Monday, 24 October 2016
HEEDAYAH!
3⃣6⃣
written by miemiebee👄
Heedayah tayi murmushi sosai "kai mummy what where u thinking?" Kafin mummy tace komi heedayay tayi waving hand wa daddy ta fice, motarta ta shige me gadi ya bude mata gate ta nufa gdan su don moha straight tayi parking a corner yadda ta saba yau kam harda niqab nata, kafin tafito daga motar ta sa yau kam ba baba megadi ma a bakin gate din dan haka ta shiga hankalinta a kwance a parlour ta tarar da shams, tace "bini" suka shige dakin alhj ismail yauma shams na labe a bakin kofa da tsintsiya a hannunta, haka heedayah tayi duban duniyan nan bataga wannan cctv datake nema ba can ta hakura tace zata duba dakin mamansu ko ya kai can, shams tace da ta bari se gbe dan kar a kamasu hakan kuwa akayi har heedayah ta fice daga gdan ba wanda ya ganta ko me gadi ma. The nxt day again shams tamata waya da ta xo ba kowa a gdan haka tasake shiri taje da niqab nata saidai yau batayi parking motartan a inda ta saba ba tadan fito da ita daga corner din cuz anyi packing wata mota a inda tasaba parking natan abakin gate suka hadu da me gadi ta gaishesa tare da fada masa "aysha ce ta ranan frnd na shams" suka dan gaisa sannan ta shige yau dakin mama suka shiga tayi searching din duniya still shima bata samu ba har cikin pillow sanda ta dudduba duk wayam! Ba komi tayi kusan 25mins a gdan sannan shams tace mata da ta tafi kar aka musu, taqi ita wai a dole se ta samu abinda take nema sanda ta kara 10mins a gdan sannan ta yarda zata tafi har ta fita daga gdan, bayan ta ja gate ta rufe juywanda tayi suka hada ido hudu ita da don moha sun kusan 30seconds suna kallon juna sannan tace "sorry" ta matsa gun da sauri tayi gun motarta ta bude ta shiga ta fice da gudu don moha yace DH836•LSR (wato plate number in motan ya karanta knan) yakuma nanatawa yadda bare manta ba sannan ya shige ciki suka hadu da baba megadi, yace "baba wace wannan kuma?" Baba yace "ahh don moha ka dawo ne? Ai kawar shams ce aysha" don moha yace "I knew it!" Da karfi "Nasan yarinyan nan dole nasanta but I don't know a ina" site nasu mama ya nufa bega shams a parlour ba haka ma a dining space dan haka ya kira sunanta ta amsa nan da nan tabar du abinda takeyi ta fito "ina kwana?" Yace "ya kke black beauty?" Wayyo zokuga washe baki gun mutumiyar sekace an mata albishir da shiga aljanna tace "lfy qlou" hakwaran nan kamar me tallen maclean azuci don moha yace "mumu am jez using u" yace "ynxu frnd naki aysha ta baro nan ko?" Shams tace "eh ko kun hadu ne?" Don moha ya gyada mata kai tare da mata wannan shegyar murmushinsan mesa mata falling masa yace "ko zaki iya kiranta kice mata tazo gbe? Inason in saba da ita naga she's calm jez like u" shams tayi shiru for a while don moha yace "common shams don't you trust me?" Tare da mata wink mutumiyar bata san sanda tace "toh zan kirata" ba, don moha yace "yawwa black beauty but fa karkice mata i asked u to do so, kinji ko?" Giada kai kawai take kamar shashasha koda shike daman shashashan ce. Don moha yace "yawwa kira ta toh ynxu karki manta anjima" shams tace "kar kadamu har zaka sani abu inqiyi ko ince na manta kasan bazata yu ba" don moha yace "nasani kawai de ki kira min ta ynxun" tayi shiru dan tarasa me zatayi ita harga Allah tana mutuwan son don moha she can do anything dan ya sota tunani kuma take taya zataci amann heedayah, haka de shedan yata mata wasa da yar hankalinta daga qarshe ta yarda biya wa don moha buqatarsa dan shashanci don moha yace "aw baraki kira min itanba knan?" Shams tace "toh me zaka min in na kira maka ita?" Don moha yace "ko me kkeso" ta washa hakwara sannan tace "dgsk?" Don moha yace "sure my black beauty zan kaiki shopping ma in kinaso" dama wayar jahilar na hannunta tanajin haka ta sa number'n heedayah ta kira bugu daya biyu heedayah ta daga tace "hello shams?" Shams tace "kixo gbe kamar time da kkazo yau kinji?" Heedayah tace toh "inade baran sami kowa a gdan ba?" Shams tace "eh mana sekace baki yarda dani ba" heedayah nason sake mgn shams tace "se anjima." (Masu karatu karku manta fa a handsfree akayi wannan waya duk don moha naji). Yace "yawwa black beauty gbe zamuje shoprite ko?" Shams da shashanci wai "eh don moha" yace "yawwa" tare da miqewa yafara tafiya a zuciya yace "ban taba ganin bahuwa, sokuwa, fool like shams dinnan ba" yayi murmushi sannan ya wuce site nasa se nanatawa yake a zuci "yau zanga aysha dan ni har a yau banyarda I dont know this gurl ba gani nake kamar wata wanda nasani ce, we will see 2moro.
Washegari! exactly time da heedayah ta iso gdan su don moha jiya haka ta hallara ma yau tayi parking motrta a inda tasaba duk don moha na labe daga wata lungun shima yana kallonta ta daura niqab nata sannan ta fito ta kusa kaiwa bakin gate nasu don moha ya fito daga gun buyarsa yakarasa yaga plate number din sak erin na jiyan ne yayi murmushi sannan ya bi bayanta takai bakin gate din knan tasa hannu zata bude don moha yasa hannu acikin aljihu yaciro wata hanky dagani yasamata erin wannan magani ne me sumar da mutum dinnan nan da nan ya manna mata a hanci kafin tayi kokarin kwatan kanta inaa! Mgnin yabi hancinta ta kwanta ajikinsa a sume nan ya dagata ya maida ita cikin motar ya ajiyeta a baya sannan ya taho gaba ya kunna motar suka bar unguwan.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment