Monday, 24 October 2016

HEEDAYAH!


                  3⃣5⃣
   written by miemiebee👄

        Shams na ganin haka ta ajiye towel dake hannunta tasha gabansa "yi hakr in abinda na fada ya bata maka rai, bana son ganin bacin ranka" cikin tsawa don moha ke mgn  "that tears it now! Enough of this nonsense in bakida sense to ni inada, maza pack ur bellongings kibar gdan nan na sallameki wacce erin sakariya ce ke?" Shams harda durqushewa a qasa tana kuka tana bama don moha hkr yayi banza da ita tsallaketa yyi ze wuce ta cafko kafarsa tana hada sa da Allah badan yayi niyya ba yace "naji disappear frm here" ta miqe tare da fadin "nagode sosai nasan meya kawoka, batun friend dinanne aysha ko? To har ynxu bata dawo daga tafiyar datai ba sede ga number inta in kanaso seka kirata" don moha yace a zuci "lalle yarinyan nan har kinsan meya kawoni wato, well fine to banaso" a fili yace "haka clueless mind naki ya gaya miki? To bashy ya kawoni ba keep ur number with u" yakama hanya yana tafiya shams tace "dan Allah kayi hkr ka karba kaifa da bakinka kace tamaka kama da someone special u know" don moha ya tsaya cak sannan ya juyo yace "ina number din?" jikinta na rawa ta jeta gun dining ta dau wayarta ta shiga contact list tayi scrolling kan aysha da tai saving ranan ta miqa masa ya amsa ya copying acikin wayarsa ko thanks bece mata ba ya fice, shams se murna take ita a dole man crush nata ya amsa abu gunta, haka tagama aikin ta ranan cikin walwala da jin dadi tana gamawa ta wuce gda inda ta kira heedayah ta gaya mata yadda sukayi da don moha, heedayah tace "aikinki na kyau keep it up!" Tayi hanging call din ta kira frnd nata zainab, bayan sun gaisa take tambayarta "don moha din ta kiraki kuwa?" Zainab tace "a'a be kiraba" heedayah tace "toh ki aje wayarki kusa dake yakusan kiranki" ahaka sukayi sallama. Don moha na kishingide a dakinsa akan gado ya miqa hannu ya dau wayarsa dake kan side drawer'n side dayake kwance ya kai daidai kan contact da ya amsa gun shams wanda yayi saving da aysha seya fara dialing se ya katse dan shegen girman kai irin nasa haka yatayi at last de yasamu ya yi dialing sanda ya kusan tsinkewa sannan zainab ta daga tayi shiru dan haka don moha yace "hello?" Zainab on the other side tace "yes hello" don moha yace "am I speaking with aysha pls?" Zainab tace "yes, aysha c" yace "good, I can't actually remember the exact day but in xaki iya tunawa there was a day kkayi visiting frnd naki shams a gidan aikinta kinxo fita mukayi bombing into each other, remember?" Zainab tace "ohh yes haka so kaine dude din daya kusan fasa min goishi knan?" Don moha yayi smiling sannan yace "sorry..." nande ya fada mata abinda yake tattare dashy bayan yagama mata bayani zainab tace "ayyah kama ne kawai danni kam i don't know u ko a ynxu akace min ya kamanninka yake baran iya fada ba, kama ne kawai bansan wata heedayah ba nd ni suna na aysha ne" don moha yace "okay toh shiknan thanks kafin ta sake mgn yayi hanging up call din, sede har ynxu yakasa believing dan har ynxu conciousness nasa cemasa yake heedayah yagani amman abun daya keta tambayan kansa shine in heedayahn ne me xai kawota gdanmu? Nd taya zatayi frndship da wancan shams din? Gaskia shes not the one kama ne kawai. Yasa hannu yayi deleting number zainab wanda yyi saving da aysha. Ya shiga gallery yakai kan picture'n heedayah yayi zooming iya face nata yatsaya admiring picture din kamar yadda yasaba a hankali yake mgn "where ever you are heedayah know that I love you nd I will nva rest until the day u become my wife"
     Washe gari! Heedayah na zaune da mummy a parlour tare da daddy se hira sukeyi su na dan kallo mummy tace "nikam heedayah se yaushe kuma zaku koma sch ne?" Heedayah tace "wani sch kuma mummy?" Mummy tace "NIGERIAN LAW SCHOOL din mana ba a can bane zaki zama prosecutor din?" Heedayah tace "aww eh se nxt year, xamu danyi hutun one year ai kaminnan mu shiga wancan din" mummy tace "ohh toh Allah taimaka amman nifa kinsan kwata kwata banso wannan idea bako? Tsufa zakiyi a boko wlh ynxu u are 21 akara hutun one year naku 22 + 4yrs da zakiyi acan NIGERIAN LAW SCH din aikingama tsufa knan" heedayah tayi murmushi sannan tace "mummy kenan nikoda it'll take me 100yrs ne I don't care is my duty to revenge for my daddy" mummy tace "toh ni dama kinfi karfita amman Allah sa hakan shiyafi alheri" heedayah tace "yawwa kokefa mummy ta? Ameen" wayarta ce ta soma ringing tana ganin wake kiraan ta miqe da sauri zata haura sama dakinta mummy ta kalleta tayi murmushi a zatonta saurayi ke kiran heedayah (lol) heedayah na kaiwa dakinta ta daga "hello shams? Ya akayi?" Shams tace "heedayah kina lfya? Ki taho ynxu ba kowa a gdan" heedayah tace "to to gani nan zuwa" nan da nan ta canza night gown dake jikinta ko wanka batai ba tadan kwaskware ta fito, mummy tace "ina zuwa haka heedayah da safennan? Karfe 10:30AM nefa ynxu, heedayah tace "gdan frnd dina mummy batada lfya" mummy tace "Allah sa dagaske kke ba qarya ba"

No comments: