Sunday, 23 October 2016
HEEDAYAH!
2⃣7⃣
written by miemiebee👄
Alhj ismail kuwa ana kaimasa key'n gdan alhj s.u ya daga kafa ya wuce gdan alhj ismail ya kaimasa, alhj lawal yayi praising nasa sannan yabasa key'n motar heedayah wato prado shiko ya amsa se faman godiya yakeyi can seyayi shiru alhj lawal ya tambayesa "ko lfy?" Yace "dan uwa ynxu in kai motan nan gda kanaganin ba matsala?" Alhj lawal cikin rashin fahimta yace "wace erin matsala kuma?" Alhj ismail yace "iyali na man, in ta ganni da motar ai zata san motar gdan alhj s.u ne dan kowa ya sansu da mota" alhj lawal yayi wata jaririyar dariya sannan yace "ya kake magana haka? Da sukadai ne masu prado a kano gaba dai? In zaka dau motarka katafi toh in bahaka ba zan saida ita" alhj ismail yace "toh shknan" Alhj lawal yace "toh ko kaifa? Kaga ko an tambaya sekace ka siya wa yaranka ne ana kaisu makaranta...(masu karatu ku dubi wani hada gu a wurin alhj lawal wato yana so ne bayan an fara kai yaran alhj ismail wato muhammad da safyan makaranta da motar heedayah, mummy taga motar ta tabbata shi alhj ismail dinne ya turo musu barayi dan dama can a baya alhj lawal ya gayamata kan barayin nan turo su akayi. Anan ke nan se maganan shi alhj lawal din ya tabbata, mummy tasake trusting dinsa nd bara ta taba suspecting nasa ba) Ni zanyi tafiya ma gbe nakeji, zani abuja inje in duba company na alhj s.u dake can, alhj ismail yamasa fatan alheri sannan ya shiga motar da alhj lawal yabasa ya dawo gda yayi parking dinta a inda yake parking motocinsa. Can da yamma matarsa ta dawo frm office taje parking motarta taga sabuwar prado a gda, ta gyara parking na motar ta sannan ta shige ciki ta wuce dakin alhj ismail yamata sannu da zuwa sannan take tambayarsa "sabuwar motar dake wajen fa? Wani ne yakawo ajia?' Ya amsa da "na siyo wasu muhammad ne, ana kaisu makaranta" mama tace "wow yaayi kyau sosai Allah kara budi" alhj ismail yace "ameen".
Washegari! Nanny ta shirya heedayah sch mal idi yyi dropping nata acikin honda V8 kasancewar ita kadai ta rage ynxu se mercedes benz E350 4matic na mummy. Bayan ya sauketa sega motar su don moha wato prado'n heedayah tasha gabansu suka fiffito shida qaninsa, heedayah da mal idi suka tsaya kura wa motar ido heedayah tace "tabbas wannan mota tace" mal idi kuwa na fadin "tabbas wannan motar heedayah ce" ze mata magana knan tafara tafiya a hankali don moha ya karaso yakira sunanta ta amsa abin yabasa mamaki dan rabuwarsa data masa mgn ya jima, sannan yace "how are you?" Ta amsa da "fine" tadanyi shiru sannan tace "nice ride erin nawa wanda barayi suka sace mana ranan" don moha yace "ayya in shaa Allah, Allah zai maido dawani karki damu" heedayah bata kuma cewa komi ba har ya kaita class sannan ya juya can yana tafiya seyana tuna abinda heedayah ta fadi mar, wait firstly, "heedayah has not been talking to me, so mesa tamin mgn yau?" Wata zuciyar tace masa "just cuz tana son kushirya ne" wata zuciyar kuma tace "a'a fa zauna kayi tunani bayan da kuka gaisa metace maka?" Don moha yace "cemin fa tayi nice ride ita ansace mata motarta erin wannan" zuciyar takuma cemasa "toh ai tana nufin wannan dinne kenan nata da aka sace" atake wata zuciyar tace "ko kadan ita de kawai tana fada maka ne kasani ka tausaya mata" haka de yata sake sake a zuciya yakasa figuring out komi. Ahaka har aka tashy, mal idi yazo daukan heedayah bece mata komi game da abinda suka gani ba da safe itama haka suna isa gda ta dau jakarta tayi ciki tafara kwala wa mummy kira, mummy na tare da daddy a dakinsa ta amsa heedayah ta karaso tace "mummy, mummy naga mota na da barayi suka sace a wajen driver nasu don moha an kaisu sch dashy yau" mummy tace "whaat??? Heedayah look at me, are you sure?" Heedayah ta gyada mata kai, mummy tace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un alhj ismail! Abinda zaka saka mana dashy knan? Bayan ka siyar mana da gda still be isheka ba sanda ka turo yan fashy suka mana aika aika? To wlh kasani Allah ya fika, mugu, azzalimi, maci amana kawai" ta fashe da kuka heedayah tace "stop crying mummy ki kai karansa gun police auntin mu tace mana in aka mana sata mukai kara gun police because police is our friend ze dawo mana da abunmu" duk wannan mgn da sukeyi daddy na jinsu zuciyarsa wata irin radadi take masa ba abinda yake yi a zuciyarsa se faman jan Allah ya isa wa alhj lawal da alhj ismail. Mummy tace "let him be, in yanaga yana da wayo ai Allah yafisa mude mu dage da addu'a jeki canxa kaya kici abinci, Allah miki albarka my princess" heedayah tace "ameen" tama mummy peck a kumatu sannan ta je gun daddy taga idanunsa duk sunyi ja sun kada tace "dnt cry daddy ta matso kusa da kunnensa tace masa "ba nace zan zama prosecutor watarana ba? Zan karbo mana gdan mu da motan mu, I promise" shima ta basa peck a kumatu sannan taja trolley jakarta ta fice zuwa dakinta
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment