Monday, 7 November 2016
HEEDAYAH!
5⃣7⃣
written by miemiebee👄
KANO STATE; Yau kimanin sati buyu da kwanaki knan, don moha yabar gda bekuma leqawa bakuma, se shirya kayakinsa yake da alama komawa zeyi yau bayan ya gama ya dau wayarsa ya kira mama, bugu daya ta daga "hello muhammad? Ya kake? Ina kake? Ka dawo gda pls," don moha yace "calm down mama ynxunnan zan dawo," mama tace "really? Muhammad zaka dawo? Ina kake inje in dauko ka?" don moha yace "kar ki damu mama in the next 25-30mins zan shigo," mama tace "toh Allah kare muhammad sekazo ko?" Ya katse wayar yaja trolley'nsa ya nufa gun biyan bills bayan ya biya ya hau hanya. Mama taje tasamu alhj ismail se murna takeyi, "alhj ynxu muhammad ya kira," alhj ismail yace "meyace? Ina yake?" Mama tace "yana hanya ma ynxu ze dawo gda!" Alhj ismail ya miqe tare da fadin "alhamdulillah dauko mayafinki muje mu siyo masa favorite dishes nasa," mama ta amsa da "toh" nan da nan ta shirya tafito suka wuce wata eatery inda suka siyo duk wani favorite abincin da don moha yakeso sannan suka nufa gda aka kintsa masa dakinsa tsaf sannan aka jera abincin kan dining kowa ya shirya yana jiran zuwansa ciki harda baba me gadi, bayan 10mins akayi honk a bakin gate baba me gadi ya karisa ya bude motar don moha suka hango bayan yayi parking yafito mummy ta qarisa dagudu tayi hugging dinsa haka daddy da safyan ma, safyan ya ciro masa jakarsa daga booth suka nufi site nasu, mummy kamar ta cinye don moha dan wani kyau da fresh daya qara, ya shiga bathroom ya watsa ruwa sannan yafito sukaci abinci dukansu bayan sungama daddy yace "muhammad inason mui mgn," don moha ji yake kamar ya kashe daddy dabanda yana planning wani abu bama da ba abinda zaisa ya dawo gda daga bisani yace "ok," suka fice zuwa garden suka zauna daddy yace "muhammad am sorry, am so sorry if only nasan inda heedayah take da na sa andawo da ita," cikin rashin fahimta don moha yace "taya zaka ce baka san inda take ba? Ba kai ka tura a dauketa ba?" Daddy yace "bani bane muhammad," don moha yasake shiga cikin duhu, "ba kai ba? Then waye?" Se alhj ismail ya bude baki zeyi mgn sekuma ya kasa, don moha ya gano hakan yace "shknan daddy na gane mesa kasa aka dauketan we don't have to talk about it any further" ya mike ni zan shiga daga ciki ya fice dakinsa ya nufa sannan ya kwanta kan gado ya zura wa ceiling ido, "why is my brain not thinking fast? Mesa na kasa figuring me heedayah ke nema a dakin daddy?" ya juya yana kallon gefe, "i have to find out bari daddy ya fita sallan la'asar"
Bayan fitar daddy sallan la'asar don moha ya shiga dakinsa yayi locking sannan yafara bibiya yana neman abinda besan meyake nema ba, can hannunsa yakai gun da daddy ke ajiye files nasa ya duba tas yaga duk files na daddy ne wannan to ina wannan tsohon ze kai files na daddy'n heedayah badan yana so ba ya fice daga dakin har ya kai bakin kofar dakinsa seya jiyo muryan daddy da alhj lawal a garden, sidak sidak ya karisa ya lebe daga wata corner yana sauraronsu, alhj lawal yace "ynxu kana nufin danka yasan asirin mu knan? Kaah! Amman wlh dan uwa ka badani, what if ya tona mana asiri fa" alhj ismail yace "muhammad bare taba yin haka ba," alhj lawal yace "is like nafika sanin halin danka, in baka sani ba toh kasani yau danka muhammad nason heedayah nd he can do everythng i mean everythng thing dan ya..." alhj ismail yace "nima nayi noticing haka, tashy mu dan fita naji ba iska a nan sosai" da sauri don moha ya shige dakinsa, sukuma suka fita bakin gate alhj ismail ya cigaba.."amman ai kaima kasan aure bare yu ba a tsakaninsu, sbd alhj s.u bare taba yarda da hakan ba bayan abinda muka masa," alhj lawal yace "den tun wuri kasa danka akan hanya ka nemo masa matar aure ya aura," alhj ismail yace "baran iya forcing muhammad ba, ze iya sake guduwa," alhj lawal yace "muhammad dan waye ne?" Alhj ismail yace "dana!" Alhj lawal yce "waya haifesa?" Alhj ismail yace "ni!" Alhj lawal yace "then sekayi controlling nasa kamar dan da ka haifa in bahaka ba muhammad ze mana ruining komi," alhj ismail yace "toh shknan zan masa mgn sukayi" sallama sannan y dawo ciki. Tun isar don moha dakinsa kansa ya daure, "wani asiri knan? This means su biyu suke aiki kenan, mummy tace daddy'n heedayah yabama daddy files na companies dinsa nd daddy ran away with it this means alhj lawal is his accomplice(me bada taimako ko hadin kai a yin abu), wow! Am suprised taya zasu yi haka wa daddy'n heedayah? Now I get it, nakasa samun files na daddy'n heedayah a dakin daddy, this simply means yana gun abban mustapha knan.
Can dare around 9:30PM safyan yayi wa don moha sallama kan daddy na kiransa ba tareda bata lokaci ba yaje yasamu daddy a parlournsa ya karisa ya zauna kan kujera, daddy yace "muhammad wai shin yaushe xamu kai gaisuwa ne? Kanada aikinka amman baka maganan aure, am starting to worry fa," don moha yayi wata murmushi a zuci yace "so accomplice naka ya gayama next move dinku knan? Lol," nan yabar mgn zuci yace "ba ynxu ba daddy, inason sena gama gina gdan da nike kai tukuna," alhj ismail yace "nawa kakeso in baka a jibi a gama ginin," don moha yace "ai bawai kudin bane banda banason ginin sauri ne i prefer taking my time a hankali har a gama," daddy yace "toh shknan, ynxu akoi tsayayyiya knan?" Don moha ya amsa da "eh daddy," alhj ismail yace "toh 'yar gdan waye ne? Ayi bincike akanta" Don moha yace "ai ba amfani daddy, sananniya ce...daddy ya katse sa "'yar gdan wa knan muhammad?" Don moha yace 'yar alhj s.u," alhj ismail ya zaro ido "gdan alhj s.u fa kace? Wa knan?" Don moha yace wa kuwa daddy inba heedayah ba," alhj ismail yace "ehm ehm ita da ta bata kuma bamusan ranan dawowanta ba har yaushe zaka tsaya kana jiranta bamu san ko tana raye bama fa," don moha yace "tana raye daddy, very soon zamu sameta in shaa Allah," alhj ismail yayi shiru cuz he's out of words don moha yayi noticing hakan yace "daddy lafy? Ya naga kamar bakayi murnan wannan abu ba? Ai daddy'nta aminin kane kaga neman aure ma bareyi wahala bako?" Baki na bari alhj ismail yace "eh eh sosai ma muhammad Allah sa hakan yafi alkheri shkenan u can go now"
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment