Sunday, 23 October 2016

HEEDAYAH!


                  2⃣6⃣
   written by miemiebee👄

       2 days later, su mummy sun gama packing kap, an wanke musu sabon gdansu, taje tayi hayan masu mota irin trailers dinnan suka iso, har sun fara sa kaya cikin mota. Heedayah tana sch dake exams sukeyi but ranan friday zasu gama. Bayan manya manyan trailers sun gama kwashe kayakin tas suka fara tafiya, mal idi na cikin mota yana leading nasu to new home. Da mutane kadan mummy tayi sallama bataso shiga gdan alhj ismail ba so kawai tayi wa matarsa waya ta gaya mata, bayan sun gama waya mummy taja daddy cikin mota da taimakon nanny sannan ta rufo gdan ta bama mal musa keys din gdan daya kai wa mal ismail, hakan kuwa akayi, bayan ya kai masa ya dawo su mummy suka fice suma, basu dau lokaci dayawa ba suka iso sabon gdansu dake unguwar danjuma goje. Gdan de ba yabo ba fallasa yana da kyau ba laifi 3 bedroom flat ne da parlour, dinning seda kitchen store. Nan da nan aka shiga sauqe kaya su mummy suna shiryawa a inda ya kamata kafin a dauko heedayah sun kusan shan rabin aikin, lokaci nayi mal idi yaje ya dauko heedayah, tana ganin a canza hanyan gda ta tambayesa dalilin hakan, be boye mata ba yagaya mata shiru ne ya biyo baya haka har suka isa sabon gdan nasu tafito daga mota ta tsaya kallon gdan ba garden inda aka ajiye mata swings da slides nata, ba inda ake aje musu numerous motocinsu ba BQ inda ta dan saba labewa sometimes...mal idi yace "mushiga daga ciki ko heedayah?" Batace komi ba tabi bayansa suka shiga adaidai lokacin mummy ke fitowa daga wata daki tamata oyoyo heedayah ta kariso gun mummy, mummy tace "ya exams?" Heedayah ta amsa da "fine" mummy tace "good Allah bada sa'a, zo muje kiga dakinki ko?" heedayah bata ce komi ba, mummy ta riko fuskarta tace "stop worrying dear everythng is going to be alright in shaa Allah, anjima kadan za'a zo a hada miki swings dinki ko?" Heedayah ta gyada mata kai suka wuce dakinta yadda yake a can babban gdansu haka yake ma a nan  ba abunda ya canza, arrangements din komi irin na canne hakan kuwa ba qaramin dadi yayi wa heedayah ba sede dakin can yafi wannan girma ta dago idanunta tace "thank you mummy, ina daddy?" Mummy tace "yana daki, ki canza kaya sekije ki samesa" tabata peck a goshi heedayah ta ce "toh" mummy ta fice heedayah tacire uniform nata tasaka wata yar kantinta sannan ta fito parlour taga dakuna biyu, daya na facing dakinta daya kuma na can ta duba na kusa da dakintan bata ga kowa ba sannan ta wuce dayan tana budewa taga daddy takarasa da gudu tayi hugging nasa se faman murmushi yake mata tace "daddy do you like our new home?" Daddy yamata murmushi sannan ya gayada kai tace "nima inaso amman nafison wancan, wannan gdan bekai wancan girma ba daddy" daddy ya gyada mata kai tacigaba "don't worry xanyi karatu sosai sena zama prosecutor se inyi arresting daddy'n don moha mu karbo gdanmu ko?" Murmushi sosai daddy keyi ya gyada mata kai, yafara kokarin daga hannunsa dan yashafa kanta amman ya kasa tamasa murmushi ta dago hannunsa ta rike tana wasa dashy tana basa labarin abinda ya faru sch.

No comments: