Wednesday, 28 December 2016

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 25

  *December, 2016*



     Line na Zeezee tayi dialing sede switched off yake ta cemata don haka ta kira na Adeel kusan 4 missed calls tamai be d’aga ba.

  _Party hall, Yankari._
    Rawa su Zeezee ke tasha, gabad’aya filin an bata ita da Adeel se cashewa suke daman gwana ce when it comes to dancing, a jikinta ba inda Adeel be ta6a ba. Ko sallan Maghrib basuyi ba to talk more of Ishaa, bayan sun gama cashewa sun yi taking dance floor, aka hau applauding nasu. Hannunsa taja suka koma gefe suka zauna bayan tasha ruwa ta d’aga wayansa dake kan table dan duban time. To her suprise taga 10:02PM “o my Gee! Na shiga uku! Very Own k’arfe 10:02 banyi sallah ba, nashiga uku Baba must have gone crazy looking for me, wayyo Allah na mutu!” Tayi maganan kamar wacce zatayi kuka all confused.
   “Calm down Babe we’ll go and pray now soon zamu tafi.”
  “Very Own dan Allah mutafi yanzu na shiga uku me zan fad’awa Baba? Please do something.” Hannunta ya kama ya had’a da nasa “calm down okay? You are not going home at this night saboda nasan Baba will be very furious at you kibari se gobe.”
  “What?!” Tayi maganan unblievably “har gobe? Kana nufin yau ba a gidan Babana zan kwana ba? Please karka min haka ba haka mukayi dakai ba Adeel save me please, wallahi Baba ze kasheni.”
  “I told you to stop crossing me, don’t you trust me? Kika koma gida a daren yau sun saki gaba sun rik’a miki questions kenan ina kikaje, if you’re not lucky har dukanki zasu iya yi amman kika bari gobe da safe kika koma seki tinkaresu da kuka kice wani ne ya d’aukeki jiya ya gudu dake, addu’a kika tayi Allah ya dawo dake.”
  “How is that even possible Adeel? My parents are not dumb dan Allah ka kaini gida I can’t sleep outside my Dad’s house.”
  “In kinga nabar nan toh safiya tayi ne, ke mesa ba’a gayamiki magana kiji ne wai? Tun da muka zo nan acikin friends d’ina kinga wanda girlfriend nasa ke basa matsala ne inba niba? Cut it out okay? This is bullsh*t!” Key’n motarsa ya zaro ya wurga mata “gashi seki tafin ai tunda ke ba’a tab’a gaya miki magana kiji mschw!” Yayi hitting table d’in so hard da hannunsa.

   Kuka ta shiga rusawa wajen if only ta iya driving late at night da ta tafin, da tasan da haka da bata biyosa bama in the first place. Taya iyayenta suna raye bawai aure ko tafiya tayi ba zata kwana a waje? Ita yanzu bama wannan ba what if shed’an ya rinjayi Adeel yayi mata wani abin da daddare fah? K’ara volume na kukan nata tayi amman ko ta kanta Adeel beyi ba, hasali wayarsa ma yake ta latsawa seda tayi me isarta sannan ta share hawayen nata. _Adeel is my only hope, dole nayi kamar yadda yakeso kokuwa nice da asara_ tayi tunanin haka a ranta. Key’n motar ta ajiye masa kan table d’in, adalilin haka ya d’ago kai yana kallonta “kin fasa tafiyan ne?” Kai kawai ta gyad’a mai.
“Why?”
  “Because I trust you Very Own.”
  “Then why did you cross me?”
  “Because I was afraid Very Own ban tab’a kwana a waje ba se yau tsoro nakeji” miqewa yayi ya jawota jikinsa “I’m with you, you are safe kinji?” Kai ta gyad’a a hankali seda hankalinta yad’an kwanta ya saketa suka fice zuwa wani hotel not too far from Yankari. D’aki ya musu booking seperately anan suka biya sallolinsu sannan suka ci abinci. Sam hankalin Zeezee yakasa kwanciya ta kunna wayarta ma tsoro take gudun kar Baba ya kirata ya shiga.
  Kafin Adeel ya kwanta ya nufi d’akinta dan dubata, “hope ba abinda kike buk’ata ko?” Kai kawai ta kad’a mai. “Don’t worry kinji? I’ve got you, gobe first thing in the morning zan kaiki gida, I love you” yayi pecking nata a forehead.
  “I love you too” ta fad’a a hankali nan ya ja mata k’ofan ya rufe. Yana juyawa sega friend nasa Anaconda da wasu mata guda biyu ta each side nasa “ya Adeel? Don’t tell me you are sleeping alone?”
  “I am” yabasa amsa a takaice.
  “Babe nakan fah meya sameta ko kunyi fad’a ne?”
  “Nahh bata sallah ne” yayi mai k’arya.
  “Ohh I see kona baka d’aya daga cikin nawa ne?”
  “No thanks seda safe” yana kaiwa nan ya fice zuwa d’akinsa.
   Kwana zaune Zeezee tayi gabad’aya takasa bacci tsantsan tashin hankali, tunanin ya iyayenta za suyi da ita gobe kawai take. Achan gida ma haka ne Mama duk ta kasa bacci as tana tunanin wani hali Zeezee ke ciki, kwana Mama tayi tana Sallah Allah dawo mata da Zeezee gida safe and sound. Abin ya bata mamaki yadda hankalin Baba ya kwanta lokaci guda gashi koda ta tambayesa any news seya ce mata babu.

   _5:56AM_
  Adeel yayi knocking bisa door na Zeezee, ba tare d a b’ata lokaci ba ta bud’e “morning Sunshine.” Yayi greeting nata.
  “Morning Very Own.” tace sama-sama.
  “Owww don’t tell me you didn’t sleep yestarnight.” Yayi maganan hannunsa k’ark’ashin fuskarta, kai ta kad’a tare da sauk’e hannun nasa.
  “I couldn’t force myself into sleeping shiyasa.”
  “So lets have breakfast?”
  “No Adeel dan Allah ka kaini gida kaji please kayi hak’uri bawai ina crossing naka bane kawai inason inje gida ne” tayi asking pleadingly.
  “Okay Babe lets go.”

  45 minutes drive yakaisu corner’n gidansu Zeezee. Tun anan tahau kakkarwa hannunta Adeel ya riqo “all is well kinji karki damu, ba abinda Baba ze miki you are his girl just tell him someone tried ro run away with you.”
   “I’ll try.”
  “Duk abinda akwai call me up kinji? Thanks for yestarday, I love you” yayi pecking kumatunta. “I love you too” tafad’a da k’yar sannan ta bud’e k’ofan ta fice seda ta shiga gida Adeel yaja mota ya tafi shima. A dai-dai bakin k’ofan ta tsaya takasa going any further. Wani erin mumunar harb’awa zuciyarta ke, tafi minti uku tsaye wajen sannan daga bisani tayi _womaning_ up ta k’arisa ciki. A dai-dai lokacin Mama da Baba suke shirin fitowa da alama don cigaba da nemanta ne, tana ganinsu ta wani mugun razana.
   “Zeezee!” Mama da Baba sukayi exclaiming in unison. Kakkarwan take har yanzu takasa ce dasu komi.
  “Zainab kece?” Mama tayi maganan some inches away from her tana shafa hannunta.
  “Nnn... Nice Mama” tayi speaking up finally in a low cracky voice.
  “Alhamdulillah! Alhamdulillah Alhj Zeezee ce Allah ya dawo mana da ita, ina kika shiga Zeezee? Meya faru?” Har anan Baba bece komi ba as se gallawa Zeezee harara yake.
  “Mm... Mama wani ne ya gudu dani” se ta rushe da kuka kaman daga sama kawai taji sauk’an mari fas! A fuskarta seda taga stars dan azaba, kafin ta hankara Baba ya sake k’ara mata d’aya. A rayuwarta bata tab’a shan zafin mari kamar na yau ba, never once did she ever imagined that Baba ze tab’a d’aga hannu ya mareta. Da sauri Mama taja crying Zeezee gefe d’aya “Alhj dan Allah kayi hak’uri hakan be kamata ba, mu godewa Allah ta dawo gida shine babba.”

  “Ta dawo? Mesa bata bi shi d’an iskan sun gudu gabad’aya ba?”
  “Alhj please calm down ka tsaya muji daga bakinta mana ko bakaji tace wani ne ya gudu da ita ba?”
   “K’aryan banza waye yaro anan da zata raina masa wayo? Ke!” Yayi maganan da Zeezee “kalleni nan! Kalleni nace!” A hankali tana kare jikinta a na Mama ta d’ago jajayen idanunta tana kallon Baba “meya faru jiya?” ya tambayeta finally. Shiru tayi tama kasa magana se hawaye kawai take a yayinda inda Baba ya zuba mata mari keta mata rad’ad’i. “Bazakiyi magana bane sena baki kashi kome?”
   “Bb... Bb.. Baba wallahi wani ne ya gudu dan-” bata k’are maganan ba Baba ya hau kanta a fusace, da wuri Mama tajasa baya “Alhj kace zaka biye wa yarinyan nan wallahi kasheta zakayi ko ka illata ta, kayi hak’uri dan Allah.”
  “Ba gwara ta mutun ba na huta akan ta b’ata min suna, kap cikin dangina ba wanda ya ta6ayin iskanci, akanki kuma” ya nuna crying Zeezee da yatsa “baza a soma ba kina jina ko? Ina kika je jiya nace? Wani d’an iskan ne yazo ya d’aukeki and ina ya kaiki? Kuma wallahi kika kuskura kikamin k’arya kinji na rantse bazaki kwana da rai ba yau.” Shiru Zeezee tayi ta kasa magana se zubar da hawaye take endlessly.
  “Alhj  dan Allah kayi hak’uri bamu sani ba ko dagaske wanin ne yaso guduwa da ita tunda kaga tadawo tana kuka.”
  “Aikin banza, ajinki bana sane ne da party’n da sukayi organising jiya a Yankari? Police excuse suka karb’a dalilin da yasa ban samu na bita har Yankarin na bata kashi a wajen ba kenan, in kuma baki yarda ba ta kwaye miki hijabin nata kiga abinda ke k’asa. Kwaye hijabin nakin!” Ya buk’aci Zeezee ko motsawa batayi ba, “ki kwaye nace ko sena kwaye miki da kaina?” salati kawai Mama ta hau yi.
  “Baba dan Allah kayi hak’uri, na tuba dan Allah kayi hak’uri.”
  “Ki kwaye nace!” Kafin Mama ta hankara ya turata gefe ya nufi kan Zeezee. Fincikota yayi da hannu d’aya sannan yaja hijabin nata seda ya cire. Sega Zeezee nan da shirin party’n ta na jiya, wani marin Baba ya sake kai mata fiye da biyun d’azu. Wani irin ihu ta saki seda Omar dake bacci yafito a gigice yana kallon ikon Allah.

   “Hakane wani ya gudu dake? K’arya zaki sake yimin akan laifin da kika aikata?” Ya d’aga hannu ze sake kai mata wani bugin Mama ta shiga tsakiyarsu “Alhj dan girman Allah kayi hak’uri inma dukan tan zakayi kayi da bulala bada hannu ba, dan Allah nace” turata gefe yayi ya sake kaiwa Zeezee wani marin ihu ta shiga yi sosai tana had’asa da Allah.
  “Omar do something karya illata Zeezee please” cewar Mama. Da k’yar Omar ya samu ya k’wato Zeezee daga hannun Baba don se ball da Zeezee yake tamkar bashi ne mahaifinta ba, bayan Omar ta lab’e se rusa kuka take.
    “Iskanci zakiyi a gida? Iskanci? Waye ubanki nace! Eyye! Har wai zaki kwana a waje, Mariam da Yasmeen ba yayyunki bane da bazakiyi koyi dasu ba? Miqo wayanki nan kuma kije ki d’auko duka wani gadgets naki including your car key” ganin bata motsa ba ya daka mata tsawa “ko baki jini bane?!” Tana b’ari cikin wata dashasshiyar murya tace, “naji” wayar nata ta miqa wa Omar yabawa Baba “wannan ne wayanki?” Ya tambayeta.
  “Omar wannan iphone 7 nawa ne? S ceh?” Da Omar ya duba seyaga pro ce “a’a pro ce Baba.”
  “Waya saya miki wannan d’in?” Shiru ba amsa, “waya saya miki nace?!” Ya daka mata tsawa.
   “Baba dan Allah kayi hak’uri.”
  “D’an iskan saurayin naki ko? Lallai yarinyan nan kinyi nisa har waya saurayi ke siya miki sabida bakida uba koh? Zaki sha mamaki baki sanni bane” Buga wayar yayi a k’asa seda ta rugurguje “wuce kije ki tattaro min gadgets naki, keda waya kuma ya k’are sede miji ne ze sai miki, wuce nace kafin na illataki anan!” Da gudu tayi d’akinta ta tattaro su ipad nata da komi ta kai ta ajiye a tsakar gidan tana ji tana gani Baba yayi rugu-rugu da komi a wajen daga kan ipad nata da mac book duk ya faffasa su sannan yasa key’n motarta ta a aljihu.

   “Ke wai iskanci kika sa a gaba koh?” Kai tayi saurin kad’awa “naki ya k’are a gidan nan inkinga kin sake taka wajen gidan nan toh gawarki za’a fita dashi kokuwa mijinki yazo ya d’aukanki, dan aure zan miki bazan zauna ina gani kib’ata min suna a gari ba. Ace ni! Ni naje masallaci ana nuna ni da yatsa ga wacce ‘yarsa tabi saurayi wallahi kinyi kad’an Zainab kina jina ba? Kinyi kad’an. Ko banzan Necon ma bazaki k’arasa ba sadaqa dake zanyi in huta. Kuma Hafsah ku shirya yanzun nan aje ayi mata gwaji ko tana tattare da wani cutan zamanin insan nayi da ita tun wuri, nan da 2 weeks kuma zaku sake komawa kuyi mata pregnancy test ‘yar iska kawai abin naki hauka ne? Bakida hankali ne? Mene ban miki ba a rayuwa da zaki saka min da wannan butulci? Tambayar ki nake! Rai ne kawai ban saya na baki ba Zeezee. Duk bakiga wannan ba zaki fifita saurayi akaina ni uban ki ko?! Har ki bisa kuje ku kwana a waje, Karuwa ce ke nace? Yaushe aka haifeki da har zaki fara bin sauarayi?”

   “Haba Alhj! Meyayi zafi haka? Abun duk be kai ga haka ba please.” cewar Mama.
  “Baki jini bane? Inje in dawo baki aikata abinda na fad’an ba kiga abinda zan miki kema, kaji ai Omar maza ka kaisu nan Reemee a gwada ‘yar iskan nan” yana kaiwa nan ya fice yabar gidan. Ihu Zeezee ta k’urma har k’asa ta sauk’a tana kuka wane zata cire ranta.
    “Mama dan Allah ki rok’i Baba yayi hak’uri wallahi na tuba wallahi ni ban kwana da wani d’a na miji ba, Ya Omar dan Allah ka tayani bawa Baba hak’uri.”
  “Da Allah ja bakinki kimin shiru!” Mama ta tsawata mata “da uban wa yace kibi saurayi har ki k’i dawowa gida ki kwana waje?”
  “Mama wallahi ban kwana dawani na miji ba Ya Omar please believe me.”
  “K’arya kike!”
  “Mama wallahi ba k’arya nake ba please believe me.”
  “Dana yarda dake da ban yarda dake ba du d’aya ne Zeezee saboda bashi ze canza mind na Babanku da fact that you slept outside ba, ni dan Allah ki mik’e mu fice asibitin kafin ya dawo.” Haka Zeezee na kukan cire rai suka fice asibiti inda aka gudanar da all tests d’in aka kuma sa gynaecologist ta duba Zeezee ta tabbatar musu virgin ce ita har yanzu. Seda result na tests ya fito suka dawo gida. Ko bud’ewa Mama batayi ba ta kaiwa Baba dake zaune a d’akinsa. “Ga result d’in” amsa yayi ya duba komi negative ne, d’an sanyi yaji aransa. Numfasa Mama tayi tace, “Alhj yarinyan nan bawai taje tayi iskanci bane a waje kawai de kamar yadda ka fad’a party ya tsaidata tunda an dubata ba’a ga alamun komi ba ya kamata ka sassauta mata.”
    “Nifa ban yarda ba inba iskancin taje tayi ba meze hanata dawowa gida jiya? Ko bakida labarin a hotel suka kwana ne?”
  “Hotel Alhj?! Dan Allah ya isa haka tunda gashi de anyi tests bata d’auke da komai, Zeezee zata k’arisa rubuta Necon ta karka mata ruining future please.”
  “In ke kike ajiyeta seki kaita school d’in gobe, ita bawai iskanci tasa a gaba ba zan koya mata hankali bata sanni hane wallahi.”
 
  “Maganan gaskiya kaima da laifinka Alhj, infact kaine sanadin komi tun farko da baka mayar da ita *_‘YAR GATAN_* da batada flaws ba da hakan duk be faru ba. Sau nawa Zeezee zatayi abinda ba dai-dai ba kaima kasani amman kak’i bata laifi ka d’aure mata gindi. Sau nawa nake cemaka Zeezee na bin samari kak’i jina? Da kaji magana na da duk hakan ya faru ne? Kaima you’re partially to blame.”
  “And I accept my mistake Hafsah nasan nayi kuskure amman ban tab’a sanin dan ka bawa yaro gata seya ta6ar6are ba. Yara nawa ake basu gata kuma su tashi da hankali da nituswansu, itade Zeezee batada wayo ne kawai. A tunani na Zeezee zatayi making d’ina proud da kalan gatan dana bata.”
  “Sam ba haka bane Alhj, duk d’an daya zamanto ba ai magana, iyayensa suna barinsa yanayin duk abinda yakeso a lokacin da yaga dama a tunaninsu wai wannan gata ne toh wallahi ba gata bane, illa 6ata tarbiyya kuma surely zasuyi regetting some day. Yanzu cikin Mariam da Yasmeen akwai wanda ya ta6a tafka rashin hankali irin wannan ne? Kai ka nunawa Zeezee she is never at fault sannan kuma duk abinda tayi dai-dai ne toh wallahi in har baka taka mata birki yanzu ba, gaba abinda zata mana semunyi kuka tunda gashi nan ta fara yin hanya yanzu. Ina kira ga dukkan iyaye masu sakankanta yara dan wai su sunje boko shikenan koda yaro yana ba dai-dai ba baza’a mai magana ba, wallahi tun wuri sudena kafin azo ayita ihu bayan hari. Kaima Alhj daka jini da a baya da duk hakan be faru ba.”
  “Tabbas Hafsah ba k’arya acikin zancen ki, ban tab’a sanin gata nada illa ba se yau, na d’au yadda na bawa Zeezee gata zan zo inyi alfahari da ita, nad’au duk cikin yaran seta fisu hankali da nitsuwa da komi badan komi ba sedan yadda na nuna mata so amman tabbas GATA yana da BABBAN ILLA. Shiyasa bazan bari abun Zeezeen yayi nisa fiye da haka ba, aure zanyi mata tun wuri in huta kafin tamin abinda ze iya tsinka min zuciya na fad’i na mutu.”
  “Alhj ni ban hanaka yi mata aure ba amma de kabari tak’are necon nata tunda ta riga ta fara.”
  “Ba abinda zata k’arisa aure zanyi mata, in kinga Zeezee ta sake laying foot a gate na gidan nan toh ko tayi aure anzo fita da ita kokuwa mutuwa tayi my decision is final.”




*© MIEMIEBEE*    *TEAM#YGC!*
👄👄👄👄
 
 www.beeenovels.blogspot.com

2 comments:

Anonymous said...

sai yanzu kagane Kenan
tnx Allah yakara baseera

Unknown said...

Su baba manya! Yana magana kamar wani innocent soul. ☺yanxu kasan gata yana da illah