Sunday, 25 December 2016

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 23

  *December, 2016*




      A guest room ta sauka, bayan ta watsa ruwa ta fito tana bin gidan da kallo, a kitchen ta tarar da Fateemah tana had’a lunch “sannu Aunty Fatee” tayi maganan cike da gatsine.
  “Yauwa Zeezee har kin fito ne?”
  “Eh ina Ya Ibraheem?”
  “Yanzun ya fita ya koma office.”
  “Ohh gidan Yaya na yayi kyau ba laifi.”
  “Ko? Toh mungode” A zuciyarta tace _ya gode ko kun gode? Sekace tare kuka gina gidan, over sabi._
   “Chab! Amman kam Aunty Fatee kin k’ara k’iba abincin gidan Yayana na aiki.”
    “LOL koh? Kije ki d’anyi kallo kafin na gama had’a lunch d’in” chan k’asa-k’asa Zeezee tace, “da yafi maki kam dan ba assisting naki girkin zanba hutu na zoyi ehe!”
  “Na’am kikace meh?”
  “A’a babu nace sannu da aiki ni zan d’an zagaya ta cikin gidan, naga kaman akwai garden.”
  “Eh akwai bismillah.” D’akin data sauk’a ta koma ta d’au wayarta sannan ta wuce garden d’in se videon kanta take tana posting a snapchat haka ta tayi har seda Fateemah ta kirata kan lunch is ready. Cikin nutsuwa suka gama cin abincin agun Zeezee tabar plate nata, Fateemah da kanta ta tattara tayi wanke-wanke. Kallo kad’an Zeezee ta tab’a ta koma d’aki ta hau waya da Adeel nata. Se 5pm da Ibraheem ya dawo tafito ta mai sannu da zuwa nan sukayi proper gaisuwa ya mutan gida da komi da komi. “Kinbar rashin kunya kokuwa har yansu halin naki na nan?”
“Ni daman ina rashin kunya ne?”
  “Allah sa toh, bazaki ci abinci bane ke?” Yayi maganan yana zama kan kujerar dining da Fateemah taja mai.
  “Munci da Aunty Fatee d’azu.”
“Oh okay” nan Fateemah tayi serving nasa tare da zama gefensa tahau feeding nasa. Baki Zeezee ta sake wangalau tana kallon ikon Allah. Yi tayi kamar tana kalllon TV amman hasali hankalinta akan su yake bayan ya gama cin abincin ya rik’o hannun Fateemah “zamu shiga ciki Zeezee feel at home.”
  “ko baka fad’a ba ai” tace tana bin interwined hands nasu da kallo suna b’acewa ta tafe hannunta “oh! iskanci a idona yau, kome zasuyi acikin d’akin kuma se Allah hehehe! Su Ya Ibraheem manya” kallo ta tayi chan da kallon ya isheta ta hau chatting. 6:30pm Ibraheem yafito sanye da jallabiya “lokacin Sallah yayi seki tashi.”
  “Toh ni banayi.”
  “Ya miki kyau ni na tafi masallaci.”
  “Allah kare toh” yana fita ta mik’e zunbur ta nufi d’akin da taga sun shiga d’azu. Fateemah ta tarar da hand drier a rik’e a hannunta tana d’aure da towel both a jikinta da kuma kanta. Wani shegen kallo Zeezee ta bita dashi ina irin nasan me kukayin nan. “Uh Aunty Fatee ashe d’akinku na shigo na zata nawa ne.”
  “A’a naki na k’arshen corrider by your left hand.”
  “Aihoo amman wanke kanki kikayi ko?”
  “Eh” ta amsa a takaice.
  “Ohh amman meyasa? Naga sabon kitso ne akanki.”
  “Ermm... Eh normally idan nayi wanka haka nake sena wanke kan.” tayi maganan tana neman ignoring topic d’in.
  “Wow wierd! Ga kuma ko ina tsaf a d’akin illa kan gado sekace anyi dambe akai.”
  “Zeezee kije kiyi sallah kinji? Nima yanzu zanyi.”
  “Nikam bana Sallah bazan taya ki gyaran gadon kafin Ya yadawo.” Ganin ta nufi gadon Fateemah tayi saurin shan gabanta “a’a bari karki damu ai hutu kika zoyi ba aiki ba zan gyara da kaina nagode.”
  “Allah Aunty Fatee kibari na gyara miki.”
  “A’a Zeezee kibari nagode” haka suka tayi seda Zeezee ta wahalar da ita ta hak’uran tare da ficewa “‘yar is.. ai da kin bari na gyaran naga me kike b’oyewa, ai wallahi sena hanaku sukuni keda Ya” tayi maganan tana mik’ewa kan gadonta.

     Washegari ranar ta kasance Saturday ba aiki, tun 9am su Ibraheem suka tashi banda Zeezee dake ta sharb’an bacci. Shi da Fateemansa suka had’a breakfast suka karya sannan suka ajiyewa Zeezee nata se 12noon ta tashi tayi wanka ta shirya sannan ta fito. A parlour ta tarar dasu suna hira suna kallo Fateemah ta kwanta jikin Ibraheem comfortably sekace ‘yar baby. Seda Zeezee ta k’are musu kallo sannan tayi gyaran murya nan Fateemah tahau k’ok’arin d’agowa daga jikin Ibraheem, ganin haka shikuma yak’i saketa “toh in bazaku gyara ba ina kwananku.”
  “Baby ka sakeni please” Fateemah tayi maganan can k’asa-k’asa.
  “Ko gaisuwan ma bazaku amsa bane Lovey-Dovey?”
  “Kin fara koh? Baki bar halin nan naki na rashin kunya ba ashe.”
   “Hali zanen dutse, kuma ai naga akan gaskiya na nake, inba neman ku b’atani ba taya kunji motsi na bazaku d’an gyara ba?”
  “Yi hak’uri Zeezee ga can breakfast naki a dining.” Fateemah tayi stating shamely.
  “Apologies accepted, me kika girka?”
  “Chips ne da omalet.”
  “Nikam banason chips indomie nakeso.”
“Ga kitchen ai seki shiga ki dafa ko ita Fateeman kikeso ta girka miki?”
  “Aiko tanason girkamin d’in ma ba barin ta zakayi ba yadda kawani damk’eta ajikin ka sekace za’a sace maka ita, you may carry on  na wuce kitchen.” Anan ta fice kai kawai Ibraheem ya kad’a Fateemah na murmushi tace, “Zeezeenmu se a hankali.”
  “Ai nakega kafin ta gama hutun nata seta bugu zatayi hankali, tad’an manta ni ne two days”
  “No Baby banda duka please.”

****
   Bayan Sallan Azahar Fateemah ta shiga had’a lunch, Ibraheem na dawowa yaga Zeezee zaune a parlour tana kallo while Fateemah nacan tana aiki. “Ke bazaki je ki taya Aunty’n ki aiki bane?”
  “Ya aiki nazo yi ko hutu? Danfa Mama na tak’ura mun agida yasa nazo nan dan na d’an huta, nan d’in ma kace wai sena taya Aunty Fatee aiki? Da bani nan wake taya ta?”
  “Karkiga fa dan kinzo hutu ki zata wai bazan iya dukanki ba tam! is better kiyi minding tongue naki.”
  “Toh Ya amman nazo hutu kuma sekace senayi aiki.”
  “Sekinyi tashi kije ki sameta.”
  “Ni wallahi-” ganin ya nufi kanta ta mik’e a 360 se kitchen d’in tana cunno baki tana gun-guni “lafiya dai ko Zeezee?”
  “Wani irin lafiya wannan mijinkin wai sede nazo na tayaki aiki sekace ba hutu nazo yiba.”
  “LOL toh karki damu jeki cigaba da kallon ki yanzu ma zan gama.”
  “Yauwa toh ki fad’a mishi yaji karya daken.”
  “Baby! Aww sorry Ya Ibraheem!” ta kirasa.
  “A’a ni koda Baby’n ma kika kirasa ba matsala nide in baze daken ba shikenan.”
  “Yes Sweetheart” yayi magana yana k’arisowa kitchen d’in “me kike tsaye achan bance kiyi assiting Fateemah ba?”
  “A’a Baby kabarta please kaga ba dad’i hutu tazo let her be. Ai aikin ma ba yawa yanzu zan gama.”
  “Wai ance miki anayiwa Zeezee abinda takeso ne? Ko washing dishes ne kibata.”
  “Seriously Babe let her be na gama komi jekiyi kallonki Zeezee.” Gwalo Zeezee tama Ibraheem tazo wucewa ya danna mata rank’washi akai “Allah ya-”
  “Me kika ce?” tana murza wajen tace;
  “Nace Allah saka maka da alkhairi” ta gyara zancen nata. Ita de Fateema dariya kawai take sha’anin Ibraheem da Zeezee se kallo.

     ★*★*★*★
  Haka fa Zeezee ta cigaba da moran hutun ta gidan Ibraheem, ba aikinda take komi Fateemah keyi koda Ibraheem yace tayi se Fateemah tace a’a tabari zatayi da kanta. In garin Allah ya waye Zeezee sede tayi wanka tayita d’aukan hoto, chatting, waya da Adeel da kuma kallo. Sekuma ta bari Ibraheem da Fateemah sunyi d’aki seta ruga aguje ta shiga ciki ba notice ta hau ihu wai taga kyankyeso ko b’era. Gabad’aya ta hana Fateemah sukuni dan ita Fateemah ta rage kalan love da take bawa mijinta amman dukda haka Zeezee bata gani bale tad’an rage mata wani abun.
 
   7:48AM Fateemah da Ibraheem suna tsaye gaban dressing mirror tana mai bottling shirt, tana gamawa ta d’aura masa necktie dai-dai tazo basa goodluck kiss kenan Zeezee ta bankad’e k’ofa yau harda ‘yar kukanta. A firgice Ibraheem da Fateemah suka juya suna kallon ta, duk kunya yabi ya ratsa Fateemah “uhm Zeezee lafiya?” tayi saurin tambaya. Kuka tasa gun ta k’arisa wajen Ibraheem da gudu tare da hugging nasa tana kuka. “Wai meke danunki ne? Ko aljanu sun shige kine bamu sani ba.” Ibraheem yayi maganan a bit confused. “Sakeni toh!” Sake matsesa tayi ajikinta “Ya tell me its a dream Baba be mutu ba tell me please” ta hau rusa kukan munafirci.
  “Mutuwa kuma?”
  “Maybe mafarki tayi” Fateemah ta amsa shi.
  “Toh sakeni mana Baba be mutu ba da Allah mafarki ne.”
  “Tsoro nakeji” ta cigaba da sobbing, hannu Fateemah tasa zata jata daga jikin Ibraheem ta bata warm hug instead aikuwa Zeezee tak’i, haka ba yadda Ibraheem ya iya yayi hugging nata back yana caressing bayan ta nan munafukan ta b’ullo da rabin idonta tana kallon sauyin yanayin fuskan Fateemah dan dole taji tokari a zuciyarta dukda tasan siblings nesu amman kishi irin namu na mata baze barta ba. Sun kusan minti uku a haka sannan ta d’ago daga jikinsa “shikenan?” ya tambayeta
  “Eh nagode.” Kai yayi nodding “koma kije ki kwanta toh ba abinda ya samu Baba, zan tafi office if you need anything else ga Fateemah.”
  “Toh Allah ya kare.” Nan ta fice tana murmushi ita kad’anta tana isa d’aki ta baje kan gado “right timing nayi ashe, wannan Fateemah ta fiye iskanci wallahi kullum cikin kissing Yaya shikuma sekace zombie yata biye mata mschww! Ai wallahi muddin ina gidan nan sekun dawo salihan dole. Ko a babu nasan na sosa miki rai.” Bacci takoma se 12noon as always ta tashi tayi wanka ta shirya tsaf sannan ta fita, breakfast nata ta tarar a dining ta bud’e ta gama ci sannan ta shiga k’wala wa Fateemah kira, daga d’akinsu ta amsa nan Zeezee ta bud’e ta shiga ta sameta zaune a k’asa tana gyaran wardrobe nata.

  “Sannu Aunty, gyaran drawer kike?”
  “Eh wallahi Zeezee harkin karya?”
  “Eh bazan tayaki.”
  “A’a bari karki damu.”
  “Allah kibari na tayaki” nan suka shiga gyara mata. Ashe dekam Zeezee da biyu tace zata taya tan don tun kafin ayi bikin, cikin kayan lefen taga wani lace daya mugun mata kyau ba yadda batayi da Ibraheem ya bata ba yak’i gakuma koda ta duba shagunan Baba duk babu.
  Tana cikin had’a mata wardrobe d’in taci karo da lace d’in ko d’inkawa ma Fateemah batayi ba “wow!” Tayi exclaiming. “Aunty Fatee wallahi wannan lace ya had’u gashi favorite color na black and red kap Bauchi na duba ban samu ba.”
  “Haba kina so ne?”
  “Sosai ma wallahi.”
  “Toh shikenan ki d’auka na baki.”
  “In d’auka?!” tayi maganan unbelievably bata d’au Fateemah is as sweet as this ba. “Eh ki d’auka ba kina so ba? Na baki.”
  “A’a Aunty ai naki ne.”
  “Banason haka fah, nace ki d’auka.”
  “Wow! To nagode Allah saka da alkhairi” nan ta cigaba da ninke mata kayakin tana cikinyi taci karo da wani white blouse daya mugun mata kyau again gashi always same as her size nanma tayita zuzuta shi haka Fateemah ta d’au ta bata a takaice seda ta kwashi kayakin Fateema har hud’u da shoe and bag guda d’aya sannan taji dad’i. Cike da jin dad’i taje tasa cikin akwatinta. Kitchen Fateemah ta zarce ta shiga had’a lunch sede tun d’azu kasala ke damunta tana cikin soya kaza ta soma jin amai take ta nufi sink ta shiga kwararowa, nan fa uwar gulma ta shigo kitchen d’in a 360 a ranta tace _bade ciki ba!_
  “Aunty Fatee lafiya? Subhanalli me kikaci haka? Sannu” nan ta tayata ta d’auraye bakin ta.
 
  “Dama bakida lafiya ne?”
  “Kar ki damu am fine something just came over me.”
  “Ahakan ne you are fine? Bari na kira Ya.”
  “A’a barshi karki tada mishi hankali a off-” bata k’are maganan ba tasake juyawa sink ta cigaba da kwararo amai tana iddawa Zeezee ta d’au waya ta kira Ya Ibraheem kan gida ba lafiya. Not long enough ya iso hankali a tashe, Fateemansa ya tarar zaune a kasalance kan kujera. ”Omg! Sweetheart whats wrong?”
  “Babu nifa seda nacewa Zeezee karta kira ka tak’i jina, am fine.”
  “Wallahi batada lafiya Ya amai tayi sau uku fitanka.”
  “Baby kinci wani abu ne?”
  “Wallahi I don’t know I keep on feeling nauseatic and weak.”
  ”Humm kinci wake kenan” cewar Zeezee. Sam Ibraheem be gane me hakan ke nufi ba, ita Fateema data gane se kawai tayi shiru.
  “Wake taci ya b’ata mata ciki?” Ibraheem ya tambaya.
  “Ai bama ita taci ba Ya, kai ka bata dan haka se kuje asibiti.”
  “Nikuma? Yaushe?”
  “Yo ina zan sani abu acikin duhu kuje asibiti de kafin jikin nata yayi worse.”
  “Uhm Zeezee d’an kashemin gas d’in muka dawo zan gama soya chicken d’in.” cewar Fateemah.
  “Ga Zeezee seta k’arisa ai kafin mu dawo.”
  “Wallahi karna k’ona kace zakamin duka gomma na fad’a maka tun yanzu ban iya soya kaza ba wallahi.”
  “Ko kunya bakiji ba da girman ki mschww”
  “To meh abin kunya aciki? Wanda taci wake bata ji kunya ba seni, ko ince wanda yabada wake beji kunya ba seni?” kai kawai Fateemah ta kad’a.
  “Wai me kike fad’a nekam? Wuce kije ki kashe gas d’in useless kawai. Kinsan gomma kin nutsu kin fara koyan girki ko?”
  “Ai nagama secondary school zan fara koya bari na d’au ma Aunty Fatee mayafinta nima zan biku.”
  “Kina gida ba inda zaki.”
  “Allah sarki mana Ya.”
  “Baby ni kawai kabarta taje jeki d’aukomin mayafi na akan gado Zeezee.” Da ‘toh’ ta fice. In less than 30 minutes suka isa asibiti nan akayiwa Fateema gwaji, not long enough result ya fito nan aka tabbatar musu juna biyu ne d’auke da Fateema. Dad’i kashe wannan happy couple banda Zeezee dake binsu da kallon tsiya “kome abin murnan oho? Dama kam akayi ai dole sakamako ya fito mschw kunada aiki wallahi.” Se anan Ibraheem ya fahimci zancen Zeezee na d’azu batun wai shiya bawa Fateemah wake taci oh! Allah ya shirya masa Zeezee yarinya sam ba kunya. Haka suna isa gida Fateemah tad’an huta tace zata cigaba da suyan sam Ibraheem ya hanata shida Zeezee suka k’arisa suyan nan ma seda ta k’ona kanta ta k’ona shi duka.

   Tun daga nan fa rayuwan Zeezee gidan Ibraheem ya soya. Wani irin d’an banzan laulayi ne da Fateemah, ko tsayuwan kirki bata iyayi dan haka bata iya aikin komi, duk wani aikin gidan Zeezee keyi banda girki saboda daman bata iya ba dan haka Ibraheem ke cikin siyo abinci ba dafe ba dare. Zeezee kullum cikin k’orafi ita wallahi hutun ma ya isheta zata koma gida.

