Saturday, 31 December 2016

‘YAR GATA CE!

BY MIEIEBEE
PAGE 26
  *December, 2016*



   _Here’s a page in honour of my dear supporters, *Lieeymarh, Humairah Melody, Princess Salmah, Khadijah👑, Aunty Jeedderh, Nusaiba Musa, Ashnur Pyar, Cute Xarah, Xee Yabour, Leemcy, Princess Haleemah, Sumee Luv, Fateemah Maid and Zainab. A* I love y’all so much #OneLove💞_

   
     
     _In Zeezee’s room..._
   Kuka take tasha tsakaninta da Allah wane zata cire ranta, ga kuma yadda kanta keyi mata sari har wani dishe-dishe take gani, tunda take bata taa6 buguwa kaman na yau ba, dukan Baba is uncomprable to Ibraheem’s. Hakan ta cigaba dayi sannan daga bisani ta miqe kan gadon ta bud’e k’ofa sanadin knock dataji, Mama tagani bayan sun iso sun zauna Zeezee tace, “Mama kin basa hak’uri ya hak’ura?” Kai kawai Mama ta kad’a mata “tukuna kema nakega sekin basa hak’uri amman ba yau ba ko zuwa gobe maybe ya tausaya miki ya hak’uran ko gobe kinada paper?”
   “Eh inada amman Hausa ne.”
  “Ko baki yiba ba matsala?”
  “Ba matsalan chan” tasa kuka.
  “Toh kukan ya isa mana, gayamin meya kaiki kwana a waje jiya Zeezee kika min k’arya kuma zan fita harkanki gabad’aya nima.”
   “Wallahi nima banyi niyyan kwana a waje ba Mama, da dare yazo yayi ne nace ya kawoni gida yak’i wai se gobe.”
  “Waye shi d’in? Saurayinki?” Kai ta gyad’a a hankali “me sunansa?”
   “Sadeeq” tayi k’arya.
  “Yanzu da Sadeeq damu suwa sukafi k’ima da daraja a idonki Zeezee dahar zaki bisa party keba muslima bace? Iyyeh? Kuma da wancan tsinannen shirin kikayi ta yawo a wajen? Nashiga uku ni Hafsah zaki halakar dani da raina. Irin tarbiyyan da na baki kenan bani bama ko Baban naku ya tab’a cemiki kije party ne?”

   “A’a Mama dan Allah kuyi hak’uri wallahi sharrin shaid’an ne baran sake ba, please kima Baba magana kada yamin auren dole wallahi na tuba.”
  “Kinsan da haka kika d’au hanyan iskanci? Aure dole a aurar dake Zeezee shi kad’ai ze sa ki nitsu kiyi hankali.”
  “Mama wallahi na nitsu ban sakewa. Ni shikenan bazan k’arisa karatu na ba?”
  “Zaki k’arasa mana idan kikayi sa’an miji dan koni bansan mawa Babanki zeyi sadak’an dake ba, inkuma ba’a dace ba keda bokon se in anayi a lahira.” Wani irin kuka Zeezee ta sakewa rushewa dashi daga k’arshe ma Mama fice mata tayi daga d’akin dan ko tak’i yin shiru. Seda tayi ta godewa Allah ta nufi bathroom ta wanke face nata sannan ta fito tasa lock a d’akin ta ciro wata k’aramar Samsung galaxy a wardrobe nata ta nufi bayi. Lubiee ta shiga kira and not long enough ta d’aga.

   “Zeezee!” Tayi exclaiming. Batasan a sanda ta fara kuka ba “na’am Lubiee.”
   “Zeezee what happened? Ina kika shiga? We’ve all gone crazy looking for you.”
  “Lubiee dan Allah ki taimaka min ina cikin tsaka meh wuya.”
  “Subhanallahi! Kina ina ne yanzu?”
“Ina gida-” katseta tayi da “alhamdulillah tunda kin dawo gida ina ba guduwa dake aka so yi ba?”
  “Lubiee I followed Adeel to a party a Yankari...” Kap ta kwashe labarin komi ta bata ba tare da ta b’oye mata komi ba. “Innalillahi! Zeezee how could you? Mesa baki fad’a minba kafin ki bisan? What were you thinking?”
  “Lubiee I wanted to make him happy, he really wanted me to go and I love Adeel morethan words can ever tell.”
  “Toh yanzu meh Baba ya miki after making your so called Adeel happy?”
  “Ya mammareni yasa akai min all Sexually Transmitted Diseases (STDs) tests acewarsa wai naje na kwana da Adeel ne.”
   “Yaaa Salam!!!”
  “Ba nan kad’ai ba ya fasa min duka gadgets d’ina, yayi seizing min mota yakuma ce bazan k’arisa Neco exams d’ina ba wai... Wai aure zemin” ta kuma rushewa da kuka. “Please help me out.”
  “Aure! Innalillahi Babe why all this? Mesa dan Allah? Da kin fad’a min zaki bi Adeel party dana hanaki no matter what yanzu gashi ya kaiki ya baroki. After making him happy look at what you’ve cursed upon yourself. Wallahi he won’t escape it sena fad’awa Abba ya kirasa yamai fad’a shima tunda duk shine sila.”
    “Inhar kina sona you won’t.”
  “What do you mean?”
   “Please don’t drag Adeel into this mess kibarshi please banason abinda ze tab’a min shi.” Cike da mamaki Lubiee tace, “lallai Zeezee na lura baki san ciwon kanki ba, infact baki ma san ina ke miki ciwo ba. Are you crazy? Taya zakice kar ayi dragging nasa into this after all everything started with him.”
 
    “I don’t care ni kawai karki had’a kansa da Abba please I beg you.”
  “Zeezee meh Adeel ya miki haka? Why are you defending him like this?”
  “Because I love him please karki had’a kansa da Abba promise me.” Shiru Lubiee tayi, “please” Zeezee ta sake pleading.
  “Alright naji.”
  “Thank you.”
  “Yanzu Zeezee ya zakiyi?”
  “Lubiee I really don’t know zan gwada basa hak’uri ni bama Neco na bane ke damuna auren da zemin d’inne. After saying sena gama degree nayi aure yanzu Baba yace zemin me kike ganin su Sumayya zasu cemin, not this auren ma bada wanda nakeso zemin bafa I can’t marry anyone else than Adeel.”
   “How comes ke tunaninki takan Adeel kawai yake zuwa? Ke baki godewa Allah bama da Baba be koreki daga gidansa ba? Believe me in Abba ne wallahi tsine min zeyi ya koreni the day ban kwana a gidansa ba, but ke all you can think of is Adeel? Adeel? Haba!”
    “Ni da kori nan ma yayi dayafi min wallahi, I know Adeel will take care of me, wallahi I can’t live without him ni banma san ta ina zan fara sanar dashi wannan news ba.”
  “You must be insane to think that way Zeezee taya zaki fifita saurayi akan mahaifinki? Akan iyayenki? Ko bakisan bakida kamansu bane?”
  “I know Lubiee amman I can’t afford to lose Adeel wallahi” ta rushe da kuka. Da k’yar Lubiee ta samu tayi shiru tace zata kirata anjima when she’s calmed. Katse wayar Zeezee tayi tafito ta miqe kan gado. Not long enough wayarta yahau vibrating tana dubawa taga Adeel ke kira ba tare da b’ata lokaci ba ta share hawayenta tare da clearing throat nata sannan takoma bayin tasa lock tayi picking.

   “Halo Sweetest Love.”
  “Na’am Very Own.”
  “Thanks Gee! I’ve been trynna reach you but can’t get through meya samu d’ayan line naki?”
  “Uhm... Na had’a a charging ne.”
  “Is that so?”
  “Yeah.”
  “Oh okay then how did things work out for you and Baba?”
  “He believed me we all good.”
  “Wow! Cool, I love you Babe and thanks for yestarday.”
  “I love you too I’ll call you later.”
  “Okay Babe take care.” Tana katsewa ta sake rushewa da sabon kuka haka ranan Zeezee ta yini tana kuka ko cin abinci tak’iyi. Baba kuwa anytime Mama ta d’auko masa maganan Zeezee sede yaja tsaki yabar mata gun.

   Washegari da safe Lubiee ta kira Zeezee kan ya Baba ya hak’ura ya barta ta k’arisa Necon ne?
  “A’a wallahi Lubiee bayama son maganan zuwa anjima zanje na samesa na gwada basa hak’uri.”
  “Toh Allah yasa ya hak’ura sorry kinji?”
  “Uhum and please koda Adeel yazo school yau kice masa nariga na tafi gida kinji?”
  “Tom naji bye.” Bayan breakfast Zeezee tayi sallama a d’akinsu Mama, Mama ce kad’ai ta amsa bayan ta shiga ta nemi gu ta zauna a k’asa.
   “Ina kwana Baba?” Ko kallonta ma beyi ba bale yasan tanayi.
  “Baba dan Allah kayi hak’uri, na tuba wallahi bazan k’ara ba kayi hak’uri dan Allah.”
  “Tashi kifita kibar min d’aki kafin na sab’a miki!” Yayi maganan cikin kakkausar muryan daya mugun razana ta. “Baba dan Allah kayi hak’uri” tayi stating in a crying tone.
  “Alhj kayi hak’uri ka saurari yarinyan nan tunda hak’uri zata baka ba wani abin ba.”
   “Bazan sauraretan ba bana buk’atar hak’urin ta, tashi kifita nace.”
  “Baba I’m terribly sorry dan Allah kayi hak’uri.”
  “Bazaki fitan bane?!” Har tana neman cin tuntu6e ta miqe ta fice tana kuka sosai.
  “Alhj ya kamata ka yayyafa wa zuciyarka ruwan sanyi kayi hak’uri yarinyan nan ta gama exams nata, yau mafa suna da paper amman bata je ba.”
  “Semeh? Ba exams da zata k’arasa wai ni zata tozarta a idanun jama’a!”
   “Wai toh kai bakajin hak’uri ne kuma naga da baka d’aura Zeezee kan wannan gur6arcacciyar tarbiyan ba da duk hakan be faru ba so kadena blaming nata ita kad’ai.”
  “Ya miki kyau.”
  “Amman Alhj kayi hak’uri” nasiha sosai Mama ta tayi masa amman sam yace shifa ba makarantar da Zeezee zata sake komawa.

   Da Maghrib Zeezee na zaune a d’akinta ta had’a kai da guiwa se kuka take Mama ta shigo “Zeezee tashi muje Babanki nason miki magana.” A sanyaye tabi bayan Mama sannan ta samu gu ta zauna “gani Baba.” Kamar wanda bazeyi magana ba yace, “toh ki bud’e kunnuwanki da kyau ki saurareni, dan Mamanku kad’ai zan barki ki k’arisa exams naki kuma hakan bawai na nufin na sauk’o bane daga laifin da kika min. Omar will be the one to take you and bring you back home, inhar kika taka inda ba school ba ban yafe miki ba Zainab kuma ina kan bakata har yanzu kina gama Necon duk wanda yazomin zanyi sadaqar ki masa koma waye ne tunda ke rayuwan bariki kika d’au wa kanki.” Tana hawaye tace, “nagode Baba, kuma kayi hak’uri nasan nayi laifi amman it will never repeat itself again dan Allah kayi hak’uri ka barni in cigaba da karatu na.”
  “Tashi kifita kibani gu!”
  “Alhj kayi hak’uri ka saurari yarinyan nan.” Hak’uri sosai Zeezee tayita bawa Baba tana kuka tsakaninta da Allah, shida kansa yagaji da jin hak’urin yace, “naji tashi kifita.”
  “Nagode Baba in shaa Allahu bazan sake tafka rashin hankali irin wannan ba inna sake kamin duk abinda kaga ya dace dani” tana kaiwa nan ta koma d’akinta.

   Washegari tun 8:15AM ta gama shirinta ta zarce d’akinsu Mama ta gaishesu sede sam ba fara’a tattare da Baba ko kud’in break yak’i bata. “Toh ni na tafi.”
  “Allah bada sa’a” cewar Mama.
  “Ameen” ta amsa tana jiran ko Baba ma zece mata hakan sede kota kanta beyi ba dan kanta ta fice zuwa d’akin Omar, “Ya Omar na shirya.” In less than 20 minutes suka isa school.
  “Nasan halinki Zeezee baki ta6a jin magana koda an miki, the reason why su Ya Ibraheem dasu Mariam basu san wannan abu da kikayi ba is because of me ni na rok’i Mama da Baba kar a fad’a musu saboda there is no point doing so. Kinfi kowa sanin yadda ran Baba ya 6aci dan kanki sekiyi whats good Allah ya bada sa’a.”
  “Ameen nagode Ya Omar amman wallahi believe me ni banje na kwana da wani na miji ba party kawai naje.”
  “Naji goodluck.”
 
    Sosai Lubiee taji dad’i ganin Zeezee sun gama paper 1 a intervals Zeezee ta labarta wa Lubiee all thats been going on lately. By 3pm suka gama exams na yau immediately Baba ya aika Omar yaje ya d’aukota. Da tafiyan su befi minti uku ba Adeel yazo, Lubiee kad’ai ya tarar wani erin mugun kallo take mai “Baby Sis ina girlfriend d’ina?”
  “Ajiyanta kabani?”
  “Ohh why the act? Meya faru?”
  “Ban sani ba yanzu kai ka kyauta kenan? Seka d’auki Zeezee ka kaita party kak’i dawo da ita gida se a washegari, don’t you know the implications of doing so? Karfa kamanta Zeezee ‘ya mace ce koda ba abinda ya shiga tsakaninku her parents will think taje tayi iskanci ne a waje.”
  “What gibberish are you speaking? Give me a break please, we all good, I told her to set up a lie, and she did Dad nata believed her what else do you want me to do?”
  “Oh haka ne?”
  “Don’t you know? Ba abinda Babanta ya mata.”
  “Yayi kyau.”
  “So ina take?”
  “Ta tafi gida batajin dad’i sosai.”
  “Ohh ayyah, thanks then na tafi ki gaishe da Ummi.” Lubiee na isa gida ta kira Zeezee, “mesa baki fad’awa Adeel abinda yafaru ba?”
  “Kamar ya?”
  “Mesa baki fad’a masa for what he did ya b’ata tsakaninki da Baba ba?”
  “Sabida I don’t want him to feel guilty.”
  “But why? He have to take the blame Zeezee.”
  “No he don’t have to, I’ll alone banason abinda ze tab’amin Adeel na gwammaci ni nayita suffering akanshi so please let things be the way they are for me please.”
  “Toh shikenan as you say se jibi in mun had’u a school.” Suna gama wayan Adeel ya kirata “Babe I went to your school earlier Lubiee tace you left you aren’t feeling too good.”
  “Yeah wallahi Very Own amman karka damu da sauk’i”
  “And you didn’t tell me.”
  “Sabida banason abinda ze tayar naka da hankali ne, I love you way much.”
  “And I love you as much, get well soon okay? Your man loves you so much.”
  “I love you too bye zan d’an huta”
  “Okay rest well” tayi hanging. Fitowa tayi daga bayin ta mik’e kan gado tana tunanin ya rayuwar ta zata kasance without Adeel. Da ta rasa sa ta gwammaci ta rasa ranta, wannan kenan!

        ★*★*★*★
   Haka rayuwan Zeezee ya cigaba da kasancewa kullum cikin k’unci. Har a yau kuwa bata sanar da Adeel gaskiya ba, kullum cikin bawa Baba hak’uri suke ita da Mama har suka samu suka shawo kansa yaja baya da zancen auren sadaqan da zeyi da Zeezee. Se anan taji sanyi a ranta finally zata kasance da Adeel nata. Cikin ikon Allah suka gama neco exams nasu a ranan sukayita having fun like never se da yamma ta dawo gida.
    “Haka kuma kukayi da uniform nakun?” Mama dake fitowa daga kitchen ta kalli Zeezee da tayi rugu-rugu da uniform nata ko ina jiki autographs ne da marker sannan kuma sprays.
  “Mama makaranta fa muka gama.”
  “Toh Allah sanya albarka.”
  “Ameen Baba na gida?”
   “A’a ya fita amman soon ze dawo.”
  “Oh okay sannu da aiki toh” tana kaiwa nan ta fice zuwa d’akinta ta hau waya da Adeel.
   “What is tomorrow?” ya tambayeta.
   “Tomorrow is my man’s birthday, you think I could ever forget your birthday? I might forget mine but yours NEVER!”
  “Awwn! I love you Barbie.”
  “I love you too.”
  “I miss your arms around me two days, lets meet up today please.”
  “Very Own I don’t think you miss me as much as I do miss you wallahi amman kasan I have to be vigilant yanzu sabida abinda yafaru recently in bahaka ba Baba yana iya gano ni.”
  “Hakane kuma but know that I miss you.”
  “I miss you too Cuddle bear, so what do you plan on doing for your silver jubilee birthday?”
  “Nothing much, I’ll just be celebrating it here at Zaranda.”
  “Oh really? A grand party?”
  “Yes a grand one Babe, I’ll be turning 25 dole ai.”
  “So by what time?”
  “Its starting by 8pm ending till down.”
  “8pm?!” Tayi exclaiming itan data d’au da safe za’ayi yadda zata samu taje.
  “Yes you know you need to be there ko?”
  “Sure I’ll be there for you, if I don’t who will?”
  “Number one reason why I love you so I’ll come and pick you up.”
  “Toh sekazo I love you.”
  “I love you too.” Tana hanging ta fito daga bayin tana me tunanin ya za’ayi tayi attending birthday’n Adeel, tasani inhar wannan karan ta sake fita da daddare da k’yar abu su dai-daita tsakaninta da Baba amman kuma abinda ta sani for sure is she can’t miss her Very Own’s birthday, not ever! Seeing batada way out ta kira Lubiee “hello Babe is the cake ready?”
  “Yyess almost sede bada wancan picture nakun akayi ba fa, da wanda ku kasa polo shirt black and white akayi using.”
    “Why toh?”
  “An kasa minimizing pic d’in chan.”
  “Damn it! Banso haka ba amman yayi kyau?”
  “Eh karki damu zan miki sending sneak pic ta whatsapp.”
  “Okay toh amman Babe da akwai matsala fah.”
  “Meneh kuma yanzu?”
  “Yanzu Very Own yake sanar dani wai birthday’n shin fa da dare za’ayi.”
  “Da dare?!” Lubiee tayi exclaiming.
  “Eh wai Babe ya zanyi dan Allah?”
  “Ya kuwa zakiyi? Tell him bazeyi kije da daddaren ba.”
  “Tell him? That will be the last thing I’ll ever do.”
  “Zeezee baki horu bane waikam? You mean zaki sake binsa goben ma after what happened kwanaki?”
  “No amman I can’t tell him that I can’t attend his birthday.”
  “Why not?”
  “Because he is my Man Lubiee can’t you get it, ya kike tsammanin zeyi feeling ace girlfriend nasa guda can’t make it to his birthday?”
  “Toh kice mishi time d’in is inconvenient to you acanza a miyar 2-5pm haka.”
  “No I don’t wanna be a burden to him.”
  “Zeezee get brain kina jina koh? You are not attending this party inhar da daddare za’ayi ni na gaya miki am calling Adeel up.”
  “A’a Babe please don’t zan masa magana da kaina kinji please.”
  “Better senaji daga gareki” nan tayi hanging. Safa da marah Zeezee tahau yi a bayin sam tarasa meke mata dad’i she can’t miss Adeel’s birthday for the world to ya zatayi yanzu? Tafi minti biyar tana tunani sannan daga k’arshe tayi making up mind nata she’ll call him up and tell him what happened last time data kwana a waje. Number’nsa ta shiga dialing and not long enough ya d’aga.


 

*©MIEMIEBEE*  TEAM#YGC*
👄👄👄👄
  wwww.beeenovels.blogspot.com

No comments: