Saturday, 29 October 2016

HEEDAYAH!


                4⃣9⃣
   written by miemiebee👄

        Dagaske?" Guy din yace "absolutely sir you can always count on us, yanzu ya za'ayi da itan?" Alhj lawal yace "ku biya ta gdana amman fa kuyi a hankali kar a ganku, zan baka key din gda na dake old GRA seku kaita can ku ajiye ta before inyi figuring out abinda zamui da ita," guy din ya amsa da "okay oga sir!" Gamu nan zuwa sannan yayi hanging. Nan da nan alhj lawal yakira alhj ismail ya labarta masa komi alhj ismail yace "toh toh yayi kyau amman kace kar nayi scolding muhammad?" Alhj lawal yace "ka fallasar damu knan ai" alhj ismail yace "toh shknan" ahaka sukayi sallama bayan 'yan mintuna mutanen alhj lawal suka iso gdan alhj lawal ya miqa masu key din gdan sannan suka fice daidai 3:30PM suka isa gdan alhj lawal din sanda suka tabbata ba me ganinsu sannan suka shige gdan maimakon su kwantar da ita kan gado a'a zaunar da ita sukayi kan wata kujera ta katako sannan suka daddaure hannayenta bibbiyu a baya haka kafafunta ma sannan suka mata taping baki da wata erin cellotape me zafin tsiya sun kaida fita knan alhj lawal ya kira daynan, daga wayar da zeyi yayi daidai da farkawan heedayah motsi ta soma yi a taqure "hello oga sir?" Alhj lawal from the othet side ya amsa "eh ya?" Guy din yace "gashy mun kawota gdan kamar yadda kace muyi oga sir" alhj lawal yace "good gbe around 5:30AM na safe nakeson ku fita da ita daga garin nan ku kaita can ta kudu kudu ko erinsu Osun ko Ogun kowani Edo erin garin 'inyamuran nan de ku kashe min ita yadda ko gangan jikinta bara'a sake gani ba" zaro ido heedayah tayi tasoma bari guy din ya amsa da "yes oga sir!"...duk wannan magana a kunnen heedayah hawaye tafara zubda a hankali meban tausayi, "mesa don moha ze min haka? Meh mutuwa ta xe kara masa? Me na taba masa da ya gommaci ya raba ni da mummy na da daddy na?" Duk wannan tambayoyi jerosu takeyi wa kanta ba tare da answers insu ba. Hawaye takeyi sosai... Guy din ya dawo da kallonsa kan heedayah "heedayah kke ko me? Oga sir bece mu baki abinci ba sbd haka ba abinci miki," dan uwan nasa yace "ko ruwa mu bata mana kalleta fa dagani 'kishi takeji," dan uwan yace "to je ka dauko mata" nan ya fice yaje ya dauko ya dawo ya miqa wa dan uwan nasa ya amsa yayi kan heedayah data fara shaking already hannu hasa ya balla cellotape dake bakin nata da karfi sanda gun yayi ja dan azaba ihu ta sakar yace mata "shhh" ya bude ruwan yafara bulbula mata a fuska haka ya jiqa ta tsam! Sanda ruwan goran faro irin babban nan ya kare tas, yana kaiwa nan yaja hannun dan uwan nasa suka fice daga gdan tare da locking ko ina. Fashewa tayi cikin wata erin matsanancin kuka ga hannayen nan nata du an daure mata su a baya harsun soma mata tsami haka kafafunta ma, gashi ya jiqa mata kaya har jikin nata yafara kai kayi tunanin mummy'nta da daddy tasoma tana hawaye sosai.
        Daidai 4:15PM don moha yayo gun motarsa acikin hanzari dake yau ya makara bekai ma heedayah lunch da wuri ba daga balcony alhj ismail ya hango sa murmushi yayi sannan yace "dan banza zaka gun heedayah ba? Allah bada sa'a" yana kaiwa nan ya shige ciki don moha ya fice nan da nan ya siyo mata abincin ko office daya saba labewa yau be labe gun ba direct gdan ya nufa he's ready to take her to another home koda masu binsan suna biye dashy yau, yana kaiwa gdan yayi parking a waje se sauri yakeyi ya shige ciki ya budo dakin daya ajiye heedayah yagani wayam! Ba kowa ya gwada knocking a bakin kofar a zatonsa ko tana ciki nan ma yaji shiru dan haka ya fada cikin toilet din nan ma bega ko alamarta ba hankalin don moha in yayi dubu be tashy ba "shin ina heedayah zataje?" Sunanta yahau kira da karfi yana zagaye every inch na gdan amman ina heedayah is nowhere to be found kasa daukansa kafafunsa sukayi kawai yajisa akan daya daga cikin sofa's dake parlourn hannu yasa a kai idanunsa cike da hawaye "my heedayah, my baby my future wife where are you pls? Show urself to me pls ,kinsan I can't do without you, I really hope am dreaming sbd in na tashy inganki kwance akan gadon dakin can pls heedayah come back to me..." yana cikin wadannan maganganu idanunsa suka kai kan wani piece of abu a kasar parlour din ta wajen bakin kofar da kyar ya iya ya miqe ya nufa gun ya miqa hannu ya daga dankunne yagani nd ga dukkan alamu dankunnen heedayah ne cuz for sure yana ganinsa a kunnen heedayah ...

No comments: