Monday, 24 October 2016
HEEDAYAH!
3⃣8⃣
written by miemiebee👄
Don moha yace "home! Heedayah ta taso tazo ta samesa "pls kar ka min haka dan Allah ka kaini gda, banason mummy tashiga damuwa pls am begging you muhammad nasan u cant do this to me" don moha yace then stop forcing me to, its simple ki gayamun meke kaiki gdanmu nd mesa baki zuwa se in bakowa a gdan?" Heedayah tace "I don't have ansers to these questions becuz bansan me kake fada ba, dan Allah ka kaini gda" don moha yace "fine then, sekiyi xaman ki anan dama ban gaji da ganinki ba" heedayah tace "pls muhammad so u can kidnap the person u love? Remember don moha kace u love me then mesa zaka rabani da mummy na eh, mesa? Shin zaka iyayin haka ma wanda kakeso?" Jikinsa duk yayi sanyi yakasa cewa komi ya ja kofar yayi locking ta waje kawai, heedayah tafara bubbuga kofar "don moha let me out of here pls" se bugawa takeyi don moha na tsaye a bakin kofar dakin tafi 2mins tana bugawa can yasa hannu ya bude kofar tare da fadin "come lets go" sanda yabari ta matso kusa dashy yasa hannu a aljihu yaciro hanky'n dazu ya manna mata a hanci atake ta kwanta sumammiya ajikinsa ya daga ta yakaita kan gado ya kwantar da ita sannan ya sami wata igiya ya daure hannunta biyu da gadon haka kafarta ma yadda ko ta tashy barata iya guduwa ba, a hankali yacire mata hijabin dake jikinta, akasan dakin yaga ribbon nata ya miqa hannu ya dauka sannan ya mata packing gashin ta gu daya yabata peck a kumatu sannan ya fice ya tari taxi dan baiso tafiya da motar heedayah ba kar ya hadu da wanda yasan ta da motan asirin sa ya tonu. Bayan isarsa gda ya watsa ruwa ya feffeshe turare ya gyara gashin kansa yasa jeans nd T shirt masu amsar body figure nasa, ni miemie na dau ko gun budurwa zasa senaga ya nufa side nasu mama a zuciya nace "don moha anne ynxu duk uban wankan nan gun shams zasa, lallai!" karan shams ya jiyo a kitchen yayi wata shu'umar murmushi sannan ya kai daidai bakin kofar ya tsaya ya dan jingina da bango ya daura kafa daya kan daya yayi folding arms nasa kamar me jiran a masa picture ko cikakken 30secs bayi ba turarensa ya buga hancin shams a take ta juya tare damasa murmushi shima murmushin yamata shima yace "ko kin manta yau zan kaiki shopping din?" Shams tace "laaa haka fa yi kr dan Allah kar ka fasa aiki ne yamin yawa sena dan sha'afa" don moha yamata murmushi sannan yace "dont worry jeki shirya mu tafi tace to kajirani a parlour" se washe baki take tayi nan danan ta kammala abinda takeyi don moha na jiranta a parlour ba abinda yakeyi a zuciyarsa se zagin shams shi har yau mamaki yake how stupid nd senseless can she be bayan like 5mins shams tafito jan bakin nan kamar me jiran a mata kiss tasha sa sosai gashy ja be karbi bakin fuskarta ba ko kadan, ga giran nan katin katin ga concealer kamar an shafa mai se wani sallama yake, kayanta ne kawai yyi kyau doguwar rigar ce setayi irin rolling dinnan da don moha yaganta besan sanda dariya ya kubuce masa ba seyaci fuska yamaida dariyan tari kar yyi ruining plan nasa yace "black beauty kinyi kyau amman wannan jan baki beyi yawa ba?" shams tace "ai haka ake yayi ynxu, shine makeup na zamani bakaga yamin kyau bane?" Don moha yace "ahh sosai ma, lets go?" Shams tace "eh" don moha ya mike tana biye dashy a baya daidai gun motarsa ya tsaya kirar audi 2016 ya bude yashiga itama ta bude gaba tashiga me gadi ya bude musu kofa, bece mata komi ba itako se kallonsa takeyi har yafara feeling uncomfortable yakunna cool music nasa yana dan bi a hankali, shams kamar ta hadiye don moha ahaka ha suka isa sahad dan bare iya shiga da ita shoprite ko sabuwar jifatu bakam gomma sahad dinde bayan yyi packing yace "muje ko?" Suka fita a tare tana biye dashy a baya suka shiga ya nuna mata trolley daya ta dauka yace "oya ki zagaya ki duka duk abinda ya miki kyau har sama ki haura ki dauki komi its ur day black beauty" tare da winking dinta shams sekace wanda aka ma albishir da aljanna baki na rawa tace "toh toh kana jira na anan kenan?" Don moha ya gyada mata kai su shams ba'a taba shopping ba se diban kaya akeyi kamar hauka da abunda tasan amfaninsa da wanda batasani ba komi dauka takeyi sanda tayi 30mins sannan ta karaso gun don moha tare da fadin wlh nagaji ne kawai amman kayan kam har ynxu akoi wanda ban diba ba
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment