ba? Please ya isa don’t call him up zan kira shi anjima inya sauk’o kukan is enough.” Se bayan La’asr Zeezee ta koma gida ba annashuwa ko kad’an a tattare da ita. Miqe take bisa gado amman hankalinta sam baya jikinta. Daga bisani ta miqe zaune, “wallahi wallahi Ya have to share this burden with me also, duk laifin wannan mayen Aleeyun ne wama ze sake ce mai Yaya? Mschww! Kuma harda na Ya aciki tunda friend nasa ne” trying Adeel’s line for the last time baya shiga taje ta samu Baba da Mama a d’akinsu. Ba sallama ta fad’a tana kumbure-kumbure.
“Ya haka K’anwata wani abu ne?”
“Ke wai bazaki koyi yin sallama bane? Wawiya kawai.” Mama tayi scolding nata. Ai dama a cike Zeezee take seta sa kuka unstoppingly “haba Hafsah! Yanzu ai kin huta da kika sata kuka, zo K’anwata” har kan gado yayi beckoning nata over ta zauna gefensa sannan ya share mata hawayen, “yi hak’uri kinji? Allah Hafsah kika sake cema yarinyan nan wawiya you’ll answer to me.”
“Yo inba wawanci ba yarinya is sixteen (16) years old amman ace har yanzu barging into our room take ba sallama.”
“Ba ruwanki, kiyi abinda ke gabanki. Ehem ina jinki K’anwata meya kawo ki? Ko kinzo tayani hira ne?”
“Ba d’azu zan fita gidansu Lubiee ba?”
“Ehemm... Ina jinki” ya bata full attention nasa wanda ko Mama bata samun irinsa. Itama Mama kasa kunne tayi tana sauraron Zeezee’n.
“Nazo zan fita kenan kawai sega friend na Ya Ibraheem Aleeyun nan, dana gaishe shi seya cemin wai yanason min magana nace yabari anjima yata insisting then nace masa ina jinsa, kawai ya hau cewa wai yana sona. Son ma wai na aure Baba bayan ni ka hanani yin saurayi se after secondary school.”
“Haka shi Aleeyun yace?! Lallai yaron nan baida hankali, har gida na zezo ya nemi K’anwata ba tare da ya tambayi izini daga guna ba? Allah kaimu rananda ze sake zuwa!”
“Uhn-uhn Alhj don’t just jump into conclussion.”
“Like how Hafsah? Ke bakiji abinda Zeezee ta fad’a bane? Mu godewa Allah ma Zeezee nada wayo in wata sakariyan ne ba sede ta bisa ba suzo su mana abin kunya.”
“Kai yanzu how sure are you Zeezeen naka ba k’arya take ba?”
“Wallahi wallahi ba k’arya nake ba kuma tun kafin yau dama ranan na jisu da Ya suna maganan. Ya yake cemai wai ya basa go ahead.”
“Shi Ibraheem d’in? La’ila! Jeki kiramin shi.” Nan ta fice, “hmm Allah kyauta de amman dekam I don’t believe this girl, itan da tun a Ss1 take kula samari dan yanzu Aleeyu yace yana sonta wai take kawo ma k’ara? Akwai abinda ke cikin duhu.”
“Haka kuwa zakiyi ta nema ki gaji saboda ba abinda ke duhu, samari kuma tun Ss1 dana mata magana ta denayi” dai-dai nan Ibraheem yayi sallama “wa’alaikum salam” suka amsa a tare. Wucewa Zeezee tayi taje ta zauna gefen Baba.
“Yanzu kai Ibraheem ka kyauta kenan a matsayinka na babba? Ina ganinka da hankali amman seka tafka sakarci haka?”
“Gaskiya wannan bayi bane, taya a gaban K’anwarsa zaka tsaya kana mai magana haka?” Mama tayi maganan a fusace.
“Ke dama ai tanan kika fi kauri, d’aure ma k’arya gindi. Dake Ibraheem ne me sunan Babanki dole kik’i ganin laifinsa ai to ni kimi shiru.” Har anan Ibraheem bece komi ba.
“Ehh Ibraheem? Hakan da kayi ka kyauta kenan?”
“Baba nifa ban fahimce kaba.”
“Batun friend naka Aleeyu nake magana. Taya zakayi haka? Kai bakasan a rashi na kaine uba ga Zeezee ba? Seka kama ka bawa d’an iskan can go ahead, wato yayi komi da k’anwarka kai baka damu ba ko?”
“Ni!” Yayi pointing kansa. “Yaushe na bawa Aleeyu go ahead? Infact ni koda yacemin gashi gashi yana sonta ma ban yi backing maganan ba ce masa nayi Zeezee is still a girl yabari ni ba ruwa na kuma ko ke Zeezee banje na sameki nace miki duk wanin dana sani inya ce yana sonki kisan ba bakina aciki ba?”
“Ni! Yaushe akayi haka dani? Nide baka cemin komi ba.” Ibraheem was left dumbfounded, lallai Zeezee!
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
No comments:
Post a Comment