   *~ *~ *~
  “Zeezee! Zeezee!” Ibraheem ya kira ta daga ciki.
  “Na’am” ta amsa tana zaune a parlour seda ta gama d’ura ashar sannan ta mik’e ta nufi d’akin nasu “gani.”
  “Ki had’awa Fateemah custard.”
  “Ni ban iya ba.”
  “Baby she don’t have to kabarta please.”
  “Had’a custard ma baki iya ba? Cinki za’a zo ayi ne?”
   “Ni wallahi zan koma gida nagaji da ni nace tayi cikin.”
  “Me kike ce?” yayi tambayan in a serious tone daya razana Zeezee.
  “Babu nace barin je na had’a mata sannu Aunty Fatee” tana kaiwa nan ta fice in less than 15 minutes ta had’a ta dawo kad’an Fateemah tasha Zeezee ta miyar da sauran, ga wanke-wanke nan tun na jiya da rana bata wanke ba. Da yamma Fateemah tad’an warware ta fad’a kitchen se gani tayi wanke-wanke nayi mata sallama. Kai kawai ta kad’a ta shiga wankewa tana cikin yi Ibraheem ya shigo “Sweetie wanke-wanken meh kuma bayan kinsan you’re sick, kibari Zeezee zatayi.”
  “Naga kaman muna tak’ura mata dayawa kabari yanzu zan gama.”
  “Kibari nace, Zeezee zo nan!” seda ta gama b’ata lokaci ta fito “gani.”
  “Oya karb’i wanke-wanken ki gama.”
  “Allah sarki Ya kabari ko zuwa gobe mana, yau fa nayi shara.”
  “Meaning? In anyi shara ba’a wanke-wanke kenan?”
  “Ni wallahi zan koma gida nagaji.”
  “Ai tunda kika kawo kanki sekun kusa fara Neco zaki koma gida.” K’afa tahau bugawa amman kota kanta beyi ba yaja Fateemah suka fice. Harara tabi wanke-wanken da sannan daga bisani ta d’aga wuk’a ta yanke yatsanta dagangan nan jini yahau bulbula. Wani irin rikicaccen ihu ta saki Ibraheem besan a lokacin da yafito ba “amman lafiyan ki kuwa?”

   “Wayyo Allah yatsa na, jinin jikina ze k’are na shiga uku!”
  “Meya sameki?” yayi maganan yana k’arasawa gun sink d’in, kawai gani yayi hannun Zeezee na jini sosai.
  “Subhanallahi! ya akayi kika yanke haka?” Tap ya bud’e yasa yatsantan nata underneath, se ihu take bayan daya gama mata dressing ya kalleta “dagangan kika yanke hannun naki dan karkiyi wanke-wanken ko?”
  “Mahaukaciya ce ni da zan yanke hannu na da kaina? Ni wallahi yana min zafi.” bakinta ya bige paw! “Nikuma me nace? Wayyo Allah hannu na, wallahi yana min zafi”
  “Toh dama ba dole ya miki ba mschww!” shi da kansa ya k’are wanke-wanken ranan. In 2 days time suka samu meh aiki dan duk yadda zasuyi sun san Zeezee bame aiki bace.
  One more week ta musu Yasmeen ta haihu ta samu d’anta. Nan fa Zeezee ta had’a akwatinta har airport su Ibraheem suka kaita ya sallameta da 10k Fateema kuma 5k da kuma turmin zani d’aya. Daga Abuja ta wuce Kaduna inda ta had’u dasu Mama, d’an Yasmeen kyakkyawa kaman Babansa anyi suna yaro yaci sunan Kakansa (baban mijin Yasmeen) Sulaiman. Bayan suna su Zeezee suka dawo Bauchi. Ko nunawa Mama kud’in dasu Ibraheem da mijin Yasmeen suka bata batayi ba seda ta gama kashe kud’in tukunah ta fad’a mata.

   Kowa na preparation na Neco banda Zeezee data sa yawo a gaba, yau ma as usual by 11am ta gama shiri ta fita, ta shiga cikin gari tana ta driving da gudu kamar yadda ta saba ta k’ure music, wayanta ne ya soma ringing d’agawan da tayi don ganin waye kawai the next abinda tayi noticing shine wani Baba tsoho dake dab da gabanta. Kafin ta ce zata danna brake harta bigesa. Kan motan ta juya da wuri hakan yasa ta buga kanta jikin wani pole. Kaca-kaca gaban motanta yayi, wani irin ihu ta saki daga nan bata sake sanin meya faruwa ba. A sume kanta na jini aka ciro ta daga motan, ita da tsohon data mai k’ariya biyu dakuma fashewan kai aka tattarasu se Teaching Hospital. Baba aka fara kira aka sanar dashi halin da ake ciki.

_45 minutes afterwards, Teaching Hospital..._





*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
beeenovels.blogspot.com

No comments: