Saturday, 29 October 2016

HEEDAYAH!


                4⃣6⃣
   written by miemiebee👄

        Suka amsa da "yes oga sir" sannan suka fice. Da misalin 2:00PM don moha yafito yakai daidai gun motarsa har ya bude daddy ya kwala masa kira haka ya rufo kofar yaje ya samesa "naam daddy" alhj ismail yace "ina kuma zaka?" Don moha yace "fita zanyi mana daddy," daddy yace "tohh rashin kunya zaka mun? Dama nace zama xakayi ne? Toh maza koma ciki inda ka fito ure not going anywhere," don moha yace "but why daddy? Da girmana kace ka hanani fita sekace dan yaro," daddy yace ban yafe maka ba in ka bar gdan nan yau," fuskar nan nasa a daure ya fice se guna guni yake "ai wannan ba yi bane taya da girmana za a hana ni fita" harda guntun tsukarsa banging kofar yyi da karfi sanda alhj ismail yajiyo karan har tsakiyar kansa yace "dan banza zaka gun da ka boye heedayah ba? Ai kasan ka ganta na karshe knan dan before 2moro anyi gaba da ita"*** dakinsa straight ya nufa ya miqe kan gado se huci yakeyi "taya daddy ze min haka? Yaro ne neni da ze hana ni fita mstw ynxu baby fa? Shknan barataci lunch ba ohh damn it!" Gallery'n wayarsa ya shiga yakai kan picture'n heedayah ya ajiye daidai kan heart nasa sannan ya rufe idansa kamar me bacci***mutanen alhj lawal kuwa sun kama hanya zuwa guest house na alhj ismail inda heedayah take daidai bakin gate din sukayi parking suka fito abnsu su biyu dayan ya bude musu kwadon da wata karfe sannan suka shige suka budo kofar parlour ma suka nufa dakin da suka ga heedayah daxu nanma suka bude kwadan to thier suprise sukaga dakin wayam! Ba kowa a ciki dayan harda sosa ido dayan kuma ya leqa toilet still ba sign na heedayah dan haka suka duba sauran dakunan gdan tas basu ga ko shadow inta ba, ba qaramin daure musu kai abun yayi ba, how comes? Ko guduwa tayi ne kam? Duk suka kasa kiran alhj lawal dan gaya masa halin da ake ciki dakyar atlast dayan yyi gathering courage ya kira alhj lawal ya sanardashy halin da ake ciki, alhj lawal yace "incompetence! Wace erin mgnan banza kake min? taya zakace bta gdan ghost ce ita? Bayan daxu kunxo kacemin kun ganta a gdan kuyi watever it takes ku samo min wannan yarinyan, I hope am clear" guy din baki na bari yace "super clear oga sir" tare da hanging up call din. Ya dawo da kallonsa kan dan uwan nasa guy oga sir fa ransa ya baci wai ma tsaya taya hakan ya faru, ba anan daxu muka ga yarinyan nan ba, to ina take ynxu?" Dan uwan nasa ya kada masa kai da alaman shima be sani ba. (Bayan lokacin da don moha yakaiwa heedayah breakfast ya fice exactly bayan 6mins yakuma dawowa ya labe daga wata corner cuz daman jikinsa ya gaya masa ana binsa bayan 4mins da tsayuwarsa a gun yaga guys na alhj lawal din sun shige gdan suka fito after some while, so bayan tafiyarsu ne don moha yakoma cikin gdan ya manna ma heedayah hanky'n ranan a hanci ta sume sannan ya fito da ita daga gdan yakaita wani gdansa, bawanda yasan yana da gdan ko daddy'nsa ma besani ba, beso kai heedayah dayan guest house na daddy ba cuz eventually xasu iya ganewa) abinda yafaru knan!
       Mummy kam saidai abinda yakaru dan kwata kwata ta fita daga hayyacinta takoma wani abu daban haka daddy ma tayi cigiyar heedayah har ta gaji ta rungumi qaddara takuma miqa sauran wa Allah. Heedayah kuwa kwana tayi da yunwa ko sallah da kyar ta idar, Allah ma yasota akoi fridge a dakin data bude tadan sami bottled water guda biyu atake ta kurbe daya.  WASHEGARI! da safe around 8:30AM don moha ya shirya ya fita batereda kowa yayi noticing nasa ba bayan ya hau titi ya duba mirror can ya hango motar wanda suke binsa jiya yayi wata jaririyar murumshi sannan ya cigaba da driving abinsa cikin nishadi a daidai restaurant din ya tsaya ya siyo wa heedayah abinci sannan ya fito yanufa boutique na ranan ya siyo mata kayaki da dama da inner wears ya nufa gun motarsa kamar ance ya juya, yana juyawa yaga guys din alhj lawal din, dayan yace "dan uwa is like ya ganmu fa dang it!" Tare da buga sterring motar. Don moha yaci fuska kamar be gansu ba hasali ma yi yayi kamar yana hangen wani abu ne a gefensu nan ne bakin dan uwan nasa ya budu yace "bafa mu yake gani ba ai na gaya maka," motarsa ya shige ya hau kan titi suma suka kunna motarsu suna biye dashy, yau ma kamar jiya sun bar mota daya a tsakaninsu basu san duk don moha ya ganesu ba maimakon ya zarce unguwan dakata kawaji inda ya ajiye heedayah se ya zarce sharada phase 3 gdan wani abokinsa daidai bakin kofar yyi parking ya fito da ledar abincin ya shige cikin gdan, mutanen alhj lawal din harda tafi erin mun gano ka dinnan bayan some minutes don moha yfito yaga mutanen  ko motsawa basui ba dayan harda daukan jarida irin yana karantawa dinnan bayan don moha ya fice da like 5mins daya gada cikin mutanen alhj lawal din yace "mushiga mu duba ko nan ne gdan ko?" Dan uwan nasa ya buge keyansa "kaifa wawa ne, yoh me amfanin dubawan? Ai kaima kasan dole nan ze kawota ko baka ga ya kaimata abincin bane ynxu de muje mu gayawa alhj kan mun sami gdan ko yaya?" Dan uwan nasa yace "a'a fa mutafi kum?  shi don moha yake ko me ya inya kuma dagata daga nan ya kaita wani gu daban kuma fa? Mude kira shi alhjn a waya ze fi" hakan ko sukayi alhj lawal yace "aikinku na kyau sekushiga ku daukota daga nan se musan nayi da ita" ya amsa da "toh oga sir" sannan ya katse wayar suka fito daga motar dukan su biyu da full confidence nasu da karfen bude kwadon su to their suprise suka ga kofar ko kwado ba'a datse masa ba dayan harda dariyan mugunta sannan yace "ji soko wato ko kwado ma besa ba hehhe lalle" ya tura kofar suka shige kamar yadda sukayi ranan haka suka soma yi ma yau suna zagaya windows din gdan can suka hango wata budurwa kan gado bayan like 40 seconds wani guy wanda barefi don moha a girman jiki ba yashigo dakin da short nasa dayasa ido sosai seyaga alamun mutane ta window yace "ku! Me kuke min a gda?" Budurwan ta hau ihu wanda ga dukkan alamu matar shi wannan abokin don moha dinne "kwarto kwarto..." se ihu takeyi

No comments